TIN: Muhimman abubuwa 11 game da sabuwar lambar haraji da za ta fara aiki a 2026
Abuja - Dokar Hukumar Kula da Haraji ta Kasa (NTAA) za ta wajbta amfani da Lambar Shaidar Haraji (Tax ID) don gudanar da wasu ma'amaloli daga 2026.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Fara amfani da dokar NTAA daga 2026 zai sauya yadda ‘yan Najeriya suke gudanar da harkokinsu na banki, kasuwanci, da ma rayuwar yau da kullum.

Source: Twitter
Taiwo Oyedele, shugaban kwamitin shugaban kasa, kan sauye-sauyen haraji, ya amsa tambayoyi 11 a shafinsa na X, da galibin mutane suke yi game da lambar haraji:
Tambayoyi da Amsoshi game da dokokin haraji
1. Shin gaskiya ne cewa kowa yana buƙatar lambar TIN kafin ya buɗe ko ya ci gaba da amfani da asusun banki?
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amsa: E, amma tare da wasu ƙarin bayani. Sashe na 4 na NTAA ya buƙaci dukkan masu biyan haraji su yi rajista da hukumar haraji kuma su sami lambar shaidar haraji.
"Mai biyan haraji" shi ne mutumin da ke gudanar da sana'a, kasuwanci, ko wani aiki na tattalin arziki don samun kuɗin shiga.
An buƙaci bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗi su nemi lambar shaidar haraji daga mutanen da ke biyan haraji domin ci gaba da hada-hada da su. Amma mutanen da ba sa samun kuɗi kuma ba su da wani kasuwanci ba sa buƙatar Tax ID.
2. Shin buƙatar lambar shaidar haraji sabuwar doka ce?
Amsa: A'a. Wannan ba sabuwar doka ba ce. Ya riga ya fara aiki tun bayan dokar kudi ta 2019, wadda ta sabunta sashe na 49 na dokar harajin gama garin mutane.
Tun daga Janairun 2020, ake buƙatar mutanen da ke buɗe asusun kasuwanci su bayar da Lambar Shaidar Haraji (TIN). Sabuwar dokar NTAA ta ƙara ƙarfafa wannan buƙatar ne kawai.
3. Me ya sa sabuwar dokar ta ce "Tax ID" maimakon "TIN"?
Amsa: "Tax ID" kalma ce da ta haɗa duk lambobin TIN da hukumar haraji ta tarayya (FIRS), kwamitin haraji na hadin gwiwa (JTB), da hukumar haraji ta jiha (S-IRS) ke bayarwa.
A ƙarshe, lambar NIN ɗinka (ga gama-garin mutane) da lambar CAC (ga kamfanoni) za su zama Tax ID ɗinka, wanda hakan zai sauƙaƙa wa mutane.
4. Idan na riga na mallaki TIN, shin ina buƙatar sabon Tax ID?
Amsa: A'a. TIN ɗinka na yanzu yana nan yana aiki. Idan kana da wannan lambar, ba ka buƙatar yin rajistar lambar shaidar haraji ta Tax ID kuma.
Amma ga waɗanda ba su da TIN, za su buƙaci NIN ɗinsu (ga gama-garin mutane) ko takardun rajistar CAC (ga kamfanoni) don samun lambar Tax ID ɗinsu.
5. Shin ina buƙatar bin dogon layi don samun Tax ID?
Amsa: A'a. Tax ID lamba ce kawai ta musamman da aka haɗa da ainihin bayanka, ba lallai sai ka mallaki katin lambar ba. Don samun Tax ID, za ka iya zuwa ofishin FIRS ko JTB mafi kusa, ko kuma ka yi rajista a shafin yanar gizon su. Kuma ana samun sa kyauta. Kada ka yarda da masu cewa ka biya kudi don samun wannan lamba.
6. Shin buƙatar Tax ID ta shafi kamfanoni?
Amsa: E. Ga kasuwancin da mutum yake yi na kashin kansa, ba a karshin kamfani ba, TIN/Tax ID ɗinka na sirri ya isa. Amma ga kamfanoni, da sauran ƙungiyoyi, za a samar da TIN ta amfani da bayanan rajistar CAC ɗinka.
Idan an yi wa kasuwancin ka rajista ba tare da TIN ba a baya, kawai ka je FIRS ko ka nemi lambar ta yanar gizon hukumar da takardun CAC ɗinka.
7. Shin ya shafi ‘yan Najeriya da ke kasashen waje?
Amsa: E. ‘Yan Najeriya da ke waje za su iya samun Tax ID ta hanyar amfani da NIN ɗinsu don ma'amalolin banki ko zuba jari a Najeriya.

Source: Twitter
8. Shin kamfanonin waje da waɗanda ba mazauna Najeriya ba suna buƙatar Tax ID?
Amsa: E, idan suna kasuwanci a Najeriya. Dole ne kamfanin da ba mazaunin Najeriya amma yana samar da kayayyaki ko ayyuka ga abokan ciniki na Najeriya ya yi rajista don samun Tax ID.
9. Shin hukumomin gwamnati ba za su biya haraji ba?
Amsa: A'a. Sashe na 5 na NTAA ya buƙaci dukkan ma'aikatu, da hukumomi, da kamfanonin gwamnati (na tarayya, jiha, ko ƙananan hukumomi) su yi rajista don biyan haraji kuma su sami Tax ID.
10. Me zai faru idan mai biyan haraji bai yi rajista ba kafin 1 ga Janairu, 2026?
Amsa: Ba tare da Tax ID ba, mai biyan haraji ba zai iya amfani da asusun banki, inshora, asusun fansho, ko asusun zuba jari ba. Haka kuma, zai fuskanci hukunci a karkashin dokar NTAA.
11. Wane amfani talakawan Najeriya za su samu daga wannan?
Amsa: Manufar ita ce a sauƙaƙe gano mutane, a rage yin ayyuka biyu a lokaci guda, da kuma rufe hanyoyin da masu gujewa biyan haraji ke bi.
Ga yawancin mutane da kamfanoni, NIN ɗinsu ko lambar CAC za ta zama Tax ID ɗinsu ba tare da ƙarin takarda ba. Hakan zai tabbatar da cewa duk wanda ke samun kuɗin da za a cire haraji ya bayar da rabon sa.
Tinubu ya sanya hannu kan dokokin haraji
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan sababbin dokokin gyaran haraji huɗu, wadanda ya kira "sabon babi ga Najeriya."
Tinubu na fatan waɗannan sababbin dokokin za su daidaita haraji, haɓaka kuɗaɗen shiga, da inganta yanayin kasuwanci a Najeriya baki ɗaya.
Dokokin da aka rattabawa hannu sun haɗa da dokar haraji, dokar gudanar da haraji, dokar kafa hukumar haraji da kuma dokar kafa hukumar haɗin gwiwar haraji.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng




