Saudiyya Ta Sako Maniyyatan Najeriya da Aka Tsare kan Zargin Safarar Kwayoyi

Saudiyya Ta Sako Maniyyatan Najeriya da Aka Tsare kan Zargin Safarar Kwayoyi

  • Hukumomi a Saudiyya sun saki ’yan Najeriya uku da aka tsare a Jeddah tsawon makonni hudu bisa zargin safarar miyagun kwayoyi
  • Binciken NDLEA ya gano cewa wata kungiyar masu safara ce ta sanya sunayensu jakunkunan dauke da kwayoyi a filin jirgin saman Kano
  • An kama shugaban kungiyar, Mohammed Ali Abubakar (Bello Karama), tare da wasu mutum uku ciki har da ma’aikatan jirgin sama

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - 'Yan Najeriyan da aka tsare a Saudiyya bisa zargin safarar kwayoyi sun shaki iskar 'yanci.

Hukumomi a Saudiyya sun saki ’yan Najeriya uku da aka tsare tsawon makonni hudu bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.

Maniyyatan Najeriya da aka kama a Saudiyya sun samu 'yanci
Hoton kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi Hoto: @ndlea_nigeria
Source: Twitter

Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana hakan a taron manema labarai a Abuja, kamar yadda aka sanya a shafin X na hukumar.

Kara karanta wannan

Malami ya shiga rikici da gwamna, ana zarginsa da ingiza ta'addanci a jihar Kebbi

Saudiyya ta sako masu zuwa Umrah

Maniyyatan da aka saki su ne, Maryam Hussain Abdullahi, Abdullahi Bahijja Aminu da Abdulhamid Saddieq.

An kama su ne bayan sun isa birnin Jeddah a kan jirgin Ethiopian Airlines ET940 daga Kano ranar 6 ga watan Agusta, 2025, domin yin Umrah.

A cewarsa bincike ya gano cewa wata kungiyar masu safarar kwayoyi ce a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano (MAKIA) ta sanya sunayensu a jakunkunan dauke da miyagun kwayoyi ba tare da saninsu ba.

Binciken ya kai ga kama Mohammed Ali Abubakar (Bello Karama), mai shekaru 55, wanda ake zargin shine shugaban kungiyar, tare da wasu mutum uku ciki har da ma'aikatan jirgin sama.

Taimakon da gwamnati ta bada

Babafemi ya ce shugaban NDLEA, Birgediya-Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya gudanar da tattaunawa mai zurfi da hukumomin Saudiyya a matakai daban-daban, tare da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ya kara da cewa Tinubu ya dage cewa babu wani ɗan Najeriya da zai sha wahala a kasashen waje bisa laifin da bai aikata ba.

Kara karanta wannan

Karar fashewar abu ta tayar da hankula a Madina, kusa da Masallacin Annabi SAW

An saki mutum na farko ranar Lahadi, 14 ga Satumba, 2025, yayin da sauran biyun kuma aka sake su ranar Litinin, 15 ga watan Satumba, 2025

Shugaba Tinubu ya samu yabo

Saudiyya ta saki 'yan Najeriya da ta tsare kan safarar kwayoyi
Hoton kakakin hukumar NDLEA na kasa, Femi Babafemi Hoto: @ndlea_nigeria
Source: Twitter

Mai magana da yawun na NDLEA ya yabawa Shugaba Bola Tinubu bisa taimakon da ya bada wajen ganin an sake su.

"Babban tallafin da muka samu a wannan lamari ya fito daga Shugaba Tinubu, wanda yake da kishin ganin cewa duk wani ɗan Najeriya yana samun mutunci da adalci a duk inda yake."
"Wannan lamari ya tabbatar da hakan cewa ba dan Najeriyan da za a hukunta kan laifin da bai da masaniya a kai, a ko'ina cikin fadin duniya."

- Femi Babafemi

NDLEA ta kama kayan laifi a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an hukumar NDLEA sun cafke kayan laifi a jihar Kano.

Jami'an na NDLEA sun samu nasarar kama kwalaben Akuskura 8,000 da kullin tabar wiwi 43.

An gano kayan laifin ne a kan titin Zaria-Kano bayan an dakata da wata motar tirela mai dauko kaya daga Legas zuwa Maiduguri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng