Daga Kaduna, Taraba da Wasu Jihohi Ake Kai Hari a Filato Inji Rahoton Gwamnati
- Kwamitin bincike na gwamnatin Plateau ya gano cewa yawancin masu kai hare-hare kananan hukumomin jihar na shigowa ne daga jihohi makwabta
- Kwamitin ya ziyarci al’ummomi sama da 420 da suka fuskanci hare-hare inda aka tabbatar da asarar rayuka kusan 12,000
- Gwamna Caleb Mutfwang ya ce zai gabatar da rahoton ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma kwararru kan tsaro domin samar da mafita
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Plateau – Wani rahoton bincike da kwamitin musamman da Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Plateau ya kafa ya fitar da rahoto.
Rahoton kwamitin ya nuna cewa masu kai hare-haren da ake ta fama da su a jihar na shigowa ne daga wasu jihohi.

Source: Twitter
Daily Trust ta rahoto cewa cewa shugaban kwamitin, Manjo Janar Rogers Ibe Nicholas (mai ritaya) ya bayyana cewa sun gana da kabilu da kungiyoyin al’umma daban-daban.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baya ga haka, ya ce sun ziyarci dukkan wuraren da ake ta samun tashin hankali domin tattara bayanai kai tsaye.
Dalilin kai hare-hare a jihar Filato
Rahoton ya kuma bayyana cewa an gano sansanoni a wasu sassan Kananan Hukumomin Wase da Kanam, inda ake zargin suna da alaka da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi.
Nicholas ya ce dalilan da ke haddasa wadannan hare-hare sun hada da neman mallakar kasa da albarkatu, fadada yankuna, rikicin addini da kabilanci, da kuma haifar da rudani na siyasa.
Ya kara da cewa akwai kuma masu amfani da rikicin wajen yin garkuwa da mutane domin kudin fansa da kuma satar shanu.
Daga ina ake kai hari Filato?
A cikin rahoton, an bayyana hanyoyin da ake amfani da su wajen shigowa da fita daga Plateau ba tare da tsaro ba.
Wadannan sun hada da Nasarawa ta Wamba, Lafia da Awe; Kaduna ta Lere, Kaura da Sanga; Bauchi ta Toro, Tafawa Balewa, Bogoro da Alkaleri; da kuma Taraba ta Ibi da Karim Lamido.

Kara karanta wannan
Filato: Bincike ya bankado yadda aka hallaka mutum kusan 12,000 a 'yan shekarun nan
Ya ce wadannan hanyoyi suna taimaka wa masu hare-hare wajen shiga cikin gaggawa, kai farmaki, sannan kuma su tsere cikin sauki ba tare da cikas ba.

Source: Facebook
Matakin gwamnati kan rahoton
A yayin karbar rahoton a fadar gwamnati da ke Jos, Gwamna Caleb Mutfwang ya tabbatar da cewa za a aiwatar da shawarwarin kwamitin domin tabbatar da dorewar zaman lafiya a jihar.
Rahoton This Day ya nuna cewa ya ce zai gabatar da rahoton ga shugaba Bola Tinubu da kwararrun tsaro domin a samar da tsari na dindindin da zai kawo karshen tashin hankali.
Jihar Filato dai ta shafe shekaru da dama tana fama da rikice-rikice da suka hada da na addini da na kabilanci.
Legit ta tattauna da Muhammad
Wani mazaunin karamar hukumar Karim Lamido, Muhammad Abubakar ya bayyanawa Legit cewa sun hada iyaka da Filato kuma su ma sun yi fama da matsalar 'yan bindiga a baya.
Muhammad ya ce:
"Duk wanda ya ke Karim zai tabbatar da cewa ana amfani da iyakar Filato da Taraba wajen kai hari."
"A Taraba an yi amfani da wani mutum dan sa-kai da ake kira Babangida Kwamnada wajen yaki da masu garkuwa."
"Bayan gama wa da 'yan ta'adda a Taraba, Babangida bai samu hadin kan gwamnatin Filato ba."
An kama mai kera makamai a Filato
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta kama wani mutum da ake zargi yana hada bindiga ba bisa ka'ida ba.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama mutumin ne a karamar hukumar Barikin Ladi bayan dogon bincike.
Dakarun Najeriya sun bayyana wa manema labarai cewa sun gano bindigogin gida 12 tare da wasu makamai a wajen mutumin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

