‘Manyan Dalilan da Suka Sanya Aka Girmama Ni da Digirin Dakta’: Rarara

‘Manyan Dalilan da Suka Sanya Aka Girmama Ni da Digirin Dakta’: Rarara

  • Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya bayyana godiyarsa bayan girmama shi da digirin Dakta daga jami’ar European American, duk da cece-kuce kan haka
  • Rarara ya musanta zargin biyan kudi don samun digirin, inda ya ce karamawar ta biyo bayan gudunmawarsa ga al’umma, yaren Hausa da siyasa
  • A cewarsa, jami’ar ta yaba masa ne saboda kokarinsa wajen kula da jama’a da rawar da ya taka a siyasa da bunkasa harshen Hausa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Mawakin siyasa a Najeriya, Dauda Abdullahi Kahutu Rarara ya yi martani bayan girmama shi da digirin Dakta a yau Asabar 20 ga watan Satumbar 2025.

An yi ta maganganu kan karrama mawakin duba da cewa bai yi makaranta mai zurfi da har ya cancanci hakan inda mawakin ya fito ya yi karin haske.

Kara karanta wannan

Hotunan manya a Najeriya da suka halarci bikin karrama Rarara da digirin Dakta

Rarara ya yi magana bayan karrama shi da aka yi
Mawaki Rarara da baki yayin bikin karrama shi da digirin girmamawa. Hoto: @Imranmuhdz.
Source: Facebook

Digirin Dakta: Rarara ya yi martani ga al'umma

Mawakin ya yi martani kan lamarin yayin hira da jaridar DCL Hausa wanda aka wallafa a shafin Facebook a yau Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin hirar, Rarara ya yi godiya ga jami'ar kan wannan karramawa da kuma wadanda suka halarci wannan taro.

Ya kuma tabbatar da cewa ko sisin kwabo bai biya ba domin ba shi wannan lambar yabo kamar yadda ake zato.

A cewarsa:

"Abubawa ne da yawa amma dan kadan a ciki sun ce na farko ina da kokarin kula da al'mmar yankina, yawanci ina yawan zama da su, mu ji matsalolin juna.
"Sannan muna yin iya bakin kokari domin kawo karshen wannan matsalolin, sai kuma tasiri wurin takar rawar gani a maganar yare na Hausa.
"Sai kuma na uku gudunmawar da na ke bayarwa a siyasance kuma abubuwan yana yi wa wadanda ake yi don su dadi musamman yan siyasa."

Kara karanta wannan

Wike ya fadi abin da ƴan siyasar Ribas suka saka a gaba bayan dawowar Fubara

Rarara ya fadi dalilin karrama shi da aka yi
Mawaki Dauda Kahutu Rarara yayin bikin karrama shi a Abuja. Hoto: @Imranmuhdz.
Source: Twitter

Rarara ya yi godiya bayan karrama shi

Rarara ya ce kawai jami'ar fada masa suka yi suna da taro rana kaza, idan yana da yan uwa ya taho da su za su karrama shi da digirin girmamawa.

Mawakin ya ce yana yi musu godiya saboda kawai sun ga wasu abubuwa da ya burge su ba tare da ya sani ba duba da irin gudunmawar da ya ke ba al'umma a bangarori da dama.

Har ila yau, Rarara ya bayyana cewa daga yanzu sunansa Dakta, bai kamata ana kiransa da gayan suna ba inda ya shawarci mutane su rika girmama sunan da aka ba shi.

An karrama Rarara da digirin Dakta a Abuja

Mun ba ku labarin cewa Gwamna Dikko Radda, tsohon Sanata Sa’idu Alkali da Nasir Bala Ja’oji sun halarci taron girmama Dauda Kahutu Rarara da aka yi a Abuja.

An gudanar da bikin karrama mawakin ne a Abuja a yau Asabar 20 ga watan Satumbar 2025, inda jami’ar European American ta ba shi lambar yabo

Kara karanta wannan

Shehi ya soki zargin gina masana'antar fim, ya gargaɗi gwamna kan mummunar ƙarshe

Taron ya samu halartar mutane da dama na kusa da mawakin ciki har da gwamna, minista da kuma amaryar Rarara, jarumar Kannywood Aisha Humairah.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.