Jerin Gwamnonin Najeriya da Suka Kori Ma’aikata a Satumba da Dalilan da Suka Bayar

Jerin Gwamnonin Najeriya da Suka Kori Ma’aikata a Satumba da Dalilan da Suka Bayar

  • Gwamnonin Najeriya sun fara ɗaukar matakai masu tsarui kan ma’aikatan gwamnati da suka karya ka’idojin aikin gwamnati
  • A cikin makonni biyu na farkon watan Satumba 2025, akalla gwamnoni uku daga Arewa da Kudu suka kori ma’aikata a jihohinsu
  • Daga cikin rahotannin da suka bayyana, an kori ɗaya daga cikin ma’aikatan bisa zargin cin zarafin dalibai ta fuskar latata da su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Wasu gwamnoni uku sun dauki matakai masu tsauri kan ma’aikatan gwamnati da suka karya doka ko kuma suka aikata ayyuka na rashawa.

An gano cewa gwamnonin uku sun yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya basu don hukunta ma’aikatan gwamnatin a cikin watan Satumba, 2025.

Gwamnoni 3 sun kori ma'aikatan gwamnati a watan Satumba.
Gwamna Alex Otti na jihar Abia (hagu), Gwamna Lucky Aiyeditawa na jihar Ondo (tsakiya) da Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi (dama). Hoto: @alexottiofr, @LuckyAiyedatiwa, @SenBalaMohammed
Source: Twitter

Kodayake, ba gwamnonin da kansu ne suka yi korar ba, amma an ce sun yi hakan ne ta hanyar amfani da hukumomin kula da ma'aikatan gwamnati a jihohinsu, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi kisa a Gombe, sun sace mutum 2 da matar aure

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ƙasa akwai jerin gwamnonin da suka kori ma'aikatan gwamnati, da dalilan da suka bayar:

Abia: Gwamna Otti ya kori ma’aikata 6

A jihar Abia, Gwamna Alex Otti ya amince da korar manyan jami’an gwamnati guda shida daga ma’aikatar shari’a ta jihar a ranar Talata, 9 ga Satumba.

Mun ruwaito cewa, an kama jami’an da laifin sauya tsarin albashi da kuma karbar albashin da ya zarce wanda ya dace a tura masu.

Shugaban hukumar kula da ma’aikata ta jihar, Eno Eze, ya tabbatar da haka, inda ya ce an gudanar da binciken kudi mai zurfi kafin daukar matakin.

Bauchi: Gwamna Bala ya kori malami

A Bauchi, gwamnatin Bala Mohammed ta sanar da korar wani malami mai suna Emos Joshua daga aikin gwamnati saboda zargin cin zarafi.

Joshua wanda shi ne babban jami’in ilimi a kwalejin gwamnati da ke Azare, ya fuskanci tuhumar lalata da dalibai, da ta kai ga korarsa, kamar yadda muka ruwaito.

Kara karanta wannan

Sulhu ya kankama, gwamna ya kawo shirin da za a tallafawa tubabbun 'yan bindiga

Mai magana da yawun hukumar kula da ma’aikata ta jihar, Saleh Umar, ya bayyana wannan a wata sanarwa ranar Alhamis, 11 ga Satumba.

Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya dakatar da manyan jami'ai uku bisa zargin hannu a badakalar daukar malamai.
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa yana daga tutar jam'iyyar APC a lokacin yakin neman zabensa a 2024. Hoto: @LuckyAiyedatiwa
Source: Twitter

Ondo: Aiyedatiwa ya dakatar da ma'aikata

A jihar Ondo, Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya dakatar da manyan jami’ai uku – daraktoci biyu da mataimakin darakta daya – bisa zargin hannu cikin badakalar daukar malamai.

An ce jami’an na fuskantar bincike yayin da ake ci gaba da tantance sahihancin zargin da ake yi masu na damfarar masu neman aiki, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Aiyedatiwa ya kafa kwamiti na musamman domin gudanar da bincike kan lamarin, tare da umartar SUBEB ta gayyaci wadanda aka damfara domin tattaunawa da su.

Gwamna Nasir ya dakatar da kwamishina

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Kebbi ta sanar da dakatar da kwamishinan lafiya, Yunusa Ismail, bisa umarnin Gwamna Nasir Idris.

Gwamna Nasir Idris ya ba da umarnin dakatar da dan majalisar zartarwar ne bisa zarginsa da sakaci da rashin aiwatar da ayyukan da aka dora masa.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Bayan likitoci, kungiyoyin ma'aikatan jami'a za su ja zare da gwamnatin Tinubu

Gwamnatin jihar ta kuma umarci kwamishinan da aka dakatar da ya ba da hujja mai karfi da za ta hana daukar karin matakan ladabtarwa a kansa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com