Masarautar Kano Ta Yi Babban Rashi, Sarkin Gabas Ya Rasu bayan Hatsarin Mota
- Masarautar Kano ta tabbatar da rasuwar Sarkin Gabas, Hakimin Kabo, Alhaji Idris Muhammad Adamu DanKabo, bayan hatsarin mota da ya rutsa da shi
- Bayanai daga shafin Sanusi II Dynasty sun bayyana cewa marigayin ya kasance shugaba mai saukin kai, mai kyakkyawar mu’amala da jama’a
- Masarautar ta yi addu’ar Allah ya gafarta masa, ya jikansa da rahama, ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdaus mai daraja
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Masarautar Kano ta sanar da rasuwar daya daga cikin masu sarauta a jihar bayan gamuwa da hatsarin mota.
An tabbatar da rasuwar Sarkin Gabas kuma Hakimin Kabo, Alhaji Idris Muhammad Adamu DanKabo a jihar wanda ya bar duniya yana da shekaru 48.

Source: Facebook
Kano: Sarkin Gabas ya riga mu gidan gaskiya
Shafin Sanusi II Dynasty da ke kawo bayanai game da masarautar shi ya tabbatar da haka a jiya Alhamis 18 ga watan Satumbar 2025 a shafin Facebook.

Kara karanta wannan
Kwana ya kare: Malamin da ya fi 'tsufa' yana wa'azi ya bar duniya yana shekaru 95
Sanarwar ta yi jimamin mutuwar marigayin Alhaji Idris wanda ya kasance mutum mai kan-kan da kai da mu'amala da al'umma.
Daga bisani, masarautar ta yi addu'ar Ubangiji ya gafar ta masa ya kuma saka masa da gidan aljanna firdausi.
Sanarwar ta ce:
"“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!.
"Muna sanar da rasuwar Sarkin Gabas, Hakimin Kabo, Alhaji Idris Muhammad Adamu DanKabo.
"Allah ya gafarta masa, ya jikansa da rahama, ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdaus.”

Source: Facebook
Musabbabin rasuwar marigayi Hakimin Kabo a Kano
Majiyoyi sun tabbatar da cewa Hakimin Kabo kuma Sarkin Gabas, Alhaji Idris Adamu Dankabo ya rasu, ya na da shekaru 48 a duniya a jiya Alhamis.
An ce marigayi Alhaji Idris ɗa ne ga marigayi Jarman Kano, Alhaji Muhammad Adamu Dankabo, ya rasu ne sakamakon haɗarin mota a jihar Kano.
Har ila yau, mariagyin ya rasu ya bar mata ɗaya da ƴaƴa biyu inda mutane ke ci gaba da yi masa addu'ar samun rahama.
Yaushe za a yi jana'izar Hakimin Kabo?
Za a yi jana'izar sa a yau Juma'a 19 ga watan Satumbar 2025 da misalin ƙarfe 10 na safe a fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu.
Ana sa ran Sarkin Kano, Khalifah Muhammadu Sanusi ne zai yi masa sallah tare da rakiyar manyan baki a jihar.
Mutane da dama suna da addu'ar neman gafara ga marigayin inda suke yabawa gudunmawar da ya ba al'ummar jihar baki daya.
Sanusi II ya jagoranci jana'izar matar Sanusi I
A wani labarin, an ji Masarautar Kano ta shiga jimami bayan rasuwar iyalin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I, Yaya Jide da 'yarsa, Goggo Ummahani.
Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammad Sanusi II, ne ya jagoranci sallar jana’izar matan biyu a ranar Laraba, 16 ga Yulin shekarar 2025.
Sanusi I ya mulki Kano daga 1954 zuwa 1963, kuma Sanusi II ya fara hawan karagar 2014, sannan ya sake komawa a 2024 bayan Abba Kabir Yusuf ya dawo da shi.
Asali: Legit.ng
