Lamari Ya Girma: Jami'ar da Aka ce Ta Karrama Rarara Ta Raba Gardama bayan Ce Ce Ku Ce
- Jami’ar European-American ta yi martani kan maganganu da ake ta yi bayan rahoton karrama Dauda Kahutu Rarara
- Jami'ar ta fitar da sanarwa tana nesanta kanta daga digirin girmamawa da aka baiwa mawaki Dauda Kahutu Rarara a Abuja
- Hukumar makarantar ta ce za ta kai maganar ga hukumomin Najeriya domin a hukunta masu yin irin haka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jami’ar European-American ta yi karin haske kan bikin karrama mawaki Dauda Kahutu Rarara a Abuja.
Jami'ar ta fitar da sanarwa tana nesanta kanta daga digirin girmamawa da aka ba shahararren mawaki Dauda Kahutu Rarara.

Source: Facebook
Martanin jami'ar da ta karrama Rarara
Jami'ar ta wallafa a shafinta na yanar gizo cewa kwata-kwata ba ta da hannu a karramawar da aka yi wa Rarara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Makarantar ta nesanta kanta daga mawaki Rarara da wadanda suka gabatar kansu a matsayin jami’an makarantar.
Sanarwar ta ce:
"Jami’ar ba ta amince da kowanne taron karramawa a Abuja ba, an shirya shi ba tare da saninta ko yardarta ba."
Jami’ar ta ce wadanda suka shirya taron sun yaudari mutane, suna kiran kansu wakilan jami’ar, amma ba su da hurumin wakilta ko karbar kudi.
Ta kara da cewa:
"Ba mu ba Dauda Kahutu Rarara, Ahmed Saleh Jnr., Mustapha Abdullahi Bujawa, ko Tarela Boroh digirin girmamawa ba."

Source: UGC
Jami'ar ta yi fatali da wasu a bikin
Makarantar ta ce ana samun sunayen masu digiri ne a rajistar malamai a shafinta, wadanda aka ambata ba su cikin jerin sahihai.
An kuma bayyana cewa Musari Audu Isyaku wanda aka ce wakilin Arewa ne, babu hurumin wakiltar makarantar, don haka maganar bogi ce.
Haka kuma aka ce Idris Aliyu wanda aka bayyana a jarida a matsayin dan majalisar makarantar, ba ya daga cikin shugabannin makarantar.
Jami’ar ta ce Aliyu Idris wanda aka baiwa matsayi a 2024, an cire shi nan take saboda rawar da ya taka a lamarin bogin.
Makarantar ta kuma tuna sanarwar da ta fitar a Afrilu cewa tsohuwar shugabar jami'ar, Josephine Egbuta, ta rasa hurumin wakiltar jami’ar.
Jami'a ta fayyace gaskiya kan shugabanta
Jami’ar ta kara bayyana cewa yanzu shugaban makarantar shi ne Farfesa Luca Scotto di Tella de’ Douglas di Castel di Ripa.
Ta bayyana matsayinta na doka a Faransa da kuma samun 'Royal Charter' daga Bunyoro-Kitara, ta nesanta kanta daga ikirarin Panama da Dominica.
Sanarwar ta kammala da cewa jami’ar za ta tuntuɓi hukumomin Najeriya domin su dakile masu fitar da takardun bogi tare da gurfanar da su.
Rarara ta magantu kan karrama shi
Kun ji cewa mawaki Dauda Kahutu Rarara ya bayyana godiyarsa bayan girmama shi da digirin Dakta daga jami’ar European American, duk da ce-ce-ku-ce kan haka.
Rarara ya musanta zargin biyan kudi don samun digirin, inda ya ce karamawar ta biyo bayan gudunmawarsa ga al’umma, yaren Hausa da siyasa.
A cewarsa, jami’ar ta yaba masa ne saboda kokarinsa wajen kula da jama’a da rawar da ya taka a siyasa da bunkasa harshen Hausa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


