'Yan Bindiga Sun Yi Kisa a Gombe, Sun Sace Mutum 2 da Matar Aure
- Bayan sace wani mutum mai matsakaicin shekaru a kauyen Galumji a jihar Gombe, an buƙaci kudin fansa kafin kashe shi
- Iyalan marigayin sun bayyana cewa sun tara kuɗin fansa ne bayan sayar da amfanin gona da dabbobinsu a kasuwar Dukku
- Rahotanni sun bayyana cewa bayan biyan kuɗin fana ne aka gano gawar shi a ƙasan gada tsakanin yankunan Dukku da Akko
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Gombe – Wasu 'yan bindiga sun kashe wani mutum da suka sace a Gombe duk da cewa an biya kuɗin fansan da suka nema.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya girgiza mazauna kauyen Galumji a ƙaramar hukumar Dukku.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ce ta wallafa labarin a daidai lokacin da ake ganin babu matsalar 'yan bindiga a Arewa maso Gabas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya ƙara tayar da hankali a tsakanin jama’a, musamman ganin cewa bayan biyan kuɗi, an ci gaba da kai farmaki a kauyen tare da yi wa wasu iyalai barazana.
Yadda aka sace Hammayidi a Gombe
Rahoton ya bayyana cewa 'yan bindigar sun yi awon gaba da Hammayidi ne tsakar dare, sama da mako uku da suka gabata.
Biyo bayan haka, iyalansa sun yi ta kai kawo kafin su tara Naira miliyan 5 da aka nema a matsayin kudin fansa.
Bayan biyan kuɗin, an gano gawarsa a ƙasan wata gada a cikin daji da ke tsakanin garuruwan Dukku da Akko. An ce an shake shi, sannan aka harbe shi kafin a jefar da shi.
Yadda aka tara kudin fansa a Gombe
Wani ɗan ’uwan marigayin ya shaida cewa sai da suka sayar da kayan gona da dabbobi a kasuwar Dukku domin su iya biyan kuɗin.
Ya ƙara da cewa masu garkuwan sun ƙirga kuɗin da kansu sannan har suka yi masa tayin bayar da N10,000 don ya hau babur ya dawo gida daga daji.
Iyalan sun kuma ce sun kashe sama da Naira 500,000 wajen bin sawun lambar wayar da masu garkuwar suka yi amfani da ita.
Hare-hare sun biyo baya a Gombe
Rahoton Trust Radio ya nuna cewa bayan kwana biyu da sace shi, wasu masu satar shanu sun shiga gidansa, inda suka sace bijimai a wajen daure dabbobi.
Bayan kwana biyar kuma, suka sake dawowa kauyen inda suka yi ƙoƙarin kama maƙwabcin Hammayidi. Duk da ya tsere, matarsa ta shiga hannunsu har yanzu kuma tana tsare.
Rahotanni sun ce a lokaci guda, an kuma yi garkuwa da wasu maza biyu daga wani kauye da ke kusa da Dukku. Bayan tattaunawa, an biya Naira miliyan 10 kafin a sake su.

Source: UGC
Ba a samu bayanin 'yan sanda ba
Yayin da ake jiran karin bayani daga jami’an tsaro, ba a samu wata sanarwa daga rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ba.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, bai amsa kira ko saƙonnin da aka tura masa ba a lokacin hada rahoton.
Haka kuma, babu wani bayani da aka wallafa a shafukan sada zumunta na rundunar a Facebook ko X game da lamarin.

Kara karanta wannan
Sa'o'i da sulhu, 'yan bindiga sun rufe masallaci, sun sace masu sallah 40 da Asuba
An shawo kan 'yan bindiga a Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta ce ta shawo kan kaso mafi tsoka na matsalar 'yan bindiga.
Kwamishinan tsaron jihar ya bayyana cewa sun yi amfani da wasu dabaru na musamman ne wajen yaki da 'yan ta'addan.
Rahoton da gwamnatin Katsina ta fitar ya nuna cewa ta ce dabarun da ta aiwatar ne suka jawo fara neman sulhun da 'yan bindiga ke yi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

