"Yana Gyara Shirmen da Aka Yi": Kusa a APC Ya Yabi Uba Sani, Ya Soki Nasir El Rufai
- Gwamna Uba Sani ya samu yabo a wajen wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC da aka gudanar a Kaduna
- Hamisu Yusuf Mairago wanda yake kusa da gwamna ya bayyana irin jajircewar da gwamnan yake yi wajen kawo ci gaba a jihar
- Alhaji Hamisu Yusuf Mairago ya kuma soki gwamnan da ya gabaci Uba Sani, bisa zargin kokarin kawo katsalandan a Kaduna
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Jam'iyyar APC ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Kaduna ta Kudu ta jihar Kaduna.
A wajen taron, Alhaji Yusuf Hamisu Mairago, ya kwararo yabo ga Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna..

Source: Twitter
Shafin Better Kaduna na manhajar X, ya sanya wani bidiyo da ya kunshi wani bangare na jawabin da Alhaji Hamisu Yusuf Mairago, ya yi a wajen taron.
Gwamna Uba Sani ya samu yabo
Kusan na APC ya bayyana cewa Gwamna Uba Sani yana kokari wajen tafiyar da mulkin jihar Kaduna.
Ya bayyana cewa gwamnan yana kokarin gyara shirmen da aka yi a jihar, shekara takwas da su ka gabata.
"Mu mun san abin da muke da shi. Ya kamata mu daina jin kunya. Gwamna Uba Sani abin alfahari ne. Duk inda ya je a Najeriya da duniya, na je da shi na gani, na ga yadda ake girmama shi."
"Mataimakin shugaban ya ce ko da kawai wannan aikin da Uba Sani ya yi a cikin shekara biyu, ko da shi kadai ya yi, ya isa ya kafa tarihi a Najeriya."
- Alhaji Hamisu Yusuf Mairago
Uba Sani ya damu da jihar Kaduna
Hakazalika ya bayyana cewa Gwamna Uba Sani ba ya barci don ganin ya sauke nauyin da ke kansa na al'ummar jihar Kaduna.
"Gwamna Uba Sani baya barci. Barcin da kawai yake yi shi ne yana cikin mota tsakanin inda za a tafi daga nan ya dan gyangyada. Ko kuma ana kan tebur wajen cin abinci ya dan gyangyada. Kullum karfe 6:00 na safe ake barin gidansa."
"Mutum ne wanda a kullum yake tunanin al'umma kuma yake tuna rantsuwar da ya yi. Tunaninsa ya za a zauna lafiya. Ya za a yi jihar Kaduna ta samu ci gaba. Ya za a yi al'umma su samu sauki."
- Alhaji Hamisu Yusuf Mairago

Source: Facebook
Kusa a APC ya soki El-Rufai
Alhaji Hamisu Yusuf ya kuma yi wasu kalaman suka da ake ganin ya yi su ne kan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Ya nuna cewa tsohon gwamnan yana kokarin kawo katsalandan ga Gwamna Uba Sani, duk da kammala shekara takwas a kan mulki.
"Akwai wani ne da aka ce shi ne mai kula da Kaduna,. Ka yi zamaninka ka dawo ka ce za ka yi zamanin kowa. Ba ka isa ka yi ba. "
"Ramalan Yaro ba shi ba jini ba ne a jikinsa, yana gwamna yana yaronsa shekara hudu ka zo ka karbi mulkin nan, ba irin zagi da cin mutuncin da ba ka yi masa ba."

Kara karanta wannan
Ganduje ya kafa kwamiti, zai binciki gwamnatin Kano kan korar kwamandojin Hisbah 44
"Kai ka yi na ka shekara takwas ka yi abin da ka ga dama ka tafi. Sannan an zo ana gyara shirmen da ka yi, ka zo ka ce za ka yi wa mutane shirmen banza da wofi."
- Alhaji Hamisu Yusuf Mairago
Uba Sani ya yi martani kan biyan 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi raddi kan zargin cewa gwamnatinsa na ba 'yan bindiga kudi don sulhu.
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa ko kadan babu kamshin gaskiya a cikin irin wadannan zarge-zargen.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ba ta taba biyan ko sisin kwabo ba ga 'yan bindiga tun da ya hau kan mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

