Ana Barazanar Daina Noma a Najeriya kan Karya Farashi da Tinubu Ya Yi
- Ƙididdiga ta nuna an shigo da kayan noma da ya kai N2.2tn a 2025, abin da ya jawo suka daga manoma da masu casar shinkafa
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni ga kwamitin majalisar zartarwa domin tabbatar da saukar farashin abinci a ƙasar
- Manoma da masana sun ce shigo da kayayyaki da rashin tallafi yana durƙusar da noman cikin gida tare da ƙara barazana ga tsaron abinci
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Rahoto daga hukumar ƙididdiga ta ƙasa ya nuna cewa an shigo da kayan abinci da ya haura Naira tiriliyan 2.22 a 2025.
Rahotanni sun yi hasashen cewa hakan ya haifar da ce-ce-ku-ce daga ƙungiyoyin manoma da masu sarrafa shinkafa a Najeriya.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa manoman sun yi suka ga umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na karya farashin abinci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun yi korafi suna masu cewa hakan bai dace ba matuƙar gwamnati ba ta magance ƙalubalen asali da ke hana noma bunƙasa ba.
Masu ruwa da tsaki sun ce tsarin karya farashin barazana ne ga samar da abinci a ƙasar, tare da nuna cewa gwamnati na ɗaukar matakan da ba su dace ba.
Manoma sun soki shugaba Tinubu
Shugaban ƙungiyar manoman Najeriya (AFAN), Kabir Ibrahim, ya bayyana cewa manoma na cikin halin kunci saboda tsadar taki da rashin tallafi.
Kabir Ibrahim ya kara da cewa shigo da kayan abinci daga waje ya jefa noman cikin gida cikin barazana.
Shugaban ya nuna cewa saukar farashin kaya ba zai yi tasiri ba idan ba a rage kuɗin sufuri ba tare da inganta kayan aikin noma ba.
“Manoma suna kuka kan rashin iya sayen taki saboda farashin kayan abinci ya faɗi ƙasa,”
- In ji shi.
Barazanar daina noma a Najeriya
Shugaban masu casar shinkafa, Peter Dama, ya kalubalanci tsarin gwamnati, yana cewa umarnin saukar da farashin kaya ba zai yi aiki ba idan ba a tattauna da masu ruwa da tsaki ba.
Ya ce kamata ya yi gwamnati ta kira masu ruwa da tsaki a harkar sufuri da noma, ta ba da tallafi ko rangwamen haraji, maimakon fitar da sanarwa kawai.
Dama ya ce:
“Idan aka ci gaba da shigo da kayan abinci ba tare da tallafi ba, manoma za su daina noma,”
Batun raba motocin noma a Najeriya
Baya ga shigo da kayayyaki, Daily Trust ta wallafa cewa akwai motocin noma 2,000 da aka ƙaddamar a Yulin 2024 amma har yanzu ba a raba su ba.
Ibrahim ya ce manoma sun gaji da jira, domin motocin za su taimaka wajen rage wahalar aiki da suke fama da ita.
Wani jami’in ma’aikatar noma ya tabbatar da cewa har yanzu ana jiran amincewar fadar shugaban ƙasa kan tsarin rabon motocin.

Source: Twitter
Legit ta tattauna da manomi
Legit Hausa ta tattauna da wani manomi a jihar Gombe, Muhammad Abubakar, inda ya ce suna fuskantar kalubale babba.
Muhammad ya ce:
"Yanzu haka akwai wajen da muka yi noma ba mu samu riba ba, saboda kudin da muka kashe ba zai dawo ba. Mun samu matsala ga farashin kayan ya yi kasa sosai.
Za a ba manoma lamunin N250bn
A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa ya yi zama na musamman da masu ruwa da tsaki kan noma.
A yayin zaman da suka yi, Sanata Kashim Shettima ya yi umarni da a gaggauta raba wa manoma rancen Naira biliyan 250.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a raba kudin ne domin karfafa manoman a fadin Najeriya da samar da abinci yadda ya kamata.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


