Gwamnatin Tinubu Ta Yi Albishir ga Yan Najeriya kan Zubewar Farashin Abinci

Gwamnatin Tinubu Ta Yi Albishir ga Yan Najeriya kan Zubewar Farashin Abinci

  • Fadar shugaban kasa ta yi magana kan farashin kayan abinci inda ta yi wa yan Najeriya albishir game da lamarin
  • Fadar ta ce hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya na dab da sauka zuwa kasa sosai inda ta ba da tabbacin samun sauki
  • Hadimin shugaban kasa ya ce rahoton Hukumar Kididdiga ta Ƙasa ya nuna hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 20.12% daga 21.88%

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Fadar shugaban kasa a Najeriya ta yi albishir ga yan Najeriya yayin da ake zancen faduwar farashin abinci a fadin kasar.

Gwamnatin ta ba da tabbacin cewa farashin kayan abinci yana dab da sauka kasa zuwa lamba daya yayin kwatanta faduwar farashin.

Gwamnatin tarayya ta yi albishir kan farashin abinci
Shugaba Bola Tinubu a ofishinsa a Abuja da ma'ajiyar abinci. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: UGC

Gwamnati ta yi albishir kan farashin abinci

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tattalin arziki, Tope Fasua shi ya tabbatar da haka yayin hira da Channels TV.

Kara karanta wannan

Noma: Mutane miliyan 21 za su samu ayyuka a shirin da gwamnati ta kawo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fasua ya ce 'yan Najeriya za su ga hauhawar farashin kaya ya koma lamba guda nan gaba kadan kuma za su yi farin ciki.

Ya bayyana cewa farashin kayan abinci sun fara raguwa yayin da hauhawar farashin kaya ke sassautawa a sassan kasuwa daban-daban a ƙasar nan.

Sanarwar hukumar NBS kan saukar farashin kaya

Sanarwar ta fito ne jim kaɗan bayan rahoton Hukumar Kididdiga ta Ƙasa ya ce hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 20.12 a watan Agusta.

A cewar NBS, wannan ya nuna raguwar kashi 1.76 idan aka kwatanta da watan Yuli, inda aka samu hauhawar farashi kashi 21.88.

Hukumar ta ce, a wata-wata, hauhawar farashi ya tsaya kan kashi 0.74 a watan Agusta, yayin da hauhawar abinci ya kasance kashi 1.65.

Gwamnatin Tinubu ta fadi farin ciki da zai faru game da farashin abinci
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Hadimin Tinubu ya dura kan Atiku

Hadimin Tinubu ya mayar da martani kan kalaman Atiku Abubakar da ya ce ’yan Najeriya na mutuwa da yunwa,' inda ya ce magana ta siyasa ce kawai.

Kara karanta wannan

An kara samun sauki da farashin abinci da wasu kayayyaki ya sauka a Najeriya

Ya amince cewa kashi 20.12 har yanzu babban adadi ne, amma ya jaddada cewa alkaluman sun nuna sabuwar kididdiga ta dogon lokaci.

Ya bayyana cewa sake daidaita alkaluman ya kawo sahihin bayanai, kuma raguwar hauhawar farashi yanzu na fitowa a hankali cikin kowane wata.

Fasua ya ke cewa hauhawar farashin kaya ba ya tashi har abada, inda ya yi misali da Ghana da Pakistan da suka fuskanci matsalolin tattalin arziki.

Ya kara da cewa farashin kayan abinci ya fi daidaituwa a bana, inda ya ambaci rahoton wani masani a fannin noma da ya tabbatar da haka.

Gwamnati ta dakatar da harajin shigo da kaya

Kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta saurari korafe-korafen 'yan kasuwa a kan tsarin harajin 4% a kan kayan da ke shigo wa da su.

Ministan Kudi kuma Ministan Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Mista Wale Edun ya ce bayan dogon nazari da tattauna wa, an dakatar da shi.

Sai dai ya ce wannan ba ya nufin an cire harajin gaba daya, sai dai wani tsari na bayar da damar sake duba al'amarin kafin daukar mataki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.