A Wani Matsayi za a Karbi NNPP, Kwankwaso Ya Yi Maganar Yiwuwar Shiga APC

A Wani Matsayi za a Karbi NNPP, Kwankwaso Ya Yi Maganar Yiwuwar Shiga APC

  • Jagoran Kwankwasiyya na kasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya fara magana a kan koma wa jam'iyya mai mulki ta APC
  • Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa sun ji kiraye-kirayen da wasu ke yi na neman su sauya sheka, kuma za su iya amsa wannan kira
  • Ya bayyana cewa su ne suka kafa APC, kuma sun yi mata gwagwarmaya sosai, saboda haka dole a cika wasu sharudda kafin su zo

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya mayar da martani ga masu sukar sa kan yiwuwar komawarsa jam’iyyar APC mai mulki.

A wani jawabi da ya yi a Kano, Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa su ne suka tsaya suka fafata suka kuma gwagwarmaya wajen kafa jam’iyyar da ke mulki a yau, wato APC.

Kara karanta wannan

NECO: Kwankwaso ya yabi aikin Abba bayan daliban Kano sun doke na sauran jihohi

Sanata Kwankwaso ya ce zai iya koma wa APC
Hoton Sanata Rabai'u Musa Kwankwaso, tsohon Gwamnan Kano Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

A wata hira da aka wallafa a shafin Facebook na Premier Radio, Kwankwaso ya bayyana cewa duk wanda ya ce su shiga APC, sun yarda da hakan, amma akwai wasu sharudda kafin hakan ya tabbata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso: 'Mu muka kafa jam'iyyar APC'

Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa su ne suka kasance a sahun gaba wajen kalubalantar gwamnatin tarayya a wancan lokaci.

Ya ce suna daga cikin wadanda suka yi tsayin daka wajen ganin an kafa jam’iyyar APC, duk da kalubalen da suka fuskanta daga jami’an tsaro da kuma gwamnatin wancan lokaci.

Sanata Kwankwaso ya ce:

“A wannan ƙasar, wa zai gaya mana irin rigima da tashin hankali da muka fuskanta wajen kafa APC? Ai mu muka kafa ta. Mu ne muka yi jagoranci, muka tsaya muka yi aiki. Mu muka kalubalanci gwamnatin tarayya.”
“Babu irin rigima da ba a gani ba. Har ‘yan majalisarmu an zo an kwashe su, an kulle su a Abuja. Babu irin zirga-zirgar bincike da ba a yi min ba — EFCC, ICPC, ‘Yan sanda, SSS — kowa ya sa hannu. Amma duk da haka mu muka kafa jam’iyyar.”

Kara karanta wannan

Yayin da Kwankwaso ke taro a Kano, Barau ya janye 'yan NNPP zuwa APC

“Mu muka fara tun daga Eagle Square, jihohi bakwai muka fita, duk waɗancan abubuwa yanzu tarihi ne.”

Kwankwaso ya bayyana sharadin komawa APC

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa sun amince da sauya sheka zuwa APC, amma sai an ba su tabbacin abin da za su samu a matsayin jam'iyya.

Kwankwaso ya ba da sharadin koma wa APC
Hoton tsohon Sanatan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Ya ce:

“To ka gaya mana, menene NNPP za ta samu? Babu jihar da ba mu da ɗan takarar gwamna, babu inda ba mu da Sanata, da shugabannin jihohi. Duk waɗannan, menene darajarsu? Saboda haka, ka kawo amsa — mun yarda mu shiga, mun yarda mu yi.”
“Amma kada ka dawo da ni wurin da muka kafa, aka wulakanta mu. APC ta shekara takwas a lokacin Buhari, ko gutsuttsuren goro ba mu gani ba. Balle a ce mun gode.”

Ya bayar da tabbacin cewa, matuƙar aka tabbatar musu da kyakkyawar makoma a jam’iyyar APC, to za su sauya sheka zuwa jam’iyyar mai mulki.

Haka zalika Kwankwaso ya nuna za su iya koma wa PDP idan dai za a shimfida hanyar da mutanensa na jam'iyyar NNPP za su samu madafa.

Kara karanta wannan

Tinubu: Dattawan Arewa sun fusata bayan ikirarin APC kan takarar 2027

Kwankwaso ya gana da Jonathan

A baya, mun ruwaito cewa lamura na siyasa a Najeriya na kara sauya salo yayin da jam’iyyu da ‘yan siyasa ke ta kokarin hada kai domin karbe mulki daga hannun jam’iyyar APC.

Rahotanni sun bayyana cewa bangaren tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, na kokarin jawo jigon jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Rahotanni sun ce hadin gwiwar tsakanin Jonathan da Kwankwaso, idan ta tabbata, na iya haifar da babban tasiri musamman duba da karfin Kwankwaso a Arewacin Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng