Shehi Ya Soki Zargin Gina Masana’antar Fim, Ya Gargaɗi Gwamna kan Mummunar karshe

Shehi Ya Soki Zargin Gina Masana’antar Fim, Ya Gargaɗi Gwamna kan Mummunar karshe

  • Rahotanni sun nuna ana zargin kafa masana’antar fim a Gombe, lamarin da ya jawo cece-kuce bayan Ali Nuhu ya gana da gwamna
  • Sheikh Adamu Dokoro ya yi gargadi ga gwamnatin Gombe, yana cewa fina-finai ba sa gyaran tarbiya sai dai rusawa
  • Malamin ya yi kira ga gwamna kar ya bata rawarsa da tsalle, yana tunawa da yadda rusar gidajen gala ta jawo masa yabo da addu’o’i

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Wasu rahotanni sun fara yawo cewa ana shirin kafa masana'antar fim a Gombe da ke Arewa maso Gabas.

A kwanakin baya, dan wasan Kannywood, Ali Nuhu ya gana da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da ake zargin suna shirin bunkasa fim a jihar.

An taso gwamna a gaba kan zargin kafa masana'antar fim a Gombe
Ali Nuhu yayin ziyara ga Gwamna Inuwa a Gombe da Malam Adamu Muhammad Dokoro. Hoto: Ali Nuhu Mohammed, Sheikh Adamu Muhammad Dokoro.
Source: Facebook

Gombe: Ana zargin shirin kafa masana'antar fim

Sheikh Adamu Muhammad Dokoro ya yi gargadi mai zafi ga gwamnatin jihar Gombe kan wannan zargi da ake yi a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida zai rage bashin Ganduje, za a biya karin N5bn ga 'yan fansho a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya fadi haka ne a cikin bidiyo, inda ya ce bai kamata gwamnatin ta rusa ayyukan alheri da ta yi ba a baya.

Sheikh Dokoro ya ce kowa ya sani babu abin da fim ke koyarwa sai rashin tarbiya kuma bai kamata a bari hakan ya faru ba.

A cewarsa:

"Duk da cewa ba mu ji ta bakin gwamnati ba, amma muna jin wasu abubuwa suna ta yawo na wasu mutane da ke son kafa masana'antar fina-finai.
"Wannan kowa ya sani har su ma su yin aikin sun sani rusa tarbiya suke yi ba gyaran tarbiya ba, ba mu tabbatar ba amma an yi kokarin yin haka a wasu jihohi bai yiwu ba.
"Ka da wannan gwamnati ta bari ta yi wannan abin, za ta girbi abin da ta shuka tun daga ranar da ta sanya hannu har zuwa kiyama, gwamnan ka sani karara, za ka girbi zunubi kan haka."

Kara karanta wannan

Abin da Gwamna Fubara ya fada kan Tinubu da Wike a jawabinsa na farko a Ribas

An kalubalanci gwamna kan zargin gina masana'antar fim a Gombe
Jarumi Ali Nuhu da Gwamna Inuwa Yahaya yayin da dan wasan ya kai masa ziyara. Hoto: Ali Nuhu Mohammed.
Source: Facebook

Malam Dokoro ya gargadi Gwamna Inuwa

Malam Dokoro ya ce dole su fito su fadawa gwamnan gaskiya saboda duk alherin da ya kafa za ta bi shi haka kuma zunubi.

Ya gargadi gwamnan ka da ya kuskura ya bata rawarsa da tsalle duba da ayyukan alheri da ya yi na rusa gidajen gala a baya.

Ya kara da cewa:

"Gara mu fada maka gaskiya ba mu son ka mutu zunubi ya bi ka, saboda haka ka kafa ayyukan alheri, mun ga yadda aka rusa gidajen gala mutane sun yi ta addu'o'i da yabo.
"Ka da ka kuskura ka zo ka bata rawarka da tsalle domin wancan abin yana binka na lada, wannan kuma zunubi ne zai bika har tashin kiyama"

Wani a Gombe ya tattauna da Legit Hausa

Muhammad Abubakar Jarma ya ce tabbas abin da malam ya fada gaskiya ne bai kamata a samu irin wannan lamari a Gombe ba.

Kara karanta wannan

Wike ya fadi abin da ƴan siyasar Ribas suka saka a gaba bayan dawowar Fubara

"Wasu masana za su ce ai za a samu ingancin tattalin arzki amma kuma matsalar da za a ta haifar sai ya yi muni fiye da yaduwar tattalin arzikin."

- Muhammad Jarma

Jarma ya ce ya kamata hukumomi su yi mai yiwuwa don ganin an dakile hakan idan har da gaske ne da nemo wasu hanyoyi.

Sheikh Dokoro ya aika sako ga Tinubu

Mun ba ku labarin cewa Sheikh Adamu Muhammad Dokoro ya fadakar da masu mulki a Najeriya duba da wahalar da ake sha.

Babban malamin na addinin musulunci ya ce mutane suna cikin wahala, ya bukaci Bola Tinubu ya tausayawa jama’a.

A jawabin da ya yi a majalisin karatunsa, Sheikh Dokoro ya ce malaman da suka tallata APC su ankarar da shugabanni.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.