Atiku Ya Sake Yi Wa Gwamnatin Tinubu Saukale, Ya Fadi Abin da Ta Gaza Magancewa

Atiku Ya Sake Yi Wa Gwamnatin Tinubu Saukale, Ya Fadi Abin da Ta Gaza Magancewa

  • Tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi kalamai masu kaushi kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
  • Atiku Abubakar ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta gaza wajen magance yunwa da talauci
  • Hakazalika ya nuna cewa manufofin da Tinubu ya bullo da su, sun jefa 'yan Najeriya cikin halin kunci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya sake taso gwamnatin Mai girma Bola Tinubu a gaba.

Atiku ya bayyana cewa sama da shekaru biyu da Shugaba Tinubu ya karɓi ragamar mulki, babu wata alamar cewa zai iya magance yunwa da talaucin da su ka addabi kasar nan.

Atiku ya soki gwamnatin Tinubu
Hoton Atiku Abubakar da Shugaba Bola Tinubu Hoto: @atiku, @DOlusegun
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakinsa, Paul Ibe, ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku Abubakar ya koka da yunwa a Najeriya

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yanke hutunsa, ya sanya lokacin dawowa Najeriya

Jagoran 'yan adawan ya bayyana yunwar da ake fama da ita a kasar nan a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, musamman ma ga matalauta da marasa galihu.

"Duk mafi munin tarzoma da juyin juya halin siyasa da zamantakewa a duniya an fi hura wutarsu ne saboda mummunar yunwa da rashin kayan more rayuwa."

- Atiku Abubakar

Atiku ya ce babban aikin kowace gwamnati shi ne kare rayuka da samar da walwala ga jama’a, amma talakawan Najeriya na ci gaba da nutsewa cikin bakin talauci a karkashin mulkin Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC.

Atiku ya yi gargadin cewa halin da ake ciki yanzu ba abin murna ba ne, domin yana kara haifar da matsaloli na aikata laifuffuka kamar zamba, ta’addanci, garkuwa da mutane, shiga kungiyoyin asiri, shaye-shaye.

“A nan gida Najeriya, ba zai zama abin mamaki ba idan aka ce ma har zanga-zangar EndSARS ta samo asali ne daga takaicin yunwa da rashin kulawar gwamnati ga jama’a.”

- Atiku Abubakar

Atiku ya ce manufofin Tinubu ba su aiki

Atiku ya kara da cewa duk da ikirarin sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke cewa tana yi, hakikanin magana ita ce rashin tabbas kan abinci ya zama ruwan dare a fadin kasar nan, rahoton TheCable ya tabbatar da labarin.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Omoyele Sowore ya bankado game da gwamnonin Arewa

"Babu wata gwamnati mai daraja da ba ta sanya walwala da tsaron jama’a a matsayin babban ginshikin ta ba.”

- Atiku Abubakar

Atiku ya ragargaji gwamnatin Tinubu
Hoton tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar Hoto: @atiku
Source: Facebook

Ya jaddada cewa tunda ana yin sauye-sauye ne don al’umma, ba don gwamnati ba, to dole a yi irin waɗannan sauye-sauyen tare da yin la’akari da halin da mutane za su shiga.

"Ko da kuwa waɗanda ke kan mulki a yanzu sun amince ko ba su amince ba, gaskiyar rayuwarmu ita ce matalauta na kara mutuwa saboda yunwa, yayin da mafi yawan waɗanda ke raye su ke fama da manufofin wannan gwamnati marasa inganci."

- Atiku Abubakar

Shugaba Tinubu zai dawo gida Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kammala hutun da ya tafi yi a kasar Faransa.

Shugaba Bola Tinubu ya yanke hutunsa na aiki wanda ya tsara gudanarwa a kasashen Faransa da Birtaniya.

A cikin wata sanarwa, an bayyana cewa Shugaba Tinubu zai dawo ne don ci gaba da gudanar da harkokin mulki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng