An Cafke 'Dan Najeriya bayan Ya Yi wa Amurka Kutse Ya Yi Babbar Sata
- An cafke wani dan Najeriya da ke zaune a Birtaniya bisa buƙatar Amurka saboda zargin kutse a kwamfuta da damfara ta waya
- An ce matashin ya yi amfani da dabarun fasahar zamani wajen karkatar da kuɗin wata jami’a da ya kai $235,266 zuwa asusun bogi
- Yanzu haka yana fuskantar tuhuma guda bakwai, inda zai iya fuskantar hukuncin shekaru 22 a kurkuku kan damfara da yin kutse
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka - Hukumar shari’a ta Amurka ta bayyana cewa an cafke wani ɗan Najeriya mai suna Farouk Adekunle Adepoju, wanda ke zaune a Birtaniya.
An kama matashin ne bisa zargin kutse ta kwamfutoci da damfara da ta kai ga asarar $235,266 (Sama da Naira miliyan 300).

Source: UGC
Vanguard ta wallafa cewa an kama shi a ranar 15 ga Satumba, 2025, inda hukumomin Birtaniya suka fara shirye-shiryen mika shi ga Amurka domin fuskantar shari’a a Pennsylvania.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton tuhumar ya nuna cewa tsakanin watan Maris zuwa Afrilu 2023, Adepoju ya kutsa cikin kwamfutar wani kamfanin gine-gine da ke aiki tare da jami’a a Pennsylvania.
Bayan kutsen, an ce ya sauya imel din kamfanin, ya ƙirƙiri asusun imel na bogi, sannan ya yaudari jami’ar ta aika kuɗi zuwa wani asusu na jabu.
Bayanin masu shari’a a Amurka
Lauyan Amurka, Troy Rivetti, ya bayyana cewa Adepoju ya yi amfani da dabaru na zamani wajen shiga asusun wani kamfani da kuma karkatar da kuɗi daga jami’ar.
Legit ta rahoto cewa Troy Rivetti ya ce hakan babban laifi ne da ya yi barazana ga tsaro da dukiyar jama’a.
Rivetti ya ƙara da cewa:
“Kodayake yana can a wani yanki na duniya, hakan bai hana FBI gano shi da kuma ɗaukar matakin kawo shi gaban shari’a ba.”
Rawar da FBI ta taka wajen kama shi
Shugaban ofishin FBI na Pittsburgh, Kevin Rojek, ya ce wannan lamari darasi ne ga duk masu laifi da ke tunanin za su iya yin kutse daga nesa domin tara dukiya.
Ya jaddada cewa FBI ba za ta lamunci irin waɗannan ayyuka ba, kuma tana da haɗin gwiwa da sauran hukumomi wajen kamo masu aikata laifi ko da suna waje.

Source: Getty Images
Tuhume tuhume kan dan Najeriya
Rahoton ya tabbatar da cewa Adepoju na fuskantar tuhuma bakwai, ciki har da shida na damfarar waya, wanda kowanne zai iya jawo hukuncin shekaru 20 a kurkuku idan aka same shi da laifi.
Haka kuma akwai tuhuma guda ɗaya ta kutse a kwamfuta, wacce take ɗauke da hukuncin shekaru biyar a gidan yari.
A cewar rahoton, har yanzu ba a samu kuɗin da aka karkatar ba, wanda hakan ya kara ɗaga girman laifin da ake tuhumarsa da shi.
A halin yanzu, Adepoju yana tsare a hannun hukumomin tsaron Birtaniya yayin da ake jiran cikar takardun shari’ar mika shi zuwa Amurka.
An yi wa Trump zanga zanga
A wani rahoton, kun ji cewa mutanen da ba su gaza 5,000 ba ne suka taru a London domin yi wa Donald Trump zanga zanga.
Hakan na zuwa ne yayin da Trump ya ziyarci kasar Birtaniya karo na biyu domin tattaunawa da hukumomi.

Kara karanta wannan
'Dan Najeriya ya jefa kansa a badakalar 'kudin gado' a Amurka, kotu ta yanke hukunci
Masu zanga zangar sun nuna adawa da wasu tsare tsaren gwamnatin Trump da cigaba da kashe Falasdinawa da ake yi a Gaza.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

