‘Ban Ga Dama ba ne’: Obasanjo Ya Bude Aiki kan Neman Wa’adi na 3 a Mulkinsa
- Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya tabo batun neman wa'adi na uku a mulkinsa da ya yi daga 1999 zuwa 2007
- Obasanjo ya musanta zargin neman wa’adi na uku, inda ya ce babu wanda zai iya kawo shaidar hakan cewa ya nema a lokacin
- Cif Obansanjo ya ce neman yafewar bashi ga Najeriya ya fi wuya fiye da wa’adi na uku, ya kara da cewa da ya nema, da ya samu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Accra, Ghana - Bisa ga dukan alamu an kai tsohon shugaban kasar Najeriya wuya kan rade-radin cewa ya nemi wa'adi na uku a mulki.
Cif Olusegun Obasanjo ya yi martani kan lamarin duba da zargin da ake ta yadawa inda ya fito karara ya kare kansa.

Source: Facebook
Obasanjo ya karyata zargin neman wa'adi na 3
Obasanjo ya bayyana haka ne a makon jiya a taron tattaunawa kan dimukradiyya na Gidauniyar Goodluck Jonathan a Accra da ke Ghana, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da yake jawabi, Obasanjo ya musanta zargin cewa ya nemi wa’adi na uku a lokacin mulkinsa, inda ya dage babu shaidar hakan.
A Obasanjo ya ce:
"Ina ganin ni ba wawa ba ne, Idan ina son wa'adi na uku, wasu sun yi tunanin na so shi, na san yadda zan bi. Kuma babu ɗan Najeriya, matacce ko raye, da zai ce na kira shi na gaya masa cewa ina son wa’adi na uku. Babu.”
Tsohon shugaban ya jaddada cewa neman yafe bashi ga Najeriya ya fi wuya fiye da neman wa’adi na uku, ya ce da ya nema, da ya samu.
Ya kara da cewa:
"Ina yawan fada musu haka, idan har ina son wa'adi na uku a wancan lokaci, da na dade da samu saboda ni na san hanyar da zan bi."

Source: Getty Images
Obasanjo ya tabo batun tasirin dimukradiyya
Ya kuma gargadi shugabanni da ke tsawaita zamansu a mulki, yana mai cewa ya yi imanin hakan sabon Allah ne mai girma.
Obasanjo ya ce shugabanci na bukatar samun sababbin jini da masu kuzari, maimakon shugabanni da ke jingina da mulki, inda ya nuna hakan haɗari ne ga kasa.
Obasanjo ya bayyana cewa babu wani tsari na mulki da ya dace ya maye gurbin dimokradiyya idan aka bi shi yadda aka tsara tun farko.
Ya ce ya kamata mulki ya kasance na dukkan jama’a, amma abin da ake gani yanzu shi ne mulki yana shafar wasu mutane kadan ne maimakon kowa da kowa.
An 'gano' dalilin Obasanjo na tsanar Buhari
Mun ba ku labarin cewa hadimin tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari, ya yi bayani kan sabanin da ke tsakanin ubangidansa da Olusegun Obasanjo.
Garba Shehu ya bayyana cewa Obasanjo ya tsani Buhari ne kawai saboda ya gaza biya masa wata bukata da ya nema lokacin da yake kan mulki.
Martanin na sa na zuwa ne bayan Obasanjo ya yi kalamai masu kaushi kan gwamnatin marigayi Buhari wanda ya rasu a watan Yunin 2025.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

