Bukatar Godwin Emefiele Ta Samu Karbuwa gaban Kotu a Shari'arsa da EFCC

Bukatar Godwin Emefiele Ta Samu Karbuwa gaban Kotu a Shari'arsa da EFCC

  • Kotu ta amince da bukatar da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya gabatar a shari'ar da yake yi da hukumar EFCC
  • Godwin Emefiele ya samu amincewar kotu don ya dauki kwararru su bincike don binciken wasu hujjojin da aka gabatar a kansa
  • Hukumar EFCC ta yi adawa da bukatar Emefiele, tana cewa dole ne a kiyaye amincin hujjojin a hannun kotu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Babbar kotun laifuffuka ta musamman da ke Ikeja, Legas, ta amince da bukatar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Kotun ta ba Emefiele izini ya dauki kwararrun masu bincike domin duba sakonnin WhatsApp da kuma waya mai suna iPhone 2 da aka gabatar a matsayin hujja a shari’arsa da hukumar EFCC.

Kotun ta amince da bukatar Godwin Emefiele
Hoton tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele da tambarin hukumar EFCC Hoto: @cenbank, @OfficialEFCC
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa alkalin kotun, Mai shari'a Rahman Oshodi, ne ya bada iznin a ranar Litinin, 15 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan

Sheikh Isa Pantami ya gana da Peter Obi, ya jero abubuwan da suka tattauna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bukatar Emefiele ta samu shiga a kotu

Mai shari'a Rahman Oshodi, ya bayar da umarnin ne bayan babban lauyan Emefiele, Olalekan Ojo (SAN), ya nemi izinin kiran kwararrun masu binciken kwamfuta domin tabbatar da sahihancin sakonnin da aka ce na Emefiele ne.

Rahoton jaridar The Guardian ya nuna cewa an gabatar da hujjojin ne a shari'ar da ake yi masa kan zargin rashawa da almundahanar kudi har Dala biliyan 4.5 da Naira biliyan 2.8.

Hukumar EFCC ce dai ta shigar da karar a kansa tare da wani Henry Omoile.

EFCC ta ki amincewa da bukatar Emefiele

Lauyar hukumar EFCC, Chineye Okezie, ta yi adawa da bukatar, tana mai cewa hujjojin da aka gabatar dole su zauna a hannun kotu har sai an kammala shari’ar.

Ta kuma ce lauyoyin Emefiele ba su bayyana sunan dakin bincike ko kwararrun da za su yi aikin ba.

Chinenye Okezie ta bukaci kotu ta umarci sashen kwararrun masu bincike na EFCC ya zabi dakin da za a yi bincike, sannan a tabbatar da cewa mai gabatar da kara ya halarci binciken don kiyaye amincin hujjojin.

Kara karanta wannan

Watanni bayan ya rasu, an gano gidan da tsohon gwamna a Najeriya ya mallaka a Landan

Hukuncin da alkali ya yanke

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun ya ce bangaren wadanda ake kara, na da damar gudanar da bincike na kansu, amma sai dai a sanya matakan kariya domin tabbatar da amincin hujjojin.

Ya umurci a gudanar da binciken ne a gaban wakilan bangarorin duka, tare da izinin kowanne bangare ya kawo lauya daya da kwararren mai bincike daya.

Kotun ta amince da bukatar Godwin Emefiele
Hoton tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, tare da jami'an EFCC a kotu Hoto: @OfficialEFCC
Source: Twitter

Hakazalika, wakilin kotu zai sa ido a kan aikin. Sannan binciken zai gudana daga 10:00 na safe zuwa 2:00 na rana a ranakun 24 da 26 ga watan Satumba, 2025.

An dage ci gaba da sauraron shari'ar zuwa ranakun 7 da 8 ga watan Oktoba, 2025, yayin da aka sa ranar 9 ga watan Oktoba, 2025 don ci gaba da karar.

Kotu ta yi watsi da bukatar Emefiele

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da bukatar da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya gabatar mata.

Kara karanta wannan

Da yiwuwar a tsige Sarki, gwamna ya dauki mataki kan abin kunyar da mai martaba ya yi

Godwin Emefiele dai ya bukaci kotun da ta kwato rukunin gidaje 753 da shagunan haya daga hannun hukumar EFCC, don a mallaka masa su.

Alkalin kotun, Mai shari’a Jude Onwuegbuzie ya yi fatali da wannan bukatar da tsohon gwamnan na bankin CBN ya gabatar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng