Manyan Dalilai 5 da ka Iya Tunzura ASUU Ta Sake Rufe Jami'o'i a Najeriya
A baya-bayan nan Kungiyar Malaman Jami'o'in Gwamnati a Najeriya (ASUU) ta sake yin barazanar tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ƙungiyar ASUU ta daɗe tana kokawa kan rashin cika alkawurra, wanda ke haddasa sabani tsakaninta da Gwamnatin Tarayya.

Source: Twitter
A rahoton Channels tv, ASUU ta bayyana aniyarta na daukar duka matakan da suka dace don ganin cewa gwamnati ta saurare ta kuma ta yi abin da ya kamata.
ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki
Yajin aikin malaman jami'o'i na daya daga cikin abubuwan da ke kawo tsaiko a harkar ilimin Najeriya saboda yadda ASUU ke dakatar da mambobinta daga koyar da dalibai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ASUU ta bukaci 'yan Najeriya da ka da su ga laifinta a abin da zai faru, su tuhumi gwamnatin tarayya idan har ilimi ya lalace a nan gaba.
Kungiyar ta bayyana cewa har yanzu gwamnatin tarayya ta gaza cika alkawurran da ta dauka a yarjejeniyar da ta amince da ita a shekarar 2009.
Gwamnatin ta sha tattaunawa da ASUU tare da cimma matsayar yadda za a cika wannan yarjejeniya, amma daga bisani kuma a koma gidan jiya.
Dalilan da za su jawo ASUU ta rufe jami'o'i
A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro maku manyan dalilan da ka iya sanya ASUU ta koma yajin aiki a Najeirya. Ga su kamar haka:
1. Rashin cika alkawuran gwamnati
ASUU ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da dama tun daga shekarar 2009, amma har yanzu yawanci ba a aiwatar da su ba, musamman batun ƙarin kuɗi da walwalar malamai.
Kungiyar ta jima tana kokawa kan rashin cika alkawurran da ke kunshe a yarjejeniyar da ta cimma da gwamnatin Najeriya a 2009, cewar rahoton Guardian.
Gwamnatoci da dama da suka biyo baya sun yi alkawarin cika wannan yarjejeniya a lokuta daban-daban amma har yanzu babu alamar da ke nuna an biya bukatun ASUU.
Daga 2009 zuwa yau, malaman jami'o'i sun shiga yajin aiki sau sama da biyar, ciki har da wanda aka shafe watanni tara a 2020 duk saboda rashin cika alkawarin gwamnati, in ji rahoton The Cable.
2. Ƙarancin kuɗin da ake warewa jami’o’i
Ko da yake ana ta kira gwamnati da ta ƙara kuɗin da take warewa ilimi, Najeriya na ci gaba da ware kaso ƙanƙani na kasafin kuɗi ga fannin.
Kungiyar ASUU ta sha nuna damuwarta kan wannan lamarin, inda ta bayyana cewa Jami'o'in Gwamnatin Najeriya sun zama koma baya saboda rashin isassun kudin gudanarwa.
A cewar ASUU, ya kamata gwamnati ta kara yawan kudin da take ware wa jami'o'i, sannan ta inganta gine-gine da kayan aiki domin bunkasa harkokin ilimi.
Jaridar This Day ta ruwaito cewa wannan dalili na daya daga cikin abin da ya haddasa zanga-zangar da ASUU ta yi kwanan nan, ina ta bukaci gwamnati ta kara kason da ake warewa jami'o'i.
3. Batun albashi da alawus-alawus
Malaman jami'o'i na ci gaba kokawa kan walwala da jin dadinsu, wanda ya hada da albashin watanni da aka rike masu da kuma alawus-alwus, da hakkokin karin girma, in ji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan
Naira ta rike wuta, darajarta ta karu yayin da asusun kudin wajen Najeriya ke habaka
Kungiyar ta bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta rike wa malaman albashinsu na watanni saboda tsarin ba aiki ba biya da ta aiwatar lokacin yajin aiki.
ASUU na ganin cewa malaman jami'a sun cancanci albashi na musamman duba da gudummuwar da suke bayarwa, amma sai aka maida su koma-baya.
Haka zalika, alawus din mambobin ASUU da gwamnati ta rike na daga cikin abubuwan da ke fusata kungiyar, har ta shiga yajin aiki.
A zanga-zangar da mambobin ASUU suka yi a watan Agustan da ya gabata, sun bukaci gwamnati ta biya albashinsu da aka rike, hakkokin karin girma, alawus sannan ta cika yarjejeniyar 2009.

Source: Twitter
4. Ƙarin tsadar rayuwa
Tsadar rayuwa da aka shiga musamman bayan cire tallafin man fetur da wasu sababbin tsare-tsaren gwamnati, ya kara jefa malaman jami'a cikin wahalhalu.
Malaman jami’a sun bayyana cewa ba za su iya jurewa ba sai an yi dubi ga albashi da walwalarsu a wannan hali da ake ciki.
A wata sanarwa da shugaban ASUU na kasa, Farfesa Christopher Piwuna ya fitar ranar Asabar, 9 ga watan Agusta, 2025, ya ce malamai ba za su ci gaba da koyarwa a yanayin yunwa ba.
Sanarwar wacce Arise TV ta tattaro, ta bayyana cewa yanzu ASUU ta kai wuya, tana mai kira ga gwamnati da ta dauki mataki cikin gaggawa don kauce wa yajin aiki.
5. Ƙin amincewa da tsarin rance (TISSF)
Wani karin dalili da ya zo a kwanan nan shi ne shirin da gwamnatin tarayya ta bullo da shi na bai wa malaman jami'o'i lamunin kudi da nufin tallafa masu.
ASUU ta soki shirin na Tertiary Institutions Staff Support Fund (TISSF), inda ta kira shi “guba” wanda aka kirkiro don jefa malamai cikin bashi maimakon tallafa masu.
Kungiyar ta jaddada cewa abin da malamai ke bukata shi ne biyan wadataccen albashi da mutunta yarjejeniyoyi, ba ɗaura musu bashi ba, kamar yadda Punch ta rahoto.

Source: Twitter
Ma'aikatan Jami'o'i sun gindaya wa'adi
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyoyin ma’aikatan jami’o’i sun bai wa gwamnati wa’adin kwana bakwai domin ta waiwayi kalubalen da suke fuskanta kuma ta biya bukatunsu.
Kungiyoyin biyu, SSANU da NASU, sun yi barazanar cewa matukar aka share su, za su tsunduma yajin aiki a manyan makarantun da ke fadin Najeriya.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta dauki harama, nan ba da jimawa ba za a daina dauke wuta a Najeriya
SSANU da NASU sun bayyana cewa tun bayan zaman da wani kwamitin hadin gwiwa ya yi a 2024, babu wanda ya ce masu uffan har yanzu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


