Za a rika gabatar da takardun biyan haraji (TIN) wajen bude akawun a banki

Za a rika gabatar da takardun biyan haraji (TIN) wajen bude akawun a banki

- Buhari ya kai wa ‘Yan Majalisa kudirin sabon tsarin amfani da banki

- Sanatocin Najeriya sun yi na’am da wannan kudiri da ya zo gabansu

- Watakila nan gaba sai kowa ya mallaki TIN kafin ya bude asusun banki

Muddin aka sa-hannu a kudirin tattalin arzikin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mikawa majalisa domin su amince da shi, za a kawo sabon tsari na bude akawun a bankuna.

Kamar yadda mu ka samu labari, zai zama dole masu bude asusu a banki nan gaba su tanadi takardun da ke bada shaidar biyan haraji. Wannan zai karfafa sha’anin karbar haraji a kasar.

Bankuna za su rika tambayar TIN ga wanda ya ke sha’awar bude sabon asusu a nan gaba. Hakan na zuwa ne bayan Majalisa ta yi na’am da kudirin da shugaban kasa ya gabatar a Watan Oktoba.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai sa tubalin gina Jami'ar Sufuri a Kauyensa

A cikin kokarin inganta sha’anin haraji, shugaba Muhammadu Buhari ya mikawa ‘yan majalisa wannan kudiri ne tare da kasafin kudin shekara mai zuwa lokacin da ya gabatar da kudin kasar.

Bayan bukatar TIN wajen bude sabon asusu a banki, sauran masu akawun a kasa za su bukaci wannan lamba ta TIN domin su iya yin wata mu’amala da banki kamar cire kudi ko kuma adana.

TIN wata lamba ce ta musamman da kowane ‘dan kasa ko kamfani su ke da ita domin shaidar biyan haraji. Ofishin karbar haraji ne ke bada wannan takarda saboda a rike tantance jama’a.

Bugu da kari, kyauta ake bada wannan lamba ta TIN idan har mutum ya na da bukata. A ka’ida cikin kwanaki biyu mutum zai samu lambarsa bayan ya gabatar da takardu gaban hukuma.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng