Abin Fashewa Ya Tarwatse a Masana'antar Sojojin Najeriya, An Rasa Rayuka

Abin Fashewa Ya Tarwatse a Masana'antar Sojojin Najeriya, An Rasa Rayuka

  • Wani abu ya fashe a Masana'antar Kera Makaman Yakin Sojoji ta Najeriya (DECON) da ke cikin garin Kaduna
  • Rahotanni sun bayyana cewa mutum biyu sun mutu ciki har da soja guda daya yayin da wasu da dama suka ji munanan raunuka
  • Mazauna yankin sun ce karar ta girgiza gine-ginen da ke kusa kuma ta tsorata mutane har suka fara gudun neman tsira a yau Asabar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - An shiga tashin hankali a Masana'antar Kera Makaman Yaki ta Najeriya (DICON) da ke cikin garin Kaduna lokacin da wani abun fashewa ya tarwatse.

Rahotanni sun nuna cewa abin fashewar, wanda aka fara zaton bam ne da farko ya hallaka ma'aikata biyu a masana'antar yau Asabar, 20 ga watan Satumba, 2027.

Taswirar Kaduna.
Hoton taswirar jihar Kaduna a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mene ne ya fashe a masana'antar sojoji?

Kara karanta wannan

Hatsarin Jirgi ya rutsa da mutanen da suka gudo daga harin yan bindiga, an rasa rayuka

Bayanan da Leadership ta tattaro ya nuna cewa fashewar ta samo asali daga wurin hada hodar bindigogi, mutum biyu sun mutu ciki har da soja guda daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan lamari dai ya tada hankulan mutane a kewayen masana'antar, wacce ke unguwar Kurmin Gwari a cikin birnin Kaduna.

Wasu mazauna yankin sun tabbatar da cewa fashewar ta kasance mai kara da karfi har ta girgiza gine-ginen da ke kusa, lamarin da ya sa mutane da dama suka ranta a na kare.

Yadda fashewar ta auku a Kaduna

Wani mazaunin yankin ya ce:

"Na ji karar fashewar wani abu, ya girgiza gine-ginen da ke kusa da DICON. Nan take mutane suka fara guje-guje domin guduwa daga wurin.
"Da farko mun yi tunanin ko harin bam aka kawo yankin, amma daga baya muka ji cewa daga cikin masana’antar ne.”

An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Katolika na St. Gerard da ke Kakuri, kimanin kilomita biyu daga masana’antar, inda likitoci ke kokarin ceto rayukansu.

Daga bisani motar daukar marasa lafiya ta sojoji ta kwashe su zuwa Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna domin kulawa da su, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara na shirin komawa mulki, dandazon mutane sun mamaye gidan gwamnati

Mene ne ya jawo wannan fashewa a DICON?

Wani ganau wanda ya taimaka wajen kai wadanda suka jikkata asibiti, ya ce fashewar ta auku ne a wurin samar da hodar bindiga da ake amfani da ita wajen kera makamai.

“Fashewa ce daga wurin samar hodar bindiga, daga wani abu da ake kira ‘primer powder’. Ta kashe jami’in soja nan take tare da wani ma’aikaci farar hula.
"Wasu ma’aikata hudu sun samu munanan raunuka, yanzu haka suna cikin mawuyacin hali," in ji shi.
Dakarun sojojin Najeriya.
Hoton babban hafsan tsaron Najeriya, Christopher Musa tare da wasu jami'an soji Hoto: @DHQNigeria
Source: Twitter

An kafa DICON a shekarar 1964, kuma ita ce cibiyar farko ta Najeriya da ke da alhakin kera makamai da harsasai ga Sojojin Najeriya.

Bam ya tashi da kananan yara a Borno

A wani labarin, kun ji cewa wani bam da aka dauko daga bayan gari bisa rashin sani ya tarwatse a yankin karamar hukumar Konduga ta jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa mutum biyu sun rasa rayukansu yayin da wasu hudu sun samu raunuka sakamakon fashewar bam din.

Kara karanta wannan

Jiragen yakin sojin saman Najeriya sun jefa bama bamai a Borno, an kashe ƴan ta'adda

An ce wasu yara su shida da ke harkar gwangwan ne suka dauko bama-bamai ba tare da sani ba, a tunaninsu karafa ne da za su sayar su samu kudi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262