NiMet: Za a Sheka Ruwan Sama da Tsawa a Taraba, Neja da Wasu Jihohi a Yau Lahadi

NiMet: Za a Sheka Ruwan Sama da Tsawa a Taraba, Neja da Wasu Jihohi a Yau Lahadi

  • Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwa da iska mai karfi a jihohin Arewa da safe da kuma da yammacin ranar Lahadi
  • Jihohin Arewa da ake sa ran ruwan zai sauka sun hada da Kaduna, Gombe, Kebbi, Zamfara, Adamawa, Bauchi, Borno, da Taraba
  • NiMet ta shawarci masu ababen hawa da mazauna yankunan da ke da ra'ayin ambaliyar ruwa da su yi taka tsantsan a wannan rana

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar kula da hasashen yanayi ta kasa (NiMet) ta fitar da hasashen saukar ruwan sama da iska mai karfi a ranar Lahadi, 21 ga Satumba, 2025.

A cewar rahoton NiMet, yawancin jihohin Najeriya za su fuskanci ruwan sama, iska mai karfi da kuma tsawa a wannan rana.

NiMet ta ce za a samu ruwan sama hade da iska mai karfi da tsawa a jihohi da dama na Najeriya a ranar Lahadi
Ruwan sama hade da iska mai karfi da tsawa yana sauka a wani yanki. Hoto: @nimetnigeria/X
Source: UGC

NiMet ta fitar da hasashen yanayin na ranar Lahadi ne a sanarwar da ta fitar a shafinta na X a daren ranar Asabar, 20 ga Satumba, 2025.

Kara karanta wannan

Rashin Imani: Wata mata ta sa cokali a wuta, ta cusa a al'aurar kanwar mijinta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hasashen ruwan sama a jihohin Arewa

Da safiyar Lahadi, akwai yiwuwar samun ruwan sama, iska mai karfi tare da tsawa a sassan jihohin Adamawa da Taraba.

Da yammaci zuwa dare kuwa, NiMet ta yi hasashen za a samu ruwan sama tare da iska mai karfi a sassan jihohin Kaduna, Gombe, Kebbi, Zamfara, Adamawa, Bauchi, kudancin Borno, da Taraba.

Haka ma a Arewa ta Tsakiya, za a tashi da yanayin hadari a sararin samaniya, amma rana za ta bullo a safiyar Lahadi.

Akwai kuma yiwuwar ruwan sama da tsawa mai sauki a sassan jihohin Nasarawa, Neja da kuma birnin tarayya Abuja.

Da yammaci zuwa dare kuwa, ana sa ran za a fuskanci ruwan sama da iska mai karfi a mafi yawan sassan yankin.

Hasashen ruwan sama a Kudu

A yankin Kudu, NiMet ta yi hasashen samun yanayi mai hadari da hasken rana, da kuma yiwuwar samun ruwan sama mai sauki a sassan jihohin Ebonyi, Abia, Imo, Lagos, Delta, Bayelsa, Rivers, Cross River, da Akwa Ibom a safiyar Lahadi.

Kara karanta wannan

NiMet: Za a samu ruwa da iska mai karfi a Abuja da jihohin Arewa ranar Alhamis

Da yammaci zuwa dare, ana hasashen samun ruwan sama mai matsakaicin karfi a yawancin sassan yankin, wanda hakan zai iya kawo cikas ga ayyukan yau da kullum.

Hukumar NiMet ta ce ruwan sama zai iya jawo hadurra saboda rage gani ga masu ababen hawa.
Masu ababen hawa na tafiya kan babban titi yayin da ake sheka ruwan sama. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Shawarwari da gargadi ga jama'a

Hukumar NiMet ta yi kira ga mazauna yankunan da ke bakin teku da su yi taka tsantsan a yayin da suke gudanar da ayyukansu na waje.

An shawarci masu ababen hawa da su yi taka tsantsan a lokacin ruwan sama saboda yadda yawan ruwa ke rage gani, tare da sanya hanyoyi su zama masu santsi da yiwuwar haifar da darurra.

Hukumar ta kuma kara da cewa, mazauna yankunan da ke fuskantar ambaliyar ruwa su dauki matakan kariya.

An kuma bukaci hukumomi da ma'aikatan gaggawa, da sauran masu ruwa da tsaki su kasance cikin shiri don tunkarar duk wani ƙalubale da yanayin ka iya haifarwa.

An gargadi jihohin Arewa kan ambaliya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnati ta yi gargadin cewa za a iya samun ambaliyar ruwa a jihohi 14 daga ranar 16 zuwa 18 ga Satumba.

Hukumar NEMA ta tabbatar da cewa ruwan sama mai tsanani ya riga ya haifar da ambaliya a wasu sassan Yola, inda gidaje da dama suka lalace.

Kara karanta wannan

Dan majalisar Filato da ake nema ruwa a jallo ya mika kansa, ICPC ta tsare shi

An ce za a iya samun ambaliya a garuruwa 52 da ke cikin jihohin da aka fitar da hasashen, ciki har da yankunan Kogi, Sokoto, Kebbi da Cross.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com