Matatar Dangote Ta Dakatar da Hulda da Wasu Yan Kasuwa a Najeriya, Ta Fadi Dalilai

Matatar Dangote Ta Dakatar da Hulda da Wasu Yan Kasuwa a Najeriya, Ta Fadi Dalilai

  • Kamfanin man fetur na Dangote ya dakatar da sayar da kaya ga wasu ’yan kasuwa tun daga 18 ga Satumbar 2025 da muke ciki
  • Kamfanin ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan gyara ne don inganta aiki tare da tilasta ’yan kasuwa shiga tsarin 'Free Delivery Scheme'
  • Matatar ta nemi afuwar duk wani cikas da hakan ka iya jawowa tana mai cewa tsarin zai daidaita samar da kaya, rage farashi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Matatar Dangote ta dakatar da sayar da kaya ga wasu yan kasuwa saboda rashin cika ka'ida wanda ake kokarin kawo sauyi.

Matatar Dangote ta ce matakin wanda ya fara aiki daga ranar 18 ga Satumba, 2025 ya zama dole saboda inganta ayyukanta da samar da kaya cikin sauki.

Matatar Dangote ya dakatar da sayar da kaya ga waya yan kasuwa
Matatar Alhaji Aliko Dangote da ya gina a Najeriya. Hoto: Dangote Group.
Source: UGC

Dangote ya kawo sababbin tsare-tsaren ciniki

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Malamin da ya fi 'tsufa' yana wa'azi ya bar duniya yana shekaru 95

An tattaro cewa wannan mataki yana nufin karfafa tsarin rarraba man fetur kyauta ga yan kasuwa da dakatar da sayarwa ga marasa rajista, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin ya bayyana cewa matakin gyara ne na aiki da aka dauka don inganta lamura da sauƙaƙa harkokin rarraba man fetur a kasar.

A cikin wata wasika, sashen kamfanin ya ce:

"Muna sanar da ku cewa daga ranar 18 ga watan Satumba, matatar Dangote ta dakatar da tsarin karbar kaya da kai ga wasu yan kasuwa domin kawo sauyi a lamarin."
Matatar Dangote ta kawo sababbin tsare-tsare kan sayar da kaya
Shugaban kamfanin Dangote a Najeriya, Aliko Dangote. Hoto: Dangote Industries.
Source: Getty Images

Bukatar matatar Dangote ga 'yan kasuwa

Kamfanin ya bukaci ’yan kasuwa su rungumi tsarin 'raba kaya kyauta ga yan kasuwa' wanda ke kawo kaya kai tsaye zuwa masu sayan man fetur cikin sauƙi.

Sanarwar ta ce:

"Muna kira ga abokan huldarmu tsofaffi da sababbi da su yi rijista da tsarin 'DPRP Free Delivery Scheme' domin samar da kaya cikin sauki.
"Muna ba da hakuri kan wannan tsari da ka iya jawo matsala ga wasu, kuma muna godiya da fahimta da kuma goyon baya yayin da muke kokarin kawo sauyi."

Kara karanta wannan

Kiristoci sun yi magana kan dokar wa'azin addini a Niger, sun fadi matsayarsu

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake rikici tsakanin kamfanin da kungiyar NUPENG da kuma DEPMA a kan batun tallafin man fetur, Punch ta ruwaito labarin.

Kamfanin ya ce tsarin 'Free Delivery Scheme' wanda aka kirkiro shi don daidaita samar da kayayyaki da kuma rage farashi ga ’yan kasuwa ana ganin zai kawo sauki ga al'umma.

Matatar Dangote ta jaddada cewa tana da hakkin kare ayyukanta daga rahotanni da ke bata suna, musamman kan bukatar tallafin Naira tiriliyan 1.505 da ’yan kasuwa ke yi.

Dangote ya magantu kan tallafin mai

Mun ba ku labarin cewa kungiyar DAPPMAN ta bai wa Aliko Dangote wa’adin kwana bakwai ya janye zargin karkatar da man fetur ko ya kawo hujja.

Dangote ya ce ‘yan kasuwa sun nemi tallafin da ya kai Naira tiriliyan 1.5 a shekara domin daidaita farashi da na matatarsa duba sa sauran farashi a wasu wurare.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da bugawa tsakanin Dangote da masu dakon mai kan shiri fara raba fetur kyauta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.