Babu Karbo Bashi: Uba Sani Ya ce Gwamnatinsa za Ta Yi Ruwan Ayyukan Raya a Kaduna
- Gwamnan Kaduna Uba Sani ya bayyana cewa cwa gwamnatinsa ta shirya samar da manyan ayyukan more rayuwa a jihar
- Sai dai ya ce dukkanin manyan ayyukan da aka dauko, gwamnatinsa ba za ta karbo bashi da sunan kammala shi ba
- Ya bayyana haka a lokacin da ya ke kaddamar da ginin sabon titin Kayarda, wanda jama'ar garin su ka roka a yi masu lokacin kamfen
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta ci bashi don gudanar da ayyukan raya ƙasa ba.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kaddamar da ginin sabon titin Kayarda, wanda zai haɗa garuruwan Kayarda Tasha, Kayarda Gari, Unguwar Sarki, Maskawa da Dan Alhaji a ƙaramar hukumar Lere.

Kara karanta wannan
Ribas: Peter Obi ya zargi gwamnatin Najeriya da yi wa dimokuradiyya kisan mummuke

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta wallafa cewa Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta gaji tarin ayyuka da tsofaffin gwamnatoci suka bari ba a kammala ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Uba Sani ya kuduri aiki a Kaduna
Gwamna Uba ya bayyana cewa ana amfani da kware wa wajen gudanar da aikin titin da aka kaddamar mai tsawon kilomita 16.5.
Da yake bayyana farin cikinsa a kan aiki, Gwamna Uba Sani ya ce wannan shi ne karo na farko da irin wannan aiki zai shigo wannan yankin.

Source: Original
Ya ce:
“Mun riga mun kammala gadar Rewa da ke haɗa garin Gure. Mun kuma kammala gadar Marjeri, yayin da gadar Tudai za ta kammalu cikin wata ɗaya ko biyu. Mun ɗauki matakai na magance matsalar wutar lantarki a garuruwan Yarkasuwa, Kayarda, Ramin Kura da Mariri.”
An yaba wa Gwamnatin Uba a Kaduna
Kwamishinan Muhalli na Jihar Kaduna, Abubakar Buba, wanda ya halarci taron, ya yabawa Gwamna Uba Sani da cewa yana cika alƙawarin da ya dauka.

Kara karanta wannan
Filato: Bincike ya bankado yadda aka hallaka mutum kusan 12,000 a 'yan shekarun nan
Ya kara da cewa Uba Sani mutum ne mai gaskiya da rikon amana. Ya ce gwamnan ya ba da dama sosai ga ‘yan asalin Lere a cikin gwamnatinsa.
Buba ya bayyana cewa:
“Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kaduna, Hon. Munira Suleiman Tanimu, daga Lere take. Muna alfahari da ɗan majalisar tarayya mai ƙwazo, Hon. Ahmed Munir, da kuma Hon. Jafaaru, shugaban ƙaramar hukumar. Ni kaina ina matsayin Kwamishinan Muhalli.”
Kwamishinan ya ƙara da cewa Gwamna Uba Sani ya ba su cikakken ‘yanci wajen gudanar da ayyuka, yana mai cewa wannan ne ya sa suke gudanar da siyasa mai 'yanci.
A nata jawabin, Hon. Munira Suleiman Tanimu, ta tunatar da cewa tun lokacin kamfe ne mutanen Lere suka roƙi a gina musu wannan titi, kuma yanzu an cika masu burinsu.
Kaduna: Birtaniya ta ce an samu saukin rashin tsaro
A baya, mun wallafa cewa Gwamnatin Birtaniya ta sanar da cewa ta cire Jihar Kaduna daga jerin wuraren da ta hana 'yan kasarta ziyarta, wato jerin “Red list”, ta koma cikin “Amber list”.
Wannan na nufin yanzu an fara duba Kaduna a matsayin jiha da tsaro ya fara inganta bayan an samu gagarumar matsalar sace-sace da kashe jama'a ba tare da sun aikata laifin komai ba.

Kara karanta wannan
Naira ta rike wuta, darajarta ta karu yayin da asusun kudin wajen Najeriya ke habaka
Birtaniya ta sanar da janye janye takunkumin ne yayin da gwamnatin jihar Kaduna ta rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da ofishin gwamnatin Birtaniya da ke Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng