An Daura Auren Dan Kwankwaso da 'Yar Kalarawi ba tare da Sanar da Duniya ba

An Daura Auren Dan Kwankwaso da 'Yar Kalarawi ba tare da Sanar da Duniya ba

  • Ɗan tsohon gwamnan Kano, Mustapha Rabiu Kwankwaso, ya ɗaura aure da Sayyada Zulaihat Tijjani Kalarawi
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya nema wa Mustapha auren a madadin mahaifinsa, Rabiu Musa Kwankwaso
  • Kwankwaso ya yi godiya ga manyan baki da jama’a da suka hallara tare da yin addu’a ga sababbin ma’auratan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – An gudanar da ɗaurin auren ɗan tsohon gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Mustapha Rab’iu Kwankwaso.

Rahotanni sun bayyana cewa an daura auren ne a jihar Kano ba tare da sanarwa sosai ba kamar yadda aka yi na 'yar uwarsa a baya.

Yadda aka daura auren Mustapha Kwankwaso a Kano
Yadda aka daura auren Mustapha Kwankwaso a Kano. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanai kan yadda aka daura auren ne a wani sako da Sanata Rabiu Musa ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

2027: Yadda Kwankwaso ya sha yabo da raddi kan maganar yiwuwar shiga APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An daura auren Mustapha Kwankwaso

A ranar Juma'a, 19 ga watan Satumban 2025 aka daura auren Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso da Sayyada Zulaihat Tijjani Kalarawi, a birnin Kano.

Bikin ya samu halartar jama’a daga sassa daban-daban na jihar, inda Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nema wa Mustapha izinin auren a madadin jagoransa na siyasa, Kwankwaso.

Sanata Kwankwaso ya taya murnar aure

A cikin saƙonsa, Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna farin ciki da wannan rana ta musamman da ya shaida auren dansa.

Baya ga haka, madugun Kwankwasiyya ya yi addu’ar Allah ya sa auren ya kasance mai albarka ga Mustapha da Zulaihat.

Waye Mustapha Rabiu Kwankwaso?

Mustapha Rab’iu Kwankwaso ya taso ne a cikin tafarkin siyasa, kasancewar ɗa ga shahararren ɗan siyasa a Najeriya.

A watan Maris 2024, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa shi a matsayin kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa an rantsar da shi a watan Afrilu bayan tabbatarwa daga majalisar dokoki.

Kara karanta wannan

NECO: Kwankwaso ya yabi aikin Abba bayan daliban Kano sun doke na sauran jihohi

Mustapha Kwankwaso tare da mahaifinsa yayin daurin aure
Mustapha Kwankwaso tare da mahaifinsa yayin daurin aure. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Tun daga lokacin yake jagorantar shirye-shiryen matasa da inganta harkokin wasanni a jihar Kano.

Duk da haka, Mustapha na taka rawarsa cikin natsuwa, ba tare da tsunduma cikin lamuran siyasa sosai ba kamar mahaifinsa.

Premium Times ta rahoto cewa baya ga siyasa, Mustapha ya shugabanci Key Special Academy a Abuja, makarantar da ke ƙarƙashin kulawar mahaifinsa, kafin ya tsunduma gwamnati kai tsaye.

An daura auren babu gayyata sosai

Binciken Legit ya gano cewa an daura auren ne ba tare da gayyata sosai ba kamar yadda aka saba gani a auren 'ya'yan manyan 'yan siyasa.

Legit ta bibiyi shafukan sada zumuntan Rabiu Kwankwaso da gwamna Abba Kabir Yusuf ba tare da ganin sanarwar gayyatar auren ba.

Haka zalika ba a wallafa gayyatar auren ba a shafin mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa.

An daura auren dan Sanata Yari

A wani rahoton, kun ji cewa an daura auren dan Sanata Abduaziz Yari a jihar Kaduna ranar Juma'a, 19 ga Satumba 2025.

Kara karanta wannan

Yayin da Kwankwaso ke taro a Kano, Barau ya janye 'yan NNPP zuwa APC

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na cikin manyan bakin da suka hallara auren.

Haka zalika sauran manyan kasa da suka hada da gwamnoni, ministoci, Sanatoci da manyan malamai sun halarci bikin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng