An Yi Rashi a Kano: Abba Kabir Ya Kadu bayan Rasuwar Tsohon Sakataren Gwamnati

An Yi Rashi a Kano: Abba Kabir Ya Kadu bayan Rasuwar Tsohon Sakataren Gwamnati

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi juyayin rasuwar tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar da ya rasu a karshen makon jiya
  • An tabbatar da rasuwar Alhaji Sadauki Kura, wanda ya rasu yana da shekara 88 bayan fama da doguwar jinya a Kano
  • Abba ya ce marigayin ya yi hidima da gaskiya da rikon amana, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen gina tsarin gudanarwar jihar Kano

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Jihar Kano ta yi babban rashin na jajirtacce wanda ya taba rike mukamin sakataren gwamnatin jihar da sauran mukamai.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhininsa kan rasuwar tsohon Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Sadauki Kura.

Gwamna Abba Kabir ya yi ta'aziyyar babban rashi a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano da kuma Alhaji Sadauki Kura. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Abdul Umar.
Source: Facebook

Gwamna ya yi jimamin babban rashi a Kano

Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan Kano, Sanusi Bature D/Tofa ya tabbatar a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Sulhu ya kankama, gwamna ya kawo shirin da za a tallafawa tubabbun 'yan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce gwamnan ya kadu da rasuwar marigayin wanda ya rasu a ranar Asabar da ta gabata 13 ga watan Satumbar 2025.

Hadimin gwamnan, Dawakin Tofa, ya tabbatar da cewa an yi rashin Kura a Kano, bayan jinya, yana da shekara 88 a duniya.

Gwamna Abba ya yi addu'o;i ga marigayi Sadauki Kura a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano yayin wani taro. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Twitter

Yabon da marigayin ya samu daga Abba Kabir

Gwamna Abba Kabir ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen mai hidimar jama’a, wanda ya yi aiki da gaskiya da rikon amana a jihar Kano.

Ya kara da cewa marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen gina tsarin gudanarwa da kyakkyawan shugabanci, yana mai yabawa da hangen nesansa kan sha’anin gwamnati.

Gwamnan daga bisani, ya yi ta’aziyya ga iyalai, abokai da abokan aiki na marigayin, tare da yin addu’a Allah ya saka mi shi Aljanna Firdausi.

Mukaman da marigayi Sadauki ya rike a baya

Alhaji Sadauki Kura ya fara aiki da bankin Union kafin a tura shi ya zama Sakataren Gwamnatin Kano daga shekarar 1983 zuwa shekarar 1985 a jihar da ke Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan ɗan sa kai ya buɗe wuta a masallaci, an samu raunuka

Marigayin ya rike mukamin sakataren gwamnatin Kano ne a wancan lokacin karkashin mulkin gwamna Hamza Abdullahi.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu ya bar matansa biyu da yaya da kuma jikoki da dama.

Tuni aka yi jana’izarsa a gidansa da ke Gandu kusa da Kwalejin Rumfa da misalin karfe 11 na safe a ranar Lahadi 14 ga watan Satumbar 2025.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu inda suka tabbatar da cewa tabbas an yi rashin dattijo da ya ba da gudunmawa a rayuwarsa.

Auren Jinsi: Abba Kabir ya tura kudiri majalisa

Mun ba ku labarin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya amince da tura kudiri zuwa majalisar dokokin jihar wanda yake magana kan auren jinsi.

Gwamna Abba ya ce gwamnatinsa ba za ta yi sassauci ba kan dab'iun da suka sabawa koyarwar al’ada da addinin Musulunci a jihar Kano.

Abba Kabir Yusuf ya ba da tabbacin cewa duk wadanda aka samu da laifi, za su dandani kudarsu yadda ya dace domin tabbatar da bin ka'idar al'adu da Musulunci a Kano.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.