Ana Hasashen Ruwan Sama Zai Sauka a Kaduna, Kebbi, Neja da Jihohi 26 Gobe Laraba

Ana Hasashen Ruwan Sama Zai Sauka a Kaduna, Kebbi, Neja da Jihohi 26 Gobe Laraba

  • NiMet ta fitar da hasashen yanayi na ranar Laraba, 17 ga Satumba, 2025, inda ake sa ran ruwan sama zai sauka a jihohin Arewa 13
  • Ana sa ran za a yi tsawa da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a sassan jihohin Kebbi, Sokoto, Adamawa, da Taraba da sauransu
  • Hukumar ta shawarci mazauna yankunan bakin kogi, da su zauna cikin shiri, domin za a iya samun albaliya saboda cikar koguna

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta NiMet, ta fitar da hasashen ruwan sama da zai sauka a sassan Najeriya a ranar Laraba, 17 ga Satumba, 2025.

Hasashen ya nuna cewa za a fuskanci tsawa da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a yankunan Arewa da Kudancin ƙasar.

Kara karanta wannan

Hasashen yanayi na Litinin: Za a samu ambaliyar ruwa a Taraba da jihohin Arewa 2

Ana sa ran ruwan sama zai sauka a jihohin Arewa 13 a ranar Laraba, 17 ga Satumba, 2025.
Ruwan sama da iska mai karfi na sauka a wata anguwa. Hoto: Sani Hamza / Staff
Source: Original

A sanarwar da ta fitar a shafinta na X, NiMet ta shawarci mazauna yankunan ambaliya za ta iya shafa, su kasance a shirye don kare rayuka da dukiyoyinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ruwan sama zai sauka a Arewa

A safiyar ranar Laraba, ana sa ran za a yi tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a wasu sassan jihohin Kaduna, Kebbi, Sokoto, Adamawa, da Taraba.

Da yamma kuma, ana sa ran za a ci gaba da tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a wasu sassan Borno, Yobe, Kaduna, Jigawa, Adamawa, Taraba, Kano, Katsina, Bauchi, Gombe, da Kebbi.

A Arewa ta Tsakiya, NiMet ta ce hadari ne zai hadu, amma rana za ta fito, inda kuma za a iya samun ruwan sama kadan a wasu sassan jihar Neja.

Da yamma kuma, ana sa ran za a yi tsawa mai ɗauke da ruwan sama a yawancin sassan yankin.

Kara karanta wannan

'Za a sheƙa ruwa na kwana 5,' An faɗi jihohin Arewa 10 da za su gamu da ambaliya

Hasashen ruwan sama a Kudu

A safiyar ranar Laraba, ana sa ran sararin samaniya za ta cika da hadari sosai, amma kuma akwai yiwuwar rana ta fito daga baya.

Amma da yamma zuwa dare, ana sa ran za a yi tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a wasu sassan jihohin Ebonyi, Anambra, Imo, Ogun, Ondo, Edo, Oyo, Legas, Bayelsa, Delta, Rivers, Akwa Ibom, da Cross River.

Hukumar NiMet ta shawarci mazauna bakin kogi su yi taka tsan tsan da ambaliyar ruwa.
Shugaban hukumar NiMet, Prof. Charles Anosike tare da wasu jami'ai suna duba na'urar hasashen yanayi. Hoto: @nimetnigeria
Source: Twitter

Shawara da gargadi daga NiMet

A cikin hasashen, hukumar ta bayar da shawarwari masu muhimmanci ga al'umma:

  • Tsawa da ruwan sama na iya haifar da tsaiko na ɗan lokaci ga ayyukan yau da kullum a cikin garuruwa.
  • Direbobi da su yi taka-tsan-tsan idan suna tuki a ruwan sama, saboda ganinsu zai ragu, kuma hanyoyi za su yi santsi.
  • Mazauna yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa su ɗauki matakan kariya tun da wuri.
  • Haka kuma, a guji neman mafaka a ƙarƙashin bishiyoyi a lokacin iska mai karfi saboda haɗarin faɗuwar rassa.
  • Kamfanonin jiragen sama su nemi cikakken bayani game da yanayi daga NiMet domin shirya zirga-zirgar jiragensu cikin aminci.

Kara karanta wannan

Ranar Lahadi: Za a sheka ruwan sama a Kebbi, Sokoto, Zamfara da jihohin Arewa 12

Za a sheka ruwa na kwana 5 a jere

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ma'aikatar muhalli ta tarayya ta yi hasashen afkuwar ambaliya a yankuna 32 na jihohi 11 a Najeriya.

Gwamnatin tarayyar ta ce za a sheka ruwan sama na tsawon kwanaki biyar, wanda zai iya sa kogin Gongola, Benue da Niger su yi ambaliyar ruwa.

A bana kadai, ambaliyar ruwa ta kashe fiye da mutane 231, yayin da sama da ta shafi fiye da mutum miliyan 5 a sassa daban-daban.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com