Atiku Ya Yi Nazari, Ya Gano Abin da Yake Tunanin Ya Hana Kawar da 'Yan Bindiga a Najeriya
- Atiku Abubakar ya sake sukar salon shugabancin Bola Ahmed Tinubu musamman kan batun matsalar tsaro
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce jami'an tsaron Najeriya suna da kwarewa da karfin kawar da 'yan bindiga
- Ya ce yana mamakin yadda yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a wasu sassan kasar nan, har suke iya sanya haraji da hana noma
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce jami’an tsaron ƙasar nan suna da cikakkiyar ƙwarewa da ƙarfin da za su iya kawar da ‘yan bindiga.
Sai dai Atiku ya soki Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa ya gaza samar da ingantaccen jagorancin da ake bukata domin dawo da zaman lafiya.

Source: Twitter
Tha Cable ta rahoto cewa Atiku ya fadi haka ne a ranar Talata a wata ganawa da masu ruwa da tsaki daga Jihar Borno, ƙarƙashin jagorancin tsohon dan Majalisar Wakilai, Mohammed Kumalia.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya kara suka Tinubu kan tsaro
Atiku Abubakar ya yi ikirarin cewa Shugaba Tinubu ya gaza jagorantar dakarun tsaron da Najeriya ke da su ta yadda za su murkushe 'yan bkndiga gaba daya.
“Abin farin ciki shi ne ganin cewa mutane, musamman shugabannin siyasa a faɗin ƙasar, ke ƙara nuna damuwa kan tabarbarewar halin da Najeriya take ciki har ma suna ta neman mafita,” in ji Atiku.
A halin yanzu, matsalar tsaro ta ƙara ta’azzara, inda rahotanni ke cewa ‘yan bindiga sun mamaye wasu yankuna suna tilasta wa mazauna biyan kuɗin haraji.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya dora alhakin wannan matsala kan abin da ya kira gazawar jagorancin Tinubu, in ji rahoton Daily Trust.
Me Atiku ke tunanin ya hana dawo da tsaro?
“Ina ga kowa ya fahimci cewa mamayar wasu sassan Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma, da Arewa ta Tsakiya da ‘yan ta’adda suka yi, alama ce ta rashin nagartaccen jagoranci, musamman a ƙarƙashin gwamnatin APC da Tinubu ke jagoranta."
“Ba wani abu ba ne da ya fi ƙarfin jami’an tsaron Najeriya su magance shi amma gwamnatin ba ta nuna ƙwarewar da ta dace wajen tunkarar lamarin ba.
“Idan ba mu samu shugabanci mai ƙarfin hali da zai iya fuskantar waɗannan gungun masu laifi ya murƙushe su, ba za a iya samun mafita ba.
“Ta yaya gaba ɗaya ƙaramar hukuma za ta kasance ƙarƙashin ikon ‘yan bindiga? Abin kunya ne cewa har yanzu ‘yan bindiga ko suna ci gaba da mamaye al’umma, suna kakaba haraji ga jama’a, suna kuma hana ayyukan noma.”
- Atiku Abubakar.

Source: Facebook
Atiku Abubakar ya ƙara da cewa idan aka samu jagoranci mai inganci, jami’an tsaron Najeriya na da cikakkiyar damar shawo kan matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta.
Atiku ya gana da tsofaffin shugabannin CPC
A wani labarin, kun ji cewa tsofaffin shugabannin jam’iyyar CPC da aka rusa a baya sun kai ziyara ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Jiga-jigan jam'iyyar wacce tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari ya kafa, sun gana da Atiku a gidansa da ke Abuja.
Shugabannin sun bayyana goyon bayansu ga hadakar da yake jagoranta domin kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


