Manyan Jagororin 'Yan Ta'adda da Aka Gani wajen Zaman Sulhu a Katsina
Jihar Katsina - An gudanar da wani taron zaman sulhu da 'yan ta'adda a jihar Katsina don samun zaman lafiya.
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Taron zaman sulhun dai ya gudana ne a kauyen Hayin Gada da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Source: Twitter
An yi zaman sulhu da 'yan ta'adda a Katsina
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya kawo rahoto kan zaman sulhun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron zaman sulhun ya samu halartar shugabannin al’umma, wakilan jami'an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
A wajen taron, an jaddada bukatar nuna gaskiya da jajircewa don kawo karshen ta’addanci a yankin.
Taron wanda aka bayyana a matsayin irinsa mafi girma, ya haɗa gungun kungiyoyin 'yan bindiga da dama da su ka sha alwashin rungumar zaman lafiya da zama tare da al’umma.
Ra’ayoyi sun bambanta kan sulhu
Wasu mutane dai na kallon batun sulhun a matsayin wata dama ta dawo da zaman lafiya.
Yayin da wasu kuma ke shakku kan gaskiyar 'yan ta'addan duba da irin muggan ayyukan da su ka aikata a baya.
Jagororin 'yan ta'adda da su ka halarci zaman sulhu
Taron zaman sulhun ya samu halartar manyan jagororin 'yan ta'adda daga ciki da wajen jihar Katsina.
Ga jerinsu a nan kasa:
1. Ado Aleiro
Hatsabibin jagoran 'yan ta'adda, Ado Aleiro, na daga cikin mutanen da aka gani a wajen zaman sulhu.
Ado Aleiro na daga cikin mutanen da su ka gabatar da jawabi a wajen taron wanda aka gudanar a karamar hukumar Faskari.
Jagoran 'yan ta'addan ya nuna fatan cewa za a samu zaman lafiya a Katsina da ma sauran wurare bayan zaman tattaunawar.
A cikin jawabinsa, Ado Aleiro ya tuna irin gudummawar da ya bayar a baya a shirin zaman lafiya, inda ya bayyana cewa an rushe tsarin ne bayan cafke ɗansa.
Jagoran 'yan ta'addan ya ce sabuwar tattaunawar nada matukar muhimmanci domin a karon farko an ga tarin manyan 'yan bindiga sun fito fili.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa sakamakon taron zai tabbatar da zaman lafiya, ba kawai a Faskari ba har ma a kasar baki ɗaya.
2. Isiya Kwashen Garwa
Jagoran 'yan ta'adda, Isiya Kwashen Garwa, na daga cikin mutanen da suka halarci zaman sulhun.
A baya Hedikwatar Tsaro ta kasa ta ayyana shi a cikin jerin 'yan ta'addan da ake nema ruwa a jallo.
Akwai sunan Isiya Kwashen Garwa, a cikin jerin manyan ƴan ta’adda da ƴan bindiga 19 da ake nema a Najeriya.
Isiya Kwashen Garwa, dan aalin kauyen Kamfanin Daudawa ne na karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.
An daɗe ana danganta shi da kashe-kashe, sace-sace da kai hare-hare a dazukan jihar Katsina da sauran jihohi makwabta.
Shafin Katsina Daily News ya sanya bidiyon jawabin da jagoran 'yan ta'addan ya yi a wajen taron.
A cikin jawabinsa, ya bayyana cewa sun dauki makamai ne don rama muzgunawar da ake yi wa 'yan uwansu Fulani.
Ya rika jawo ayoyin Al-Kur'ani mai girma don karin gaske kan bayanan da ya rika yi a wajen taron.
3. Kachallah Babaro
Jagoran 'yan ta'adda Kachallah Babaro ya bayyana a wajen zaman sulhun da aka yi a jihar Katsina.

Source: Facebook
Hatsabibin dan ta'addan ya daɗe yana addabar yankin kananan hukumomin Kankara da Malumfashi na jihar Katsina.
Rahotanni sun nuna shi ne ya kai mummunan harin da ya hallaka masallata 32 a kauyen Mantau karamar hukumar Malumfashi.
4. Hassan Dan Tawaye
Hatsabibin jagoran 'yan ta'adda, Hassan Dan Tawaye, na daga cikin mutanen da aka gani wajen zaman sulhu a karamar hukumar Faskari.
Jagoran 'yan ta'aadan ga halarci zaman ne don ganin an samu zaman lafiya a yankin tare da daina kai hare-hare.
A jawabin da ya yi, ya nuna muhimmancin zaman lafiya tsakanin al'ummar Hausa-Fulani.
Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar sojojin Najeriya, sun ragargaji 'yan ta'adda a jihar Katsina.
Dakarun sojojin sun yi artabun ne da 'yan ta'adda a karamar hukumar Kankara, inda aka yi nasarar hallaka miyagu guda 23.

Kara karanta wannan
An bankado abubuwa, matar shedanin 'dan bindiga ta shiga hannu a Zamfara, ta tsure
Dakarun sojojin sun kuma samu nasarar ceto mutanen da aka yi garkuwa da su, wadanda suka hada da mata da kananan yara daga hannun tantiran.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


