‘Kina Bin Yan Najeriya BaShi’: Tinubu Ya Jero Gudunmawar Matarsa ga Kasa, Ya Fadi Abuin
- Shugaba Bola Tinubu ya kwarara kalaman yabo da uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu inda ya jero alherinta a Najeriya
- Tinubu ya taya uwargidansa Oluremi Tinubu murnar cika shekara 65, yana mai cewa tana bin Najeriya bashi kan gudunmawarta
- Ya bayyana cewa ita ce abin ƙaunarsa da ginshiƙin ƙarfinsa tun daga farko har zuwa jagorancinsu, inda ta tsaya tare da shi cikin kowane hali
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu ya yabawa uwargidansa, Sanata Oluremi Bola Tinubu kan jajircewarta.
Tinubu musamman ya kwararo yabo ga Oluremi yayin taya matarsa murnar cika shekara 65, yana cewa tana bin Najeriya bashi mai yawa.

Source: Twitter
Tinubu ya yabawa jajaircewar matarsa, Oluremi
Hakan na cikin wata sanarwa da hadiminsa na musamman, Dada Olusegun ya wallafa a X a yau Lahadi 21 ga watan Satumbar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ya bayyana Oluremi Tinubu a matsayin ƙaunar rayuwarsa da ginshiƙin ƙarfinsa tsawon shekaru na gwagwarmaya da hidimar jama’a.
Ya ce matarsa ta kasance tubalin kwanciyar hankalinsa a lokutan wahala, daga gudun hijira na siyasa har zuwa jagoranci, cikin haƙuri, mutunci da sadaukarwa.
A cikin sanarwar, Tinubu ya ce:
“Yayin da ki ke bikin zagayowar ranar haihuwarki shekaru 65 a yau, kin ba ni goyon baya tsawon shekaru na gwagwarmaya da gudun hijira na siyasa, zuwa jagoranci, kin tsaya tsayin daka a gefena cikin mutunci, haƙuri da sadaukarwa da kalmomi ba za su iya bayyanawa ba.
“Kin fi karfin mata a wuri na, ke ce aminiyata, mai ba ni shawara, ’ya’yanmu da jikokinmu suna ganin misalin tausayi da bangaskiya tare da ke.
"Saboda ke, ƙasarmu tana ganin ainihin mace mai karfin guiwa; mai ƙuduri amma mai taushi, mai tawali’u, kina bin Najeriya bashi fiye da yadda mutane da yawa za su taɓa sani."

Kara karanta wannan
'Za mu dora daga inda ya tsaya,' Anji abin da Tinubu ya fadawa iyalan Buhari a Kaduna

Source: Facebook
Addu'o'in da Tinubu ya yi wa Oluremi
Tinubu ya ce Oluremi ta sadaukar da rayuwarta a boye wanda ba kowa ba ne ya sani saboda yan Najeriya da kuma al'umma tsakaninta da Allah.
Akarshe, ya yi addu'ar Ubangiji ya cika mata burinta da kuma kara mata shekaru masu albarka da hikima.
Ya kara da cewa:
“Yau, a matsayin mijinki, ina gode wa Allah don rayuwarki, lafiya da ƙaunar da kike nuna min marar misaltuwa, a matsayin Shugaban ƙasa, ina gaishe ki a matsayin Uwargida ta wacce tausasawarta ke ci gaba da taɓa rayukan miliyoyin mutane a ƙasar mu."
“Barka da zagayowar ranar haihuwarki ta 65, Oluremi, Allah ya kara miki shekaru masu zuwa da farin ciki, salama domin ci gaba da ba da gudunmawa”
Tinubu ya ba 'ya'yan marigayiya Grace 4 aiki
Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin bai wa ’ya’yan marigayiya tsohuwar shugabar ma'aikata a Abuja aiki.
Tinubu ya dauki wannan matakin ne domin tallafawa rayuwar iyalan marigayiyar, Grace Adayilo da ta rasu a Abuja.
Minista Nyesom Wike ya bayyana Adayilo a matsayin mai gaskiya, jajirtacciya, mai tawali’u da biyayya ga aikinta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

