'Dabarar da aka Yi Katsina Ta Kawo Karshen 'Yan Bindiga da Kashi 70,' Gwamnati
- Gwamnatin Katsina ta ce hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da kuma satar shanun mutane sun ragu da kashi 70 a jihar
- Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Dr Nasir Mu’azu, ya bayyana hakan a wani babban taron tattaunawa kan tsaro
- Ya ce sabuwar dabarar tsaro ta haɗa da sa ido na al’umma da kuma hare-hare kan sansanonin ‘yan bindiga ne ta jawo raguwar ta'addanci
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kastina - Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da cewa ta samu gagarumar nasara a yaki da ta’addanci na ‘yan bindiga da kuma garkuwa da mutane.
Wannan na zuwa ne bayan wani rahoton da aka gabatar a gaban al’ummar jihar inda aka bayyana cewa matsalar ta ragu da kusan kashi 70.

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan Katsina, Ibrahim Kaulaha Muhammad ne ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a Facebook.
Rahoton ya nuna cewa wannan ci gaba ya samo asali ne daga sabuwar dabarar tsaro da gwamnatin jihar ta kaddamar tare da hadin kan hukumomin tsaro da al’umma.
Dabarar tsaro da aka dauka a Kastina
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Dakta Nasir Mu’azu, ya bayyana cewa an kaddamar da tsarin sa ido na al’umma tare da kai hare-hare lokaci zuwa lokaci a sansanonin ‘yan bindiga.
Ya ce wannan mataki ya tilasta wa manyan shugabannin ‘yan bindiga su nemi sulhu ta hannun shugabannin al’umma.
Daga cikin wadanda suka nuna sha’awar ajiye makamai akwai Audu Lankai daga Jibia, Abu Radde daga Batsari, da Ruga Kachalla daga Safana.
An rusa sansanin ‘yan bindigan Katsina
The Guardina ta wallafa cewa rahoton ya bayyana cewa an kubutar da sama da mutane 143 da aka yi garkuwa da daga wurare daban-daban a jihar.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kashe Sarkin da suka yi garkuwa da shi, sun jefar da gawarsa a daji
Ya ce an ceto mutum 67 daga Sayaya a Matazu, yayin da aka kubutar da mutum 76 daga Gidan Mantau a Malumfashi.
Haka kuma an rusa sansanonin ‘yan bindiga da dama wanda hakan ya tilasta musu komawa dazukan Zamfara da Kaduna.
An buɗe wasu hanyoyi a jihar Katsina
Saboda ingantuwar tsaro, gwamnatin jihar ta sake buɗe wasu manyan hanyoyi da a baya aka hana zirga-zirga a kansu.
Hanyoyin sun hada da Katsina-Jibia, Katsina-Batsari, Yantumaki-Danmusa da kuma Dutsinma-Mararrabar Kankara.

Source: Facebook
Al’umma sun kafa kwamiti na musamman da ke gudanar da tarurruka na yau da kullum da kuma bita na wata-wata domin tabbatar da dorewar zaman lafiya.
Gwamnati ta ce rahoton tsaron wani bangare ne na shirin Gwamna Dikko Radda na sanar da ‘ya’yan jihar Katsina halin da ake ciki a fannin tsaro.
Ado Aliero ya yarda da sulhu a Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa kasurgumin dan bindiga da ake nema ido rufe, Ado Aliero ya amince da zaman lafiya a Katsina.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Ado Aliero ya bayyana kansa ne a wani taro da aka yi domin kawo zaman lafiya a Faskari.
Dan ta'addan ya bayyana cewa yana fatan zaman da aka yi ya kawo zaman lafiya da karshen zubar da jini a fadin Najeriya.
Asali: Legit.ng

