Dangote Ya Ce ana Neman Ya Saka Tallafin Man Fetur na Naira Tiriliyan 1.5 a Najeriya
- Kungiyar DAPPMAN ta bai wa Dangote wa’adin kwana bakwai ya janye ikirarin karkatar da man fetur ko ya kawo hujja
- Dangote ya ce ‘yan kasuwa sun nemi tallafin da ya kai Naira tiriliyan 1.5 a shekara domin daidaita farashi da na matatar shi
- Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da bugawa tsakanin Dangote da masu dakon mai kan shiri fara raba fetur kyauta
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Rikicin dake tsakanin matatar Dangote da kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya (DAPPMAN) ya ƙara kamari.
Hakan na zuwa ne yayin da dukkan ɓangarorin biyu ke musayar zarge-zarge kan harkar rarraba mai.

Source: Getty Images
A wani sako da kamfanin Dangote ya wallafa a Facebook, ya bayyana cewa har yanzu yana kan bakarsa ta cewa dillalan sun nemi tallafin mai daga wajensa.

Kara karanta wannan
Filato: Bincike ya bankado yadda aka hallaka mutum kusan 12,000 a 'yan shekarun nan
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
DAPPMAN ta kalubalanci Dangote ya kawo hujja kan ikirarin da ya yi cewa wasu daga cikin mambobinta na karkatar da mai zuwa ƙasashen makwabta.
Ta ce wannan lamari na da alaƙa da tsaron ƙasa, don haka hukumomin gwamnati ne suka dace su gudanar da bincike.
Ƙungiyar DAPPMAN ta kalubanci Dangote
A wata sanarwa, kungiyar ta bai wa Dangote wa’adin kwana bakwai ya janye zargin ko kuma ya kawo hujja. Ta ce idan bai yi hakan ba, za ta kai ƙara kotu domin kare martabarta.
Kungiyar ta musanta cewa tana ɗaukar nauyin shirin yajin aikin ma’aikatan NUPENG, tana mai cewa aikinta shi ne tabbatar da cewa ba a samu cikas wajen samar da mai ba.
Haka kuma ta ce ba gaskiya ba ne cewa ‘yan kasuwa na shigo da man da aka tace daga matatar Dangote daga Togo.
Martanin Dangote ga DAPPMAN
Dangote ya bayyana cewa ‘yan kasuwa sun fi son jigilar mai ta hanyar teku daga ketare, wanda hakan ke ƙara N75 a kowace lita.
Bisa lissafin yadda ake amfani da lita miliyan 40 na fetur da miliyan 15 na dizal a kullum, Dangote ya ce hakan na nufin ƙarin kashe Naira tiriliyan 1.5 a shekara.
Daily Trust ta rahoto ya ce:
“Yan kasuwar suna son mu rage musu N70 a kowace lita don kuɗin jigilar ruwa, NIMASA, NPA da sauran kuɗin da ke tattare da hakan...
"Tare da ƙarin N5 a kowace lita don su rika sayen mai daga matatarmu zuwa wajajen ajiyarsu a Apapa. Wannan zai ba su damar sayarwa a farashi daidai da na mu.”
Matsayin Dangote kan tallafin mai
Dangote ya bayyana a sarari cewa ba zai yarda ya ɗaga farashi domin biyan waɗannan bukatu ba, kuma ba zai shiga tsarin biyan tallafin Naira tiriliyan 1.5 ba.
Ya ce tallafin mai ya taba zama hanya da ake amfani da ita wajen damfarar gwamnatin tarayya na tsawon shekaru, don haka ba zai maimaita irin wannan kuskure ba.

Source: Getty Images
An hana Dangote gina kamfani a Benue
A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya tuna baya game da gwagwarmayar da ya yi a lokacin Olusegun Obasanjo.
Dangote ya bayyana cewa ya yi kokarin kafa kamfanin simintinsa na farko a jihar Benue amma mutanen yankin suka ki.
Ya fara shirin kafa kamfanin ne a lokacin da Olusegun Obasanjo ya bukace shi da ya kawo karshen shigo da siminti daga ketare.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
