'Yan Fansho Sun Fusata, Suna Shirin Fara Zanga Zanga Tsirara a Fadin Najeriya

'Yan Fansho Sun Fusata, Suna Shirin Fara Zanga Zanga Tsirara a Fadin Najeriya

Tsofaffin ma’aikatan gwamnatin tarayya sun yi barazanar gudanar da zanga-zangar tsirara a fadin kasar nan ranar 6 ga Oktoba

Sun ce har yanzu ba su samu kudaden tallafin N25,000 da karin fansho ba, duk da umarnin shugaban kasa Tinubu

Sun koka da cewa ma’aikata na samun tallafi da karin albashi, amma tsofaffin ma’aikata na cikin halin kunci da fatara.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gamayyar Kungiyoyin Tsofaffin Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta ta gudanar da zanga-zangar tsirara a fadin kasar.

Ta yi barazanar fara wannan zanga-zanga daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, saboda rashin biyan su bashin kudin da su ke bin gwamnatin tarayya.

Yan fansho sun sako gwamanti a gaba
Hoton Shugaban Kasa, Bola Tinubu yana addu'a Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa Shugaban gamayyar, Mukaila Ogunbote ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a Legas a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Malami ya shiga rikici da gwamna, ana zarginsa da ingiza ta'addanci a jihar Kebbi

'Yan Fansho a Najeriya sun fusata

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa 'yan fanshon sun bai wa gwamnatin Najeriya wa’adin zuwa karshen watan Satumba don ta biya su hakkokinsu.

Sun bayyana cewa matuka aka yi watsi da lamarinsu, babu shakka za su fito zanga-zangar domin nuna mawuyacin halin da su ke ciki.

A cewarsa, zanga-zangar za ta zama wata hanya ta fallasa gazawar gwamnati da kuma nuna irin wahalar da suke ciki.

Tsofaffin ma'aikata sun fusata
Hoton wasu ma'aikatan a karkashin NLC Hoto: Nigeria Labour Congress HQ
Source: Facebook

Shugaban gamayyar ya ce:

“Yayin da ma’aikata suka karɓi tallafin N35,000 cikin wata guda bayan amincewar shugaban kasa a watan Oktoba 2023, mu tsofaffin ma’aikata har yanzu muna jiran N25,000 ɗinmu."

'Gwamnati ta watsar da lamarinmu,' 'Yan Fansho

Shugaban ya ƙara da cewa, tun bayan tallafin farko, ma’aikata sun samu karin wasu tallafi har na watanni 10, amma tsofaffin ma’aikata sun bukaci na watanni shida kacal, amma shiru.

Ya kara bayyana cewa Shugaba Tinubu ya bada umarnin a ƙara N13,000 a kan kudin fansho, amma har yanzu ba a aiwatar da hakan ba.

Kara karanta wannan

Sulhu ya kankama, gwamna ya kawo shirin da za a tallafawa tubabbun 'yan bindiga

Ya ce:

“Da muka bincika, sai aka ce karin N32,000 da ya kamata a mana, an manta da shi a kasafin kudin 2024 da 2025. Wannan rashin adalci ne."

Fashola Oluwo, wani daga cikin tsofaffin ma’aikatan ma’aikatar yada labarai, ya bayyana cewa tsadar rayuwa ta hana su iya rayuwa yadda ya kamata.

Wata tsohuwar ma’aikaciya, Dupe Ogunniyi, ta roki uwar gidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, da ta sa baki wajen shawo kan wannan matsala.

Albashi: NLC ta taso gwamnati a gaba

A baya, mun wallafa cewa Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta sake jaddada bukatar a sake duba mafi ƙarancin albashi, tana mai cewa Naira 70,000 da aka ayyana a baya ya yi kada.

Babban sakataren rikon kwarya na NLC, Benson Upah, ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da aka yi da shi, inda ya ce lokacin duba yiwuwar yin kari ya yi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe Sarkin da suka yi garkuwa da shi, sun jefar da gawarsa a daji

Upah ya ce hauhawar farashin kaya, kuɗin haya, sufuri, abinci da wutar lantarki ya karya darajar albashin da aka amince da shi a shekarar 2024, kuma ma'aikata na ji a jikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng