Tinubu zai Je Gidan Buhari, Manyan Kasa za Su Dura Kaduna Auren Dan Sanata Yari

Tinubu zai Je Gidan Buhari, Manyan Kasa za Su Dura Kaduna Auren Dan Sanata Yari

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyara ta kwana ɗaya jihar Kaduna a ranar Juma’a, 19 ga Satumba
  • Yayin ziyarar, shugaban zai halarci daurin auren ɗan Sanata Abdul’aziz Yari tare da sahibarsa, Safiyya Shehu Idris
  • Zai kuma ziyarci Aisha Buhari, matar marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, a gidansu na Kaduna

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyara jihar Kaduna a ranar Juma’a domin gudanar da wasu muhimman al’amura na musamman.

Wannan na zuwa ne a matsayin ziyararsa ta farko ga iyalan tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari, tun bayan komawarsu Kaduna bayan rasuwarsa a watan Yuli.

Tinubu yana dagawa mutane hannu yayin da zai yi tafiya
Tinubu yana dagawa mutane hannu yayin da zai yi tafiya. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Legit Hausa ta tattaro bayanai kan ziyarar ne a cikin wani sako da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

Manyan 'yan siyasa 4 da za su koma bakin aiki bayan janye dokar ta baci a Rivers

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu zai je auren ɗan Sanata Yari

Tinubu zai halarci daurin auren Nasirudeen Yari, ɗan Sanata Abdul’aziz Yari, wanda ke wakiltar Zamfara ta Yamma da amaryarsa Safiyya Shehu Idris.

Ana sa ran bikin zai jawo hankalin manyan baki daga sassan ƙasar nan, ciki har da jami’an gwamnati da jiga-jigan siyasa.

Halartar shugaban kasa auren ta ƙara wa taron muhimmanci, inda ake sa ran haduwa da fitattun shugabanni daga Arewacin Najeriya da sauran jihohi.

Tinubu zai je gidan Marigayi Buhari

Daga cikin shirin ziyarar, Tinubu zai ziyarci Aisha Buhari a gidansu na Kaduna a karon farko bayan komarsu jihar.

Wannan shi ne karo na farko da shugaban zai kai ziyara ga iyalan tun bayan da aka yi jana’izar marigayi Buhari a Daura bayan an dawo da gawarsa daga Landan a watan Yuli.

Tun daga lokacin rasuwar, iyalan Buhari sun koma gidan su na Kaduna, inda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da sauran manyan ‘yan Najeriya suka kai musu ziyara.

Kara karanta wannan

Malami ya shiga rikici da gwamna, ana zarginsa da ingiza ta'addanci a jihar Kebbi

Sai dai zuwa yanzu, Tinubu bai samu damar yin hakan ba har sai wannan ranar Juma’a da ya tsara.

An daura auren jikar Buhari

A ranar 30 ga watan Agustan 2025 aka daura auren daya daga cikin jikokin marigayi shugaba Muhammadu Buhari a Kaduna.

Daurin auren ya samu halartar manyan baki daga Kaduna da ma wasu jihohin Najeriya, kuma Sanata Kashim Shettima ne ya bayar da auren da kansa.

Shettima yayin daura auren jikar Buhari a Kaduna.
Shettima yayin daura auren jikar Buhari a Kaduna@stanleynkwocha
Source: Twitter

Yaushe Tinubu zai koma Abuja?

Punch ta rahoto cewa Onanuga ya bayyana cewa bayan kammala daurin auren da ziyara gidan Buhari, shugaban kasa zai dawo Abuja a ranar Juma'a.

Wannan na nuna cewa ziyarar ba ta da alaka da harkokin gwamnati kai tsaye, illa dai girmamawa da hulɗar zumunci.

Radda ya ziyarci kabarin Buhari

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kastina, Dikko Umaru Radda ya kai ziyara ta musamman kabarin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura.

Gwamna Radda ya kai ziyara kabarin ne tare da jami'an gwamnatin jihar Katsina kuma sun yi ma marigayin addu'o'in samun rahamar Allah.

Kara karanta wannan

Ana maganar sulhu, 'yan bindiga sun farmaki motar jami'an tsaron NSCDC

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan ya halarci wani taron gargajiya ne da aka gudanar a masarautar Daura, wanda ya yi amfani da damar wajen ziyarar marigayin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng