'Yan Najeriya Sun Fadi 'Wanda' Suke So Tinubu Ya Nada Shugaban INEC

'Yan Najeriya Sun Fadi 'Wanda' Suke So Tinubu Ya Nada Shugaban INEC

  • Wasu ‘yan Najeriya sun bukaci a nada shugaban INEC mai karfin hali, nagarta da kwarewa ba tare da la’akari da kabilanci ko addini ba
  • Masu ruwa da tsaki sun ce dole ne sabon shugaban ya kasance mai mutunci, jajircewa da ikon tsayuwa da kafarsa wajen yin aiki
  • An jaddada bukatar canza tsarin nada shugaban INEC domin tabbatar da adalci da dogaro da tsarin dimokuradiyya a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Wa’adin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, zai kare cikin wata biyu masu zuwa.

Lamarin da ya tayar da muhawara kan irin shugaba da ya kamata a nada a matsayin magajinsa, musamman saboda zaben 2027.

Shugaban INEC da ke kokarin kammala wa'adinsa
Shugaban INEC, Mahmud Yakubu, da ke daf da kammala wa'adinsa. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Daily Trust ta tattauna da kungiyoyi da masu ruwa da tsaki a harkar dimokuradiyya kan wanda suke ganin ya kamata ya shugabanci hukumar INEC bayan Mahmood Yakubu.

Kara karanta wannan

Sakkwato: Shugabannin makarantun sakandare 6 sun tsunduma kansu a matsala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ra’ayoyin sun sha bam-ban, amma duk sun yi nuni da muhimmancin shugaba mai gaskiya wanda zai iya jawo amincewar al’umma, da kuma gyara matsalolin da ake ta fama da su a tsarin zabe.

Bukatar shugaban INEC mai karfin hali

Shugaban Arewa Defence League, Multala Abubakar, ya ce dole sabon shugaban INEC ya zama mai jajircewa kamar tsohon shugaban hukumar, Farfesa Attahiru Jega.

Ya jaddada cewa batun yanki, addini ko kabila bai kamata ya zama sharadi ba, domin abin da ake bukata shi ne wanda zai iya kawar da magudin zabe.

Haka kuma ya nuna cewa tsarin da ake ciki na barin shugaban kasa ya nada shugaban INEC na iya sa a dauko wanda zai fifita muradun jam’iyyarsa.

Ana so dole kwararre ya rike INEC

Wani malamin jami’a, Joseph Kyuior ya ce ya kamata sabon shugaban INEC ya zama mai basira da kwarewa.

Ya kara da cewa ya kamata ya kasance malami a jami’a mai akalla digirin PhD a fannin zamantakewa.

Kara karanta wannan

Daga Kaduna, Taraba da wasu jihohi ake kai hari a Filato inji rahoton gwamnati

Tsohin shugaban hukumar INEC, Farfesa Jega tare da Tinubu
Tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Jega tare da Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

A nasa bangaren, Emmanuel Onwubiko, jagoran wata kungiyar farar hula, ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne kishin kasa da wadatar zuci.

Ya ce dole sabon shugaban ya zama wanda zai iya tsayawa gaban shugaban kasa ya ki amincewa da kowane yunkuri na murdiya.

Nnachi ta ce ana son mai fasaha

Wata mai fafutukar kare hakkin mata, Eunice Nnachi, ta ce abin da ya fi muhimmanci shi ne a samu mutum mai gogewa da mutunci.

Ta ce yana da kyau idan sabon shugaban ya mallaki ilimi a fannin gudanar da harkokin zabe, doka ko fasaha domin tabbatar da amfani da tsarin zamani wajen gudanar da zabe.

Haka kuma Edward Akpen ya ce ya kamata sabon shugaban INEC ya zama mutum mai gaskiya wanda ba zai bar siyasa ta rinjaye shi ba.

INEC: Buba Galadima ya yi gargadi

A wani rahoton, kun ji cewa daya daga cikin jagororin jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya yi magana kan nada shugaban INEC.

Kara karanta wannan

Majalisar Rivers ta ba Fubara umarnin gaggawa kan kasafin kudi da kwamishinoni

Yayin wata hira da aka yi da shi, Buba Galadima ya bayyana cewa ana rade radin shugaban kasa zai nada wani tsohon alkali.

Sai dai ya yi ikirarin cewa tsohon alkalin ba shi da tarihi mai kyau kuma nada shi zai iya jawo yakin basasa a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng