Katsina: Bayan Kachallah Isiya, Tantirin Dan Bindiga Ya Cika Alkawari domin Mutunta Sulhu
- Maganar sulhu da yan bindiga don zaman lafiya na ci gaba da sauya salo a wasu yankunan jihar Katsina
- An gudanar da zaman sulhu a kwanan nan a karamar hukumar Faskari da dan bindiga, Ado Aliero
- Wasu daga cikin wadanda aka yi sulhu da su sun fara sakin mutanen da ke hannunsu saboda mutunta tsarin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Da alamu zaman sulhu da aka yi a wasu yankunan jihar Katsina na haifar da ɗa mai ido yayin aka fara sakin jama'a.
Wasu yankunan jihar sun yi zama na musamman da yan bindiga domin tabbatar da samun zaman lafiya.

Source: Twitter
Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa wasu yan bindiga sun fara sakin mutanen da suka yi garkuwa da su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Katsina: Yadda dan bindiga ya fara sakin mutane
Yarjejeniyar sulhun da aka cimmawa a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina ta fara aiki bayan hobbasa daga wasu yan bindiga.
Hakan ya biyo bayan fara cika alkawura da yan bindiga suka fara yi daga bangaresu saboda zaman sulhu da aka yi.
Jagoran 'yan bindiga, Isiya Akwashi Garwa, ya mutunta batun sulhu ta hanyar sako mutanen da ya yi garkuwa da su.
Mazauna yankin sun nuna farin cikinsu kan wannan lamari, inda su ka bukaci ya yi wa sauran miyagu magana su daina kai hare-hare.

Source: Original
Wani dan bindiga ya cika ka'aida
Wani hatsabibin dan bindiga da ya tuba ya saki wasu mutane da ya kama domin a biya shi kudin fansa kafin zaman sulhu da aka yi.
Dan bindigar ya saki mata har guda uku a jihar Katsina a matsayin wani bangare na tsarin zaman lafiya wanda yanzu ake kokarin samarwa a Katsina.
Matan, wadanda ba a bayyana sunayensu ba, an ce sun kwashe lokaci a hannun Kacallah Zailani, fitacce ’dan bindiga a Maigora.
Majiyoyi daga al’umma sun shaida cewa a ranar Laraba 17 ga watan Satumbar 2025 cewa Zailani ya sake su ba tare da an biya kudin fansa ba.
“Ya mika matan ga masu sasanci a matsayin alamar kyakkyawan niyya don tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya."
- In ji wata majiya
Yadda mutane ke kallon sulhu da yan bindiga
Mutane da dama na damuwa kan sakin mutane da yan bindiga suke yi inda mafi yawa ke fargaba komai na iya faruwa saboda ba su da amana.
Duk da haka wasu bangare na ganin sulhu shi ne kawai hanyar samun zaman lafiya ciki har da malaman addini kamar Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah.
Yaran Aliero sun yanka Sarki a Zamfara
Mun ba ku labarin cewa yan bindiga da Ado Allero ke jagoranta sun kawo tsaiko yayin da ake cikin maganar sulhu da yan bindiga a Katsina.
Gungun miyagun karkashin Aliero sun kashe Hakimin Dogon Dawa a Keta, Tsafe Zamfara, tare da sace mutane 40 a masallaci.

Kara karanta wannan
Sa'o'i da sulhu, 'yan bindiga sun rufe masallaci, sun sace masu sallah 40 da Asuba
Duk da sulhun da ake yi a Faskari, hare-haren sun ci gaba da faruwa, ciki har da sace mutane 12 a Bukuyum da 4 a Tudun Moriki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

