Hadimin Tinubu Ya Taso Atiku a Gaba kan Ikirarin Yunwa a Najeriya

Hadimin Tinubu Ya Taso Atiku a Gaba kan Ikirarin Yunwa a Najeriya

  • Hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala ya yi martani kan maganganun da Atiku Abubakar ya yi kan matsalar yunwa a Najeriya
  • Daniel Bwala ya bayyana cewa matsalar yunwa ba a gwamnatin Mai girma Bola Tinubu ta fara ba
  • Ya bayyana cewa 'yan adawa irin su Atiku, sun sauya salon sukar da su ke yi wa gwamnati ne bayan sun gano cewa sun tafka.kuskure

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara na musamman kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala, ya yi wa Atiku Abubakar, martani kan batun matsalar yunwa da talauci.

Daniel Bwala ya ce ‘yan Najeriya suna cikin yunwa tun daga shekarar 1999 (lokacin da Atiku Abubakar ya kasance mataimakin shugaban kasa).

Daniel Bwala ya yi wa Atiku martani
Hoton Daniel Bwala da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar Hoto: @bwaladaniel, @atiku
Source: Twitter

Daniel Bwala ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar TVC.

Kara karanta wannan

2007: PDP ta bukaci Tinubu ya fara shirin mika mulki, ta kawo dalili

Atiku Abubakar ya danganta yawaitar matsalar tsaro a kasar nan kan kara taɓarɓarewar talauci da yunwa.

Wane martani hadimin Tinubu ya yi ga Atiku?

Amma a martanin da ya yi, Bwala ya yi watsi da ikirarin na Atiku, inda ya ce yunwa da wahala ba sabon abu ne a Najeriya, kuma ba gwamnatin yanzu ta kawo su ba.

Ya zargi ‘yan adawa da kokarin bata sunan gwamnatin tarayya.

Daniel Bwala ya bayyana cewa shugabannin adawa sun canza maganganu ne bayan sun tabbatar da cewa sun yi kuskure a kan manufofin tattalin arzikin Tinubu.

Ya kara da cewa yunwa babbar matsala ce da aka dade ana fama da ita a tarihin Najeriya.

"Abu mafi muhimmanci shi ne batun da (Atiku) ya yi. Shin yana da hujja? A’a, saboda bayanai sun nuna akasin haka. Me kake tsammanin za su yi face kokarin su lalata gwamnati domin su samu abin magana?"

Kara karanta wannan

ADC ta fadi gwamnan da doka ta yarje wa Tinubu ya sauke daga kujerarsa

"Ya ce mu ne muke haifar da yunwa. Shin makaho ne ko ba ya jin labarin ci gaban da muka samu? Misali, mun kara adadin kudaden ajiya na kasashen waje. Amma bai yi magana a kai ba."
"Bai yi magana kan NELFUND da muka samar ba. Ya kamata ya faɗi ko yana aiki ko bai yi ba."
“A farko sun fara da cewa tsarin tattalin arzikinmu ba daidai ba ne. Amma yanzu, bayan shekaru biyu, mun tabbatar musu akasin haka. Yanzu suna kokarin tayar da tarzoma a cikin al’umma."
“Wannan maganar cewa ‘yan Najeriya suna cikin yunwa ya kamata mu daina ta. ‘Yan Najeriya sun yi yunwa a 1960, sun yi yunwa a 1980, sun yi yunwa a 1990, sun yi yunwa a 1999. Kuma a tsakanin 1999 zuwa 2003 wani mawaki ya rera wakar ‘Najeriya Jaga Jaga’."

- Daniel Bwala

Daniel Bwala ya soki Atiku Abubakar
Hoton shugaban kasa Bola Tinubu tare da Daniel Bwala Hoto: @Bwaladaniel
Source: Twitter

Bwala ya ba 'yan Najeriya shawara

Bwala ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi hukunci bisa abin da gwamnati ke yi wajen inganta rayuwa.

“A auna mu da manufofin da muke aiwatarwa, da yadda suke aiki, ba da maganganun adawa kawai ba.”

- Daniel Bwala

Kara karanta wannan

Atiku ya yi nazari, ya gano abin da yake tunanin ya hana kawar da 'yan bindiga a Najeriya

Fadar shugaban kasa yi wa Atiku martani

A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta tanka bayan Atiju Abubakar ya bayyana cewa ta kasa magance matsalar yunwa da talauci.

Ta bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasan da magoya bayansa ba su san halin da ake ciki ba a Najeriya.

Fadar shugaban kasan ta bayyana cewa tana alfahari da nasarorin da ta samu a cikin shekara biyu da hawa kan mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng