'Yan Ta'adda Sun Tilastawa Sojoji Tserewa bayan Kai Hari a Borno
- 'Yan ta'adda dauke da makamai sun yi ta'asa bayan kai wani harin ta'addanci a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas na Najeriya
- Harin ya jawo an yi musayar wuta mai tsanani tsakanin 'yan ta'addan da dakarun sojoji, wadda ta dauki dogon lokaci
- Daga baya, 'yan ta'addan sun kwashe makamai a sansanin sojoji bayan jami'an tsaro sun ja da baya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Ana zargin ‘yan ta’adda sun kai farmaki a garin Banki, wanda yake kan iyaka a jihar Borno
'Yan ta'addan sun kai harin ne da daddare a ranar Alhamis, inda suka kwashe makamai daga sansanin sojoji.

Source: Twitter
'Yan ta'adda sun kai hari a Borno
A cewar rahoton gidan labaran Reuters, harin wanda ya faru a karamar hukumar Bama ya fara ne da misalin karfe 9:30 na dare.
Harin ya ɗauki sa’o’i har zuwa safiyar ranar Juma’a, wanda hakan ya tilastawa sojoji tserewa daga sansaninsu.
Yadda 'yan ta'adda su ka yi ta'asa
Wata takardar cikin gida daga rundunar CJTF wadda ke taimako da goyon bayan sojoji wajen yaki da ‘yan ta’adda, ta bayyana cewa maharan sun kwace garin tare da kutsawa cikin sansanin sojoji.
Wani bangare na takardar na cewa:
"Yan ta’addan sun kwace garin sannan suka shiga sansanin sojoji, inda suka sace harsasai da makamai."
“Kwamandan rundunar da sojoji sun bar sansanin, inda suka tsere zuwa Kamaru, suka bar fararen hula."
Wani mazaunin Banki, Aliyu Haruna, ya ce a safiyar Juma’a ya ga akalla gawarwaki bakwai a garin, ciki har da na sojoji uku.
"Dukkan jami’an tsaro, na sojoji da na sa-kai, sun tsere zuwa Kamaru, sai da safiyar Juma'a suka dawo."
- Aliyu Haruna
Dakarun Sojoji sun ja da baya
Maharan sun iso garin da yawa, inda su ka tilasta wa dakarun tsaro ja da baya bayan musayar wuta mai tsanani, sannan daga baya suka sake dawo wa garin da safe a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan
Sauki ya samu da aka hallaka tantirin dan bindiga yana cikin shirya kai mummunan hari
Wani soja daga bataliya ta 152 da ke Banki ya tabbatar da cewa maharan sun iso da yawa, lamarin da ya sa dakarun tsaro suka ja da baya bayan an yi musayar wuta mai zafi.

Source: Original
Me rundunar sojoji ta ce kan lamarin?
Har yanzu rundunar sojojin Najeriya ba ta ce komai ba kan lamarin.
Garin Banki ya taba shiga hannun Boko Haram shekaru 10 da suka gabata, kuma ya sha fuskantar hare-hare daga kungiyar da kuma takwararta ta ISWAP.
Sojojin sama sun kashe 'yan ta'adda a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin sama sun yi barin wuta kan 'yan ta'adda a jihar Borno.
Jiragen yakin rundunar sojojin sama sun jefa bama-bamai bayan samun bayanan sirri kan motsin ‘yan ta’adda a Bula Madibale cikin yankin Gezuwa.
Harin ya yi sanadiyyar hallaka 'yan ta'adda da dama tare da rusa gine-ginensu da sauran kayayyakin da su ke amfani da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
