Dan Majalisar Filato da Ake Nema Ruwa a Jallo Ya Mika Kansa, ICPC Ta Tsare Shi

Dan Majalisar Filato da Ake Nema Ruwa a Jallo Ya Mika Kansa, ICPC Ta Tsare Shi

  • Dan majalisar Filato, Adamu Aliyu, ya mika kansa ga ICPC bayan an ayyana shi a matsayin wanda ake nema bisa zargin damfara
  • Ana zargin shi da yin damfara da kwangilar bogi ta TETFund a jami’ar Jos da darajarta ta kai N850m, tare da karbar miliyoyin Naira
  • Yayin da dan majalisar ya musanta zargin, ya bayyana yadda ya yi da kudaden da aka tura masa da yadda ya samu takardun bogi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Yanzu haka hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC tana kan titsiye dan majalisar jihar Filato, Adamu Aliyu a ofishinta.

An ce hukumar ICPC tana bincikar dan majalisar dokokin ne bisa zarginsa da hannu a damfara da kuma amfani da takardar kwangila ta bogi.

Dan majalisar Filato, Adamu Aliyu ya mika kansa ga hukumar ICPC kan zargin damfarar N73.6m
Hoton dan majalisar Jos ta Arewa maso Arewa, Adamu Aliyu da ya mika kansa ga ICPC. Hoto: @MichaelOyewole
Source: Twitter

Dan majalisa ya mika kansa ga ICPC

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki bayin Allah suna ibada, an rasa rayukan mutane 22 a Nijar

Adamu Aliyu, wanda ke wakiltar mazabar Jos ta Arewa maso Arewa, ya mika kansa ne a ofishin hukumar a Abuja ranar Litinin, a cewar rahoton Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya mika kansa ne kwanaki bayan da Mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya ya ayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa buƙatar ICPC.

Mun ruwaito cewa, alƙalin ya ba da umarnin ne bayan da jami'an ICPC suka shaida wa kotu cewa ɗan majalisar ya yi watsi da gayyatar da aka yi masa don amsa tambayoyi kan zargin damfara.

Zargin dan majalisa da damfarar dan kwangila

Lamarin ya samo asali ne daga koken da wani dan kasuwa mai suna Mohammed Jidda ya shigar, inda ya zargi dan majalisar da damfararsa ta hanyar amfani da wata kwangilar TETFund ta N850m a jami’ar Jos.

An zargi dan majalisar da shiga wata yarjejeniya da Mohammed Jidda, inda ɗan kasuwar zai biya kimanin N73.6m idan aka ba shi kwangilar.

Kuɗin ya haɗa da N52m da za a biya wa wani kamfani mai suna, Imanal Concept Ltd, wanda ake zargin shi ne ya sa aka ba da kwangilar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ƴan bindiga sun sace ƴar NYSC da ɗalibar jami'a, suna neman N50m

Sai dai daga baya jami’ar Jos ta tabbatar da cewa takardar kwangilar da aka gabatar ta bogi ce gaba daya.

Jami'a ta musanta ba da kwangilar N500m

Masu binciken sun ce daga baya Adamu Aliyu ya ba Mohammed Jidda wata wasiƙar ba da kwangilar bogi daga Jami'ar Jos don gina dakin motsa jiki wanda darajarsa ta kai N500m.

Bisa ga wasiƙar, Mohammed Jidda ya tura kuɗin da aka amince a cikin asusun banki guda biyu da ɗan majalisar ya bayar: asusun ɗan majalisar na kansa a Guaranty Trust Bank da wani na Imanal Concept Ltd a Zenith Bank.

Amma lokacin da Mohammed Jidda ya tuntubi Jami'ar Jos don fara shirye-shiryen kwangilar, makarantar ta musanta cewa ta ba da irin wannan kwangila.

Daga baya makarantar ta tabbatar wa hukumar ICPC a rubuce cewa wasikar kwangilar ta bogi ce dan majalisar ya bayar.

Bayanan banki da hukumar ta samu sun nuna cewa an tura N47.8m a asusun dan majalisar, sai N22.4m da aka tura asusun Imanal Concept Ltd, yayin da aka tura ƙarin N3.2m kai tsaye ga ɗan majalisar.

Kara karanta wannan

Wutar lantarki ta samu matsala, mutane za su shiga duhu a jihohi 4 a Najeriya

Hukumar ICPC ce ta bukaci kotu ta ayyana dan majalisar Jos ruwa a jallo bayan yaki amsa gayyatarta.
Hedikwatar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC da ke birnin tarayya Abuja. Hoto: @icpcnigeria
Source: Facebook

Kin amsa gayyata da nemansa ruwa a jallo

ICPC ta sha kiran Aliyu don amsa tambayoyi, har ma ta aika sakonni ta hannun sakataren majalisar Filato da WhatsApp dinsa, amma ya ki bayyana gabanta.

Hukumar ta shaida wa kotu cewa tana da bayanan sirri cewa dan majalisar na shirin tserewa ya bar Najeriya don gujewa shari’a.

Saboda haka, mai shari’a Emeka Nwite ya ba da umarnin a ayyana shi wanda ake nema ruwa a jallo kafin daga bisani ya mika kansa.

Martanin dan majalisa kan zargin damfara

Da yake kare kansa, Aliyu ya ce bai aikata damfara ba, yana mai cewa ya riga ya mayar da N45m ga kamfanin Mohiba Investment Ltd na Mohammed Jidda.

Ya kuma zargi wani abokin hulda da shirya takardar bogi, yana mai cewa shi dai kawai ya mika ta ga dan kasuwar.

A halin yanzu, dan majalisar na Jos ta Arewa maso Arewa, na ci gaba da fuskantar tambayoyi daga jami’an hukumar ICPC.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan ɗan sa kai ya buɗe wuta a masallaci, an samu raunuka

Tinubu ya nada Adamu Aliyu shugaban ICPC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya nada Dakta Adamu Aliyu a matsayin sabon shugaban hukumar ICPC.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan ya nada Ola Olukoyede a matsayin shugaban Hukumar EFCC, kamar yadda sanarwar gwamnati ta nuna.

Gwamnatin ta yi bayani cewa Dakta Musa Aliyu ya kammala digiri dinsa na farko da na biyu, sannan kuma ya na da digirin digir-gir a bangaren shari'a.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com