Zamfara: Yan Sanda Sun Faɗi Gaskiya kan Sace Liman da Masallata, Sun Faɗi Yawan Mutanen

Zamfara: Yan Sanda Sun Faɗi Gaskiya kan Sace Liman da Masallata, Sun Faɗi Yawan Mutanen

  • Rundunar ƴan sandan Zamfara ta yi karin haske kan jita-jitar sace wasu masallata a wani hari da aka kai
  • Sai dai rundunar ta tabbatar da sace mutane takwas ne yayin sallar asuba a Gidan Turbe a karamar hukumar Tsafe
  • Kakakin rundunar yan sanda a jihar, Yazid Abubakar shi ya yi wannan bayani a cikin wata sanarwa da ya fitar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta fayyace gaskiya kan rahoton sace masallata a jihar.

Rundunar ta tabbatar da sace mutane takwas yayin sallar asuba a Gidan Turbe, karamar hukumar Tsafe, a ranar Litinin.

Yan sanda sun yi ƙarin haske kan sace masu sallah a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Yan sanda sun magantu kan sace masallata

Da yake mayar da martani a sanarwa ranar Talata, kakakin rundunar, Yazid Abubakar, ya karyata alkaluman, inda ya tabbatar mutum takwas ne kawai, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Mutane sun mutu da wani karamin jirgin sama ya gamu da hatsari, an samu bayanai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda aka sace sun haɗa da Liman Yahaya, Dan Garfi, Malam Damu, Bello Natsuhuwa, Yakubu Isa, Audu Minista, Yaquba Ado, da Sabi Usman.

Wannan na zuwa ne bayan wani rahoton yanar gizo ya yi ikirarin cewa mutane 40 aka sace yayin harin da aka kai masallacin.

Ƴan sanda sun bayyana cewa:

“Hankalin rundunar ya kai kan rahoton cewa an sace mutum 40 yayin sallar asuba a ranar 15 ga Satumba.”
“Akasin rahoton, lamarin ya faru da karfe 05:07 lokacin da wasu da ake zargin ƴan bindiga suka shiga Gidan Turbe suka sace mutum takwas.”

Abubakar ya ƙara da cewa ƴan sanda na aiki kafada da kafada da sauran jami’an tsaro da shugabannin al’umma don ganin an sako waɗanda aka dauka.

“Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara tana aiki tare da hukumomin tsaro da shugabannin al’umma don dawo da waɗanda aka sace lafiya.
“Muna kira ga jama’a da kafafen yada labarai da su tabbatar da sahihancin bayanai kafin yada su domin kauce wa tayar da hankula."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe Sarkin da suka yi garkuwa da shi, sun jefar da gawarsa a daji

- Cewar sanarwar

Yan sanda sun ƙaryata sace masallata 40 a Zamfara
Gwamna Dauda Lawal da Kwamishinan yan sanda a Zamfara, Ibrahim Balarabe Maikaba Hoto: Dauda Lawal.
Source: Facebook

Alwashin da yan sanda suka yi

Rundunar ta sha alwashn ci gaba da tabbatar da kokarin kare al'umma da dukiyoyinsu da yakar dukan wasu laifuffuka.

Ya kuma ƙara da cewa:

“Runduna za ta ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyi tare da yakar duk wani nau’in laifuka a fadin jihar.”

Ƴan sanda sun roƙi jama’a da su kwantar da hankali tare da kai rahoton duk wani motsi ko aiki da suka zarga ga ofishin ƴan sanda mafi kusa.

Wannan garkuwa da mutane na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara samun hare-hare kan wuraren ibada a Arewacin Najeriya cikin watannin baya.

An kama matar shedanin dan bindiga

Kun ji cewa sojojin 1 Brigade sun samun gagarumar nasara musamman game da yaki da yan bindiga a jihar Zamfara.

Rundunar ta kama wata mata mai suna Fatima Isah Ile a Kanoma, bisa zargin taimakawa ‘yan ta’adda wajen ayyukansu.

Kara karanta wannan

Watanni bayan ya rasu, an gano gidan da tsohon gwamna a Najeriya ya mallaka a Landan

An ce ta ɓoye a wani gini da ba a kammala ba, tana amfani da yara wajen sayen man fetur, an gano mugayen makamai tare da ita.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.