Abin Kunya: An Kama Masu Karkatar da Kudin Tallafin 'Taki' da Ake Rabawa Talakawa a Katsina
- An kama mutanen da aka dauka a garuruwan karkara domin raba tallafin taki da laifin karkatar da miliyoyin Naira a jihar Katsina
- Hukumar Yaki da Cin Hanci ta Katsina (KTPCACC) ta ce wasu daga cikin wadanda ake zargi sun fara dawo da kudin
- Haka zalika, hukumar ta fara bincike kan wasu shugabannin makarantun sakandire bisa zargin karkatar da kudin gudanarwa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Hukumar Ƙorafe-ƙorafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Katsina (KTPCACC) ta fara bincike kan zargin almundahana a rabon takin mai rahusa ga talakawa.
Hukumar ta fara bincike kan batan ₦188.6m a shirin rabon taki da wasu kansiloli da jami’an unguwanni suka gudanar, kudin makarantu da almundahana a ma'aikatar kudi.

Source: Facebook
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar KTPCACC ta fitar a jihar Katsina, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Yadda aka karkatar da N46m a shirin rabon taki
Ta bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa kansiloli da jami'an unguwanni (CDOs) sun karkatar da kuɗi har ₦46,061,000 a lokacin rabon taki mai rahusa ƙarƙashin shirin Community Development Programme.
Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin wadanda ake zargi sun amsa laifinsu kuma sun fara mayar da kuɗin, yayin da ake ci gaba da bincike kan wasu.
Sanarwar ta lissafa yawancin jami’an unguwanni daga ƙananan hukumomin Musawa, Malumfashi, Matazu, Faskari da Funtua a matsayin wadanda ake zargi da lakume ₦52,000 zuwa sama da ₦25m ba bisa ƙa’ida ba.
An taso wasu shugabannin makarantu a Katsina
KTPCACC kuma na bincikar shugabannin sakandare hudu a Danja, Rimaye, Maigora da Kurami kan zargin rashin gaskiya wajen sarrafa kuɗin makarantu har ₦6,628,800.
Ɗaya daga cikinsu ya ƙara fuskantar zargin sayar da kayayyakin makaranta da darajarsu ta kai “miliyoyin Naira” da ba a bayyana adadinsu ba.
A wani lamari daban, hukumar ta bayyana cewa tana ci gaba da karɓar kuɗaɗen da aka karkatar daga Sashen Harkokin Kudi da Banki na Jihar Katsina, inda ake zargin an wawure ₦136,126,970.

Source: Facebook
Hukumar KTPCACC ta kwato miliyoyin Naira
Ta ce zuwa yanzu wadanda ake zargi sun dawo da kimanin ₦70,370,000, sauran Naira miliyan 34, cewar rahoton Daily Post.
Shugaban hukumar, Dr. Jamilu M. Abdulsalam, ya jaddada kudirin KTPCACC na tabbatar da gaskiya da rikon amana tare da kira ga jama’a su rika ba da rahoton cin hanci da rashin gaskiya.
“Za mu bi dukkan hanyoyin da doka ta tanada domin tabbatar da riƙon amana da kuma dawo da dukiyar al’umma,” in ji sanarwar.
Daraktan SRRBDA ya karkatar da N305,000
A wani rahoton, kun ji cewa Babbar Kotun Katsina ta yanke wa darakta a hukumar SRRBDA, Rabiu Musa Matazu hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari.
ICPC ta ce babbar kotun ta samu Rabiu Musa Matazu, Daraktan Sashen Gudanarwa na hukumar SRRBDA, da laifi a kan tuhume-tuhume hudu da aka shigar kansa.
Tun farko, lauyoyin ICPC sun shaida wa kotu cewa Rabiu Matazu ya karɓi N305,000 da sunan hukumar, sannan ya karkatar da kudaden zuwa aljihunsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

