Musulunci Ya Yi Rashi: Daraktan Agaji na Kungiyar Izala, Alhaji Abdullahi Ya Rasu

Musulunci Ya Yi Rashi: Daraktan Agaji na Kungiyar Izala, Alhaji Abdullahi Ya Rasu

  • Kungiyar Izala ta ƙasa (JIBWIS) ta shiga dimuwa bisa rasuwar daraktan sashen agajinta na jihar Katsina, Alhaji Abdullahi I.N. Bakori
  • Shugaban kungiyar Izala, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, ya bayyana mutuwar a matsayin wani babban rashi ga daukacin kungiyar
  • Wasu mambobin kungiyar sun nuna alhininsu a shafukan sada zumunta, inda aka bayyana marigayin a matsayin mutum mai gaskiya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Kungiyar Izalatul Bid’a Wa Iqamatul Sunnah (JIBWIS) ta Najeriya ta bayyana alhinin ta bisa rasuwar daraktan agaji na jihar Katsina, Alhaji Abdullahi I.N. Bakori.

Kungiyar JIBWIS ta rahoto cewa Alhaji Abdullahi ya riga mu gidan gaskiya bayan doguwar jinya a ranar Laraba, 17 ga Satumba, 2025.

Kungiyar Izala ta shiga jimamin rasuwar daraktan agaji na kungiyar a jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Bakori.
Hoton daraktan agaji na Izala, a jihar Katsina, Alhaji Abdullahi da ya rasu, da shugaban Izala, Sheikh Bala Lau. Hoto: Jibwis Nigeria
Source: Facebook

Daraktan agaji na Izala ya rasu

A cikin sanarwar da aka wallafa a shafin Facebook na ƙungiyar, shugaban Izala na ƙasa, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, ya jajanta wa iyalan marigayin, majalisar agaji ta ƙasa da ta jihar Katsina, da kuma dukkan mabiyan kungiyar.

Kara karanta wannan

Duniyar Musulunci ta yi rashi: Babban malamin addini ya kwanta dama

Sheikh Bala Lau ya bayyana marigayin a matsayin mutum nagari, mai gaskiya, riƙon amana da dattako, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa addini da al’umma.

“Tabbas mun yi babban rashi da za mu daɗe ba mu manta da shi ba. Yana daga cikin shugabannin da suka yi fice wajen kyautata mu’amala da ayyukan addini.
"Muna roƙon Allah ya gafarta masa, ya kyautata makwancinsa, ya haɗa mu da shi a Jannatul Firdausi."

- Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau

Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin ya bar mata, yara da jikoki da dama, kuma al’ummar Katsina sun bayyana shi a matsayin abin koyi da za a daɗe ana tunawa da shi.

Addu’o’in jama’a ga daraktan agajin Izala

Bayan sanarwar rasuwar, dimbin mabiya da abokan arziki sun cika shafin Facebook na kungiyar Izala da sakonnin ta’aziyya.

Shehu A.A Gashua: “Allah ya gafarta masa.”

Hamisu Atiku: “Allah ya jikansa da rahama.”

Kara karanta wannan

Malami ya shiga rikici da gwamna, ana zarginsa da ingiza ta'addanci a jihar Kebbi

Anas Yahaya Abdullahi: “Allah ya yi masa rahama, Allah ya sa Aljannatul Firdausi ce makomarsa.”

Usman Yakubu: “Allah ya jikansa da rahama, yasa Aljanna ce makomarsa.”

Sauran masu amfani da kafafen sada zumunta ma sun bayyana addu’o’i iri-iri na jinƙai, inda suka nuna cewa marigayin ya yi rayuwa mai cike da hidima da kyautatawa.

An ce 'yan agaji suna da muhimmanci a gudanarwar kungiyar Izala, musamman wajen ba da tsaro da shirya tarurruka.
Wasu 'yan agaji suna tsara yadda za su gudanar da ayyukansu a taron Izala. Hoto: Jibwis Nigeria
Source: Facebook

Ayyukan 'dan agaji a kungiyar Izala

Ɗan agaji muhimmin matsayi ne a Izala, musamman wajen hidima ga addini da ba da tsaro, ga wasu ayyukan dan agaji a Izala:

  • Tsaro: Suna kula da tsaro a wuraren wa’azi da tarurruka.
  • Taimako: Suna tallafa wa mata, tsofaffi da yara a wuraren taro.
  • Ayyukan jiki: Suna gudanar da aikin tsabtace wurare, shirya kayan aiki da taimakon gaggawa.
  • Tarbiyya: Ana horar da su kan biyayya, da’a da sadaukarwa, wanda ke zama hanya ta tarbiyyantar da matasa cikin kungiyar.

Wannan ne ya sa marigayi, daraktan agaji na Katsina, Alhaji Abdullahi I.N. Bakori, ya kasance ginshiƙi a tafiyar kungiyar, inda ayyukansa za su ci gaba da zama abin koyi ga mabiyansa da matasan 'yan agaji.

Kara karanta wannan

Najeriya ta rasa babban malamin Musulunci, shugaban limaman Ondo ya rasu

Shugaban limaman Ondo ya rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, babban limamin Owo, Sheikh Ahmad Olagoke Aladesawe, ya rasu yana da shekaru 91.

Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayin, al'ummar Musulmi da daukacin jihar.

An shirya jana'izarsa a ranar Talata, 16 ga Satumba, 2025, a Owo, kamar yadda sanarwa ta bayyana, bayan rasuwar limamin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com