An Gwabza Fada tsakanin Sojoji da 'Yan Bindiga a Jihohin Arewa 2, An Rasa Rayuka
- Dakarun FANSAN YANMA sun kashe ’yan ta’adda a jihar Kaduna, sun kwato bindigogi da babur a wani harin kwanton bauna
- Dakarun sun kuma dakile wani harin ’yan ta’adda a Kankara da Faskari, da ke jihar Katsina, inda suka kwato babura da kayayyaki
- Wani rahoto ya bayyana dalilai uku da yasa yarjejeniyar zaman lafiya da ’yan bindiga ba za ta iya dorewa na dogon lokaci ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Sojojin hadin gwiwa na Operation FANSAN YANMA sun kashe ’yan ta’adda biyu a wani harin kwanton bauna a karamar hukumar Kachia, jihar Kaduna.
Rahoton ya nuna cewa dakarun Sub-Sector 5 na rundunar OFY ne suka gudanar da wannan aiki a kan hanyar Wake–Kabode–Abrum.

Source: Twitter
Sojoji sun kashe 'yan bindiga a Kaduna
Mai sharhi kan lamuran tsaro a Arewa maso Gabas da kuma yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya sanar da hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Sauki ya samu da aka hallaka tantirin dan bindiga yana cikin shirya kai mummunan hari
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya ta bayyana cewa kwanton baunar ya biyo bayan sahihin bayanan leken asiri da aka samu kan shirin ’yan ta’addan daga Gabachua zuwa Insami da Kabode domin garkuwa da mutane.
“Kwanton baunar, wanda ya faru da misalin karfe 7:00 na safe, ya yi sanadiyyar hallaka ’yan ta’adda biyu,” in ji majiyar.
Sojoji sun kwato bindigogin AK-47 guda biyu, alburusai, wayar salula da babur daya da aka kona nan take bayan harin.
Katsina: Sojoji sun dakile harin 'yan bindiga
Haka kuma, wani rahoton Zagazola Makama a shafinsa na X ya nuna yadda dakarun Operation FANSAN YANMA a jihar Katsina suka fatattaki ’yan ta’adda a wani kwanton bauna.
Sojojin sun kuma kwato babura guda bakwai a wasu hare-hare da suka gudanar a Kankara da Faskari.
Rahoton ya ce lamarin ya faru ne lokacin da dakarun 17 Brigade ke sintiri a hanyar Kankara–FUDMA–Makera–Dutsinma–Dabawa, inda aka kai musu hari a kauyen Turare.
“Dakarun sun mayar da martani cikin gaggawa, inda suka kuma fatattaki ’yan ta’addan,” a cewar majiyar.
An kuma gudanar da wani samame a Jeka Areda, karamar hukumar Kankara, inda sojoji suka yi arangama da ’yan ta’adda da suka tsere zuwa Ruwan Godiya a Faskari.
Sojojin DSOF da ke Ruwan Godiya ma sun yi artabu da su, inda aka kwato babura shida a Ruwan Godiya da guda daya a Jeka Areda.

Source: Twitter
Kalubale ga yarjejeniyar zaman lafiya da ’yan bindiga
Rahoton jaridar Vanguard ya jaddada dalilan da yasa yarjejeniyar sulhu da ’yan bindiga a Arewacin Najeriya za ta iya rushewa.
Na farko shi ne rarrabuwar kawunansu, domin ba su da tsari daya kamar Boko Haram. Idan aka yi sulhu da rukuni guda, sauran na cigaba da kai hare-hare.
Na biyu shi ne ribar da suke nema, domin garkuwa da mutane da tsare hanya na kawo kudi, kuma tattaunawa tana kara musu damar samun kudin fansa.
Na uku kuwa shi ne rashin ingantaccen shugabanci a karkara, inda gwamnati ba ta da karfi, makarantu sun lalace, hanyoyi sun rushe, kuma jami’an tsaro ba su da yawa.

Kara karanta wannan
Jiragen yakin sojin saman Najeriya sun jefa bama bamai a Borno, an kashe ƴan ta'adda
'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaro
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a ƙauyen Unguwar Gada da ke ƙaramar hukumar Kafur ta jihar Katsina.
Ƴan bindigan sun sace dabbobi da ba a bayyana adadinsu ba, tare da jikkata wasu mazauna ƙauyen mutum biyu a harin da suka kai ranar Juma'a.
A yayin musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da ƴan bindigan, tayoyin gaba na motar ƴan sanda mai sulke sun lalace, haka zalika injin motar ya samu mummunan lahani, wanda ya sa motar ta kasa ci gaba da aiki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
