Sirika: Ministan Buhari da Ya Zama Basarake Ya Gana da Aminu Ado Bayero, an Yada Hotuna
- Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya tarbi Sanata Hadi Sirika a fadarsa Kano, inda suka tattauna batutuwa masu muhimmanci ga masarauta da al’umma
- Hadi Sirika, tsohon Ministan Sufuri, wanda aka nada Hakimin Shargalle a Katsina, ya samu rakiyar manyan mutane zuwa fadar Kano
- Masarautar Kano ta tabbatar da ziyarar, inda ta bayyana cewa Sirika da tawagarsa sun gana da Sarkin Kano a Nassarawa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya karbi bakwancin manyan baki yan uwansa sarakunan gargajiya daga jihar Katsina.
Basaraken ya tarbi Sanata Hadi Sirika a fadarsa da ke Kano a jiya Asabar 20 ga watan Satumbar 2025 da muke ciki.

Source: Facebook
Shafin Masarautar da ke yada ayyukan basaraken shi ya tabbatar da ziyarar Hadi Sirika da tawagarsa a shafin Facebook a yau Lahadi 21 ga watan Satumbar 2025.
An tabbatar da cewa Sirika ya ziyarci basaraken ne a yammacin jiya Asabar 20 ga watan Satumbar 2025 inda suka tattauna bautuwa masu muhimmanci.
Nadin sarautar da aka ba Sirika a Katsina
Sanata Hadi Sirika wanda tsohon minisan sufuri ne a gwamnatin Muhammadu Buhari ya samu sarautar gargajiya a kwanakin baya.
Sirika shi ne Marusan Katsina kuma wanda aka nada Hakimin garin Sirika da ke jihar Katsina a kwanakin baya.
Masarautar Katsina da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya ta sanar da naɗin sababbin hakimai shida a faɗin jihar.
A sanarwar da sakataren masarautar ya fitar, ɗan Gwamna Diko Raɗɗa na cikin waɗanda aka naɗa a matsayin Hakimai.
A cikin sanarwar, har ila yau, tsohon ministan harkokin sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya zama sabon Marusan Katsina, Hakimin Shargalle a ƙaramar hukumar Dutsi.

Source: Facebook
Ziyarar Sirika ga Aminu Ado Bayero a Kano
Sanata Sirika ya samu rakiyar wasu manya a tare da shi da suka hada da Sarkin Yar Leman, Injiniya Sa’idu Njiddah mni, da Hon. Faruk Adamu Aliyu.
Sanarwar daga shafin Masarautar Kano ta yi rubutu kan ganawar sarakunan biyu kamar haka:
"A yammacin jiya Asabar 20 ga watan Satumbar 2025, Sanata Hadi Sirika CFR, FNIA FRAeS, Marusan Katsina kuma Hakimin Sirika ya ziyarci Mai Martaba Sarkin Kano, Alh Aminu Ado Bayero CFR CNOL JP a fadarsa da ke Nassarawa.
"A tare da shi akwai Sarkin Yar Leman, Injiniya Sa’idu Njiddah mni, da Hon. Faruk Adamu Aliyu."
Mutane da dama sun yi fatan alheri game da ziyarar inda suka bayyana muhimmancin hadin kai irin haka ga al'uma.
Aminu Ado ya hadu da Kwankwaso a wani taro
A baya, mun ba ku labarin cewa an gudanar da taron kaddamar da littafin tarihin Cif Gabriel Igbinedion a dakin taro na cibiyar Yar’Adua da ke birnin Abuja.
Rabiu Musa Kwankwaso ya halarci taron tare da sauran manyan ’yan siyasa da sarakunan gargajiya kamar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.
Masarautar Kano ta tabbatar da halartar Sarkin kuma ta wallafa hotunansa da Sanata Kwankwaso suna magana yayin taron.
Asali: Legit.ng

