Tirkashi: Sowore Ya Tattaro Lauyoyi, Zai Yi Shari'a da DSS, Facebook da X a Kotu

Tirkashi: Sowore Ya Tattaro Lauyoyi, Zai Yi Shari'a da DSS, Facebook da X a Kotu

  • Dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore, ya maka DSS, Meta da X Corp a kotun Abuja kan zargin takke hakkokinsa na dan Adam
  • Sowore na zargin DSS da take 'yancinsa na fadar albarkacin baki, bayan ta nemi ya goge kalaman da ya yi kan Shugaba Bola Tinubu
  • Lauyansa ya ce Sashe na 39 na kundin tsarin mulki ya ba 'yan Najeriya ‘yancin fadar albarkacin baki ba tare da tsangwama ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Dan gwagwarmaya kuma ɗan siyasa, Omoyele Sowore, ya shigar da kararraki biyu na tauye hakkin ɗan adam a Babbar Kotun Tarayya, Abuja, inda yake karar DSS, Meta (Facebook), da X Corp.

Omoyele Sowore ya shigar da ƙararrakin guda biyu ne, yana ƙalubalantar abin da ya kira zunzurutun tauye hakkinsa da gwamnatin Najeriya ta yi.

Kara karanta wannan

Lamari ya girma: Gwamnatin Tinubu ta shiga rigima da X, Facebook kan Sowore

Omoyele Sowore, ya shigar da ƙararrakin ƙwace hakkin ɗan Adam guda biyu a Kotun Tarayya da ke Abuja
Omoyele Sowore tare da tawagar lauyoyinsa, bisa jagorancin Tope Temokun, a Abuja. Hoto: @YeleSowore
Source: Twitter

Sowore ya maka DSS, Meta, X a kotu

Sowore ya buƙaci kotun da ta hana Facebook da X goge kalamansa da ke cewa Shugaba Bola Tinubu ɗan ta'adda ne, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar tawagar lauyoyinsa tara, bisa jagorancin Tope Temokun, Sowore ya ce ya shigar da ƙararrakin ne domin ya nuna muhimmancin ‘yancin faɗin albarkacin baki a Najeriya.

A cewar Temokun, kundin tsarin mulkin Najeriya ne ya ba 'yan kasa ‘yancin faɗar albarkacin baki, kuma babu wata hukuma ta tsaro da za ta iya hana wa mutum waɗannan haƙƙoƙin.

Sowore ya kuma buƙaci Meta da X da kada su bi umarnin gwamnatin Najeriya na yin kutse, yana mai nacewa cewa yin hakan zai sa su zama mataimaka wajen danne ‘yancin mutane.

Ya kuma roƙi kotun da ta bayyana cewa DSS ba ta da hurumin yi wa ‘yan Najeriya kutse a kafafen sada zumunta, kuma ba dole ba ne Meta da X su zama kafofin danne yanci.

Kara karanta wannan

Tinubu, Fubara sun dawo Najeriya ana shirin dawo da gwamnan Ribas kujerarsa

Baayanin da Sowore ya yi wa kotu

A cikin takardar ƙarar, lauyan ya ce:

"A madadin abokin huldarmu, Omoyele Sowore, mun shigar da ƙararrakin danne haƙƙin ɗan Adam guda biyu a Kotun Tarayya da ke Abuja, a kan Hukumar Tsaro ta SSS, Meta (masu Facebook), da X Corp. (tsohuwar Twitter).
"An shigar da waɗannan ƙararrakin ne don ƙalubalantar takunkumin da hukumar SSS/DSS ta sanya wa shafukan Sowore da yake da su a Meta da X.
"Ƙarar ta bayyana cewa wannan lamari ne da ya shafi rayuwar ‘yancin faɗar albarkacin baki a Najeriya. Idan hukumomin gwamnati za su iya umurtan kafofin sadarwa na duniya kan wanda zai yi mu'amala da su da abin da za a faɗa, to babu wani ɗan Najeriya da zai kasance cikin aminci, za a danne muryarsu a duk lokacin da masu mulki suke so.
"Danne sukar siyasa sabon abu ne ga dimokuraɗiyya. Kundin tsarin mulkin Najeriya, a sashe na 39, ya ba kowane ɗan ƙasa haƙƙin ‘yancin faɗar albarkacin baki, ba tare da tsangwama ba. Babu wata hukumar tsaro, ko da kuwa tana da iko, da za ta iya tauye waɗannan haƙƙoƙin.”

Kara karanta wannan

2027: Ana rade radin komawarsa PDP, Peter Obi ya yi ganawar sirri da Obasanjo

Sowore ya roki ta ayyana cewa DSS ba ta da hurumin takaitawa, ko tilasta Facebook, X su goge rubutun da ya yi a shafukansu.
Hoton Omoyele Sowore da wani jami'in hukumar DSS a bakin aiki. Hoto: @YeleSowore, @OfficialDSSNG
Source: Twitter

Bukatar da Sowore ya gabatar wa kotu

A cikin takardar karar, lauyan Sowore sun roƙi kotun da ta:

"Bayyana cewa DSS ba ta da hurumin yin kutse wa 'yan Najeriya a kafafen sada zumunta;
"Bayyana cewa laifi ne Meta da X su yi amfani da shafukansu a matsayin kafofin danne 'yanci;
"Kuma a kare haƙƙin abokin huldarmu da kuma haƙƙin dukkan ‘yan Najeriya gaba ɗaya daga kutse ba bisa ƙa'ida ba."

Sowore ya yi kira ga dukkan masu son kare 'yancin 'yan kasa, 'yan jarida, masu kare haƙƙin ɗan Adam, da kuma al'ummar Najeriya da su tsaya tsayin daka tare da shi a wannan shari'a.

Gwamnati ta maka Sowore, X, Meta a kotu

A wani labarin na daban, mun ruwaito cewa, gwamnatin Najeriya ta fusata game da rashin ɗaukar mataki kan kan gwagwarmaya, Omoleye Sowore.

Gwamnatin ta gurfanar da Omoyele Sowore tare da Facebook da X bisa zargin laifukan yanar gizo saboda sakonnin da ya kira Tinubu ɗan daba.

Kara karanta wannan

Maryam Shetty ta shirya gasar Alkur'ani, ta ba da kyautar sama da Naira miliyan 1.75

Sowore ya bayyana cewa DSS ta ƙirƙiro tuhuma inda ta ce kalamansa sun saba dokokin ƙasar amma ya ƙi goge sakonninsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com