An Shiga Fargaba bayan Ɓacewar Hadimin Gwamna a Hanyarsa Ta Zuwa Abuja
- Al’umma a Benue sun shiga fargaba bayan bacewar mutum biyu ciki har da Atu Terver, hadimin Gwamnan jihar a kan harkokin matasa
- Matarsa, Chivir Terver, ta tabbatar mijinta ya tashi daga Makurdi zuwa Abuja amma bai isa ba, lamarin da ya jefa iyalinsu cikin damuwa
- Rundunar ’yan sanda ta ce ba ta da masaniya kan cafke Asom Jerry, kuma bacewar Terver ta auku ne a birnin Abuja, ba a Benue ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - Al'ummar jihar Benue sun shiga fargaba bayan bacewar mutane biyu daga jihar da aka rasa sama ko kasa.
Fargaba ta mamaye jama’a bayan bacewar wasu matasa biyu, ciki har da wani hadimin Gwamna Hyacinth Alia mai suna Atu Terver.

Source: Facebook
An gano cewa Terver shi ne hadimin gwamna na musamman kan sha'anin matasa da yada labarai, inda aka ce ya bace a hanyarsa ta Makurdi zuwa Abuja, cewar Leadership.

Kara karanta wannan
Kwana ya kare: Malamin da ya fi 'tsufa' yana wa'azi ya bar duniya yana shekaru 95
Yadda yan bindiga suka addabi jihar Benue
Wannan batan matasa biyu a Benue na zuwa ne yayin da jihar ke fama da matsalar tsaro na hare-haren yan bindiga a wasu yankuna.
Lamarin bai ba da mamaki ba yayin da ake zargin batan na da nasaba da ayyukan yan bindiga da suka addabi jihar da yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya.
Al'ummar na ci gaba fatan samun matasan cikin koshin lafiya da kira ga gwamnati da ta yi gaggawar daukar mataki kan lamarin.
An rasa matashi dan gwagwarmaya a Benue
Haka kuma, Asom Jerry wani mai fafutuka a kafafen sada zumunta ya bace, lamarin da ya tayar da cece-kuce, wasu na cewa ’yan sanda sun cafke shi.
Matar hadimin gwamna, Chivir Terver, ta tabbatar da cewa mijinta ya bar Makurdi zuwa Abuja ranar Talata 16 ga watan Satumbar 2025 amma bai isa gare su ba.
Ta ce:
“Ya tafi daga Makurdi ranar Talata zuwa Abuja, amma bai zo gare mu ba. Mun kai korafi ofishin ’yan sanda, suna bincike har yanzu.”

Source: Original
Menene rundunar 'yan sanda ta ce?
Jami’ar hulda da jama’a ta ’yan sanda, Udeme Edet, ta ce ba ta da masaniya kan cafke Jerry da kuma bacewar Terver ta faru ne a Abuja.
Ta kara da cewa tana jin labarin ne daga manema labarai kawai, sannan ta jaddada cewa lamarin ya faru a Abuja, ba a jihar Benue ba.
Edet ta tabbatar da cewa duk lokacin da labarin ya iso ta, za ta yi ƙarin bayani kan lamarin ba tare da bata lokaci ba, cewar Daily Post.
'Yan bindiga sun hallaka bayin Allah a Benue
Mun ba ku labarin cewa an samu asarar rayuka a jihar Benue bayan wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a wani kauye.
'Yan bindigan sun kai harin ne a wani kauye dake karamar hukumar Ogbadibo inda suka bude wuta kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Mummunan harin da 'yan bindigan suka kai ya jawo asarar rayuka da raunata wani matashi wanda hakan ya tilasta aka garzaya da shi zuwa asibiti.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

