Cire Tallafi da Kalaman Sarki Sanusi II 3 da Suke Ci Gaba da Tayar da Kura a Arewa
- Sarki Muhammadu Sanusi II ya sha yin korafi kan matsalolin da ke damun yankin Arewacin Najeriya tare da kawo mafita
- Wasu al'ummar Kano da sauran jihohin yankin ba su jin dadin abin da yake fada game da koma baya da ake samu a
- Duk da haka akwai wadanda suke ganin duk abubuwan da yake fada gaskiya ne inda ake yabonsa da fadin gaskiya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II yana daga cikin sarakunan gargajiya a Arewacin Najeriya da ke fadin albarkacin bakinsu kan lamura da dama.
Basaraken wanda ke da ilimin boko da na addinin Musulunci bai boye gaskiya idan ta kama game da abin da yake ganin shi ne daidai.

Source: Twitter
Kalaman Sanusi II da suka ta da kura
A Arewacin Najeriya, mutane da dama na sukar irin kalaman da Sarkin ke yayin da wasu ke ganin cewa shi ne kawai ke fadan gaskiya a yankin, cewar rahoton Punch.
Legit Hausa ta yi duba kan wasu kalamai da Sarkin ya yi a baya wadanda suka tayar da kura a yankin Arewacin Najeria.
1. 'Ku gina makarantu ba masallatai ba'
Tun a shekarun baya, Sarki Sanusi II ya taba bayyana damuwa kan yadda ake ta kokarin gina masallatai a Arewa.
Sarkin yayin wani taro a watan Janairun 2017 ya taba cewa bai ga amfanin gina masallatai ba yayin da ake fama da rashin ingantaccen ilimi.
Basaraken ya ce ana yawan kawo masa korafi kan gina masallaci amma kuma an bar yaran mutane a cikin jahilci da rashin makarantu.
“Na gaji, mutane suna zuwa wurina suna ce min suna son gina sabon masallaci, kun sani, kullum ana ta gina masallatai amma ‘ya’yanmu mata suna zaman jahilai.
"Don haka, roƙona shi ne, idan da gaske kuke son taimakon Kano, kar ku zo wurina da neman ku gina min masallaci mai kudi Naira miliyan 300, domin masallatai sun isa ko ina.
"Idan ma ban da masallaci, zan iya gina na kaina. Amma idan kuna so ku taimaka da gaske, ku tafi ku ilimantar da ‘ya mace a kauye."
2. Maganar cire tallafin man fetur
Har ila yau, Muhammadu Sanusi II ya bayyana damuwa kan yadda aka ci gaba da biyan tallafin man fetur a kasa a baya.
Sarkin tun yana gwamnan babban Najeriya yana daga cikin masu goyon bayan cire tallafin mai a lokacin mulkin Goodluck Jonathan.
Tun a mulkin Jonathan aka yi kokarin cire tallafin man fetur amma lamarin ya yi zafi wanda ya jawo zanga-zanga mai tsanani a lokacin.
Ko a kwanan nan, Sanusi II ya bayyana cewa cire tallafin man fetur ya ceci kasar daga durkushewa, yana mai ba matasa shawara.
Sanusi II ya bayyana cewa cire tallafin man fetur ba abu ne da za a yi siyasa da shi ba, domin ya ceci Najeriya daga karyewa.
“Tallafin da ake biya kawai muna bai wa Turai aiki ne, muna tallafa musu maimakon masana’antar mu ta cikin gida ta amfana.”

Kara karanta wannan
'Dan Najeriya ya jefa kansa a badakalar 'kudin gado' a Amurka, kotu ta yanke hukunci
- Cewar Sanusi II

Source: UGC
3. Auren mace fiye da 1 a yankin Arewa
Sarkin ya kuma yi magana kan masu kara aure a Arewa musamman wadanda ba su da karfin rike mata biyu, cewar rahoton Sahara Reporters.
Mai Martaba ya ce abin takaici ne yadda mutanen Arewa suka dauki kara aure kamar gasa da juna duk da yawan talauci a yankin.
Ya ce mafi yawan masu kara auren ba za su iya rike mata daya ba kuma suna haihuwar yara da ba za su iya daukar mauyinsu ba da ke kara talauci da koma baya a yankin.
4. Kalaman Sanusi kan maza masu dukan mata
Mai martaba Sanusi II ya kuma tabo maganar yawan cin zarafin mata da maza ke yi musamman a Arewacin Najeriya.
Sarkin ya nuna matukar damuwarsa kan yadda fyade da kuma yadda maza ke dukan matansu ke zama ruwan dare a jihar Kano.
Muhammadu Sanusi II ya gargaɗi masu riƙe da sarautun gargajiya da su guji abin da zai raba su da rawaninsu.
Mai Martaba ya bayyana cewa duk basaraken da masarauta ta samu labarin ya na bugun matarsa, to ya yi bankwana da rawanin da aka naɗa masa.
Shehi ya dura kan Sanusi II kan kalamansa
Malamin Musulunci, Sheikh Musa Yusuf Assadussunnah ya shawarci Sarki Sanusi II da ya ji tsoron Allah SWT kan kalamansa.
Malamin ya ce abin takaici ne yadda basaraken da ke ikirarin ilimin addini zai furta cewa mata su rama idan mazajensu sun mare su.
Hakan na zuwa ne bayan Sarki Muhammadu Sanusi II ya maimaita cewa duk matar da mijinta ya mare ta, to ta rama.

Source: Facebook
Sanusi II ya jagoranci sallar jana'izar Sarkin Gabas
Mun ba ku labarin cewa Masarautar Kano ta tabbatar da rasuwar Sarkin Gabas, Hakimin Kabo, Alhaji Idris Muhammad Adamu Dankabo, bayan hatsarin mota da ya rutsa da shi.
Bayanai daga shafin Sanusi II Dynasty sun bayyana cewa marigayin ya kasance shugaba mai saukin kai, mai kyakkyawar mu’amala da jama’a.
Sarki Muhammadu Sanusi II shi ya jagoranci sallar jana'izar marigayin wanda aka yi a jiya Juma'a 19 ga watan Satumbar 2025.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


