Tashin Hankali: An Samu Gawar Shugaban Hukumar NDLEA a Wani Irin Yanayi a Dakin Otal
- An shiga fargaba bayan samun gawar shugaban hukumar NDLEA reshen jihar Cross River a dakin otal wanda ya tayar da hankali matuka
- An tsinci gawar Morrison Ogbonna a wani otal da ke Calabar ranar Alhamis 18 ga watan Satumbar 2025 da muke ciki
- Abokan aikinsa da suka zo daukarsa sun ce sun buga ƙofa sau da yawa ba tare da amsa ba, daga bisani aka same shi matacce
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Calabar, Cross River - Hankulan al'ummar birnin Calabar da ke jihar Cross River sun tashi da wani mummunan lamari ya faru a yankin.
An samu gawar kwamandan NDLEA reshen jihar Cross River da ake kira Morrison Ogbonna a wani otal da ke Calabar.

Source: Original
Yadda aka tsinci gawar shugaban NDLEA
Rahoton TheCable ta ce abokan aikinsa da suka je daukarsa don wani aiki ranar Alhamis da safe ne suka gano gawarsa a cikin ɗakin otal ɗin.
Suka ce sun yi ta buga kofa sau da dama amma babu wanda ya amsa wanda shi ne babban abin da ya tayar musu da hankali.
“Sun buga ƙofa sau da dama ba tare da samun amsa ba, sai suka sanar da hukumar otal, inda aka buɗe ɗakin aka tarar da shi gawarsa."
- Cewar wata majiya
Marigayi kwamandan ya samu sauyin aiki zuwa Cross River a watan Agusta domin ya maye gurbin Rachel Umebuali, wadda ta rike matsayin a baya.

Source: Twitter
Yan sanda sun magantu kan mutuwar marigayin
Mutuwarsa ta bazata ta girgiza hukumar NDLEA baki ɗaya, inda jami’an hukumar ke cikin tashin hankali da rashin yarda da lamarin, Vanguard ta tabbatar da rahoton.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Cross River, Irene Ugbo-Obase, ta tabbatar da lamarin, tare da bayyana cewa bincike ya fara kan yadda ya rasu.
Obase ta ce rundunar ta fara bincike don gano ainihin abin da ya faru saboda sanin matakin da za a dauka kan lamarin.
Har ila yau, ta bukaci al'umma ta su rika ba hukumomi hadin kai da goyon baya domin bincike musamman kan irin wadannan abubuwa da ke faruwa masu ɗaure kai.
Wane martani hukumar NDLEA ta yi kan lamarin?
Har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto, hukumar NDLEA ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan mutuwar kwamandan ba.
Hukumar ita ce ke yaki da safara da kuma ta'ammali da miyagun kwayoyi a Najeriya domin tabbatar da tsaftace harkokin magani.
NDLEA ta kama dilan kwayoyi a Lagos
Mun ba ku labarin cewa jami'an hukumar NDLEA sun kama Okpara Paul Chigozie, shugaban dillalan kwayoyi da ake nema ruwa a jallo tun 2019, a jihar Lagos.
An gano kilo 7.6 na hodar iblis da giram 900 na methamphetamine a cikin motarsa, yayin da aka gano karin kwayoyi a gidansa wanda ya tayar da hankali.
A wani samame na daban, hukumar NDLEA tare da FAAN sun kwato kwayoyin tramadol da Rohypnol guda 7,790 a hannun wani fasinjan Italiya da ake zargin za a safarar kayan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

