Sulhu: 'Dan Bindiga, Ado Aliero Ya Nemi Afuwar Mutanen da aka Kashe wa 'Yan Uwa
- Kasurgumin ɗan ta’addan Najeriya, Ado Aliero, ya nemi gafara daga jama’a bisa kashe-kashen da ya aikata a baya
- Ya yi wannan roƙo ne a wajen zaman sulhu da aka gudanar a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina
- Aliero ya bukaci a ajiye makamai domin a fara sabon gini na zaman lafiya a tsakanin al’umma a Katsina da kewaye
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina – Kasurgumin ɗan ta’adda da ake nema ido rufe, Ado Aliero, ya roki jama’a da su yafe masa bisa laifuffukan da suka shafi kisa da kwace dukiyoyi da ya aikata a baya.
Ya bayyana hakan ne a wajen zaman sulhu da aka gudanar da wasu gungun ‘yan ta’adda a karamar hukumar Faskari, jihar Katsina.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da Ado Aliero ya yi ne a cikin wani bidiyo da shafin Safana News ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aliero ya fara jawabin nasa da harshen Fulatanci, kafin daga bisani ya fassara da Hausa domin kowa ya fahimta.
Ya ce an yi kuskure a baya, amma lokaci ya yi da kowa zai rungumi juna domin gina sabon tsarin zaman lafiya.
Ado Aliero ya roki a yafewa juna
A zaman sulhun, Ado Aliero ya ce yana yi wa kowa fatan alheri tare da kira da a manta da abubuwan da suka faru a baya.
Ya yi kira da a rungumi juna, a yafewa juna, inda ya ce duk wadanda aka yi wa wani abu da suke ganin an munana musu, su yi hakuri a sake gini na zaman lafiya.
Ya ƙara da cewa kowa na iya ba da gudummawa wajen samar da tsaro, matuƙar aka ajiye makamai da komawa yin mu’amala cikin lumana.
Aliero ya yi kira ga zaman lafiya
A cikin jawabin nasa, Aliero ya bukaci al’umma da su daina tozarta juna saboda bambancin harshe ko kabila.
Haka kuma, ya shawarci iyaye da gwamnati da su gina makarantu domin yara su yi karatu domin samun cigaba.
Ya kuma bukaci waɗanda ba su da katin zama ɗan kasa su je su yi, domin su amfana da zama cikakkun 'yan Najeriya.

Source: Facebook
Maganar Aliero kan noma a Katsina
Aliero ya yi kira da cewa kofar komawa gona a buɗe take ga duk wanda yake son komawa noma a yankin.
Ya ce idan aka zauna lafiya, kowa zai cigaba da rayuwa a ko ina ba tare da tsoro ko barazana ga rayuwarsa ba.
A ƙarshe, Aliero ya yi roƙo mai taushi ga jama’a, inda ya ce:
“Duk wata bindiga da ake ba daidai ba da ita, a ajiye ta. Mu rungumi zaman lafiya,'
'Yan bindiga sun kashe jami'in NSCDC
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun yi kwanton bauna sun farmaki wasu jami'an tsaron NSCDC.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun yi nasarar kashe daya daga cikin jami'an da suka harba nan take.
A sanadiyyar farmakin, wasu jami'ai hudu da ke cikin motar NSCDC sun samu munanan raunuka kuma an kwantar da su a asibiti.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


