Kano: Lauyoyi 2 Sun Bayyana Dalilin Janye wa daga Kare Gwamnati a Shari'a da Jafar Jafar
- Lauyoyi biyu sun nesanta kansu daga ƙarar da gwamnatin Kano ta shigar kan Jaafar Jaafar da Umar Audu a gaban wata kotu
- Sun ce sun ba da izinin amfani da sunayensu a takardar ƙara ba kuma ba su da alaƙa da lauyoyin da suka rattaba hannu
- Suna zargin lauyan Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya sanya sunayensu ba tare da yardarsu ba don shari'a da Jaafar Jaafar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wasu lauyoyi guda biyu, Ahmed Musa da Ridwan Yunusa, sun nesanta kansu daga wata takardar korafi da aka ce an shigar a kotu.
Rahotanni sun ce an mika takardar ne domin gurfanar da mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, da abokin aikinsa Umar Audu, a gaban kotu bisa zargin cin mutunci.

Kara karanta wannan
Maganar N Power ta dawo, Abba Hikima, Ɗan Bello za su koma kotu da gwamnatin Tinubu

Source: Facebook
Daily Nigerian ta wallafa cewa ana zarginsu da cin hanci da ake yi wa Daraktan Tsare-tsare na Fadar Gwamnatin Kano, Abdullahi Rogo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kano ta shigar da korafi a gaban kotu
An aika takardar korafin ga Babban Rajistaran Babbar Kotun Kano da ita, ta fito ne daga ofishin lauyan Gwamna Abba Kabir Yusuf, Hamza Dantani.
Dantani ya shigar da karar bisa zargin batanci, domin a cewarsa rahoton jaridar ya bata wa Abdullahi Rogo suna da kuma iya jefa al'umma cikin rudani.
Rahoton da ya jawo rikicin ya ce hukumar ICPC da EFCC sun gano cewa Abdullahi Rogo ya karkatar da Naira biliyan 6.5 zuwa asusu mai zaman kansa.
Lauyoyi sun janye daga karar gwamnatin Kano
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Ridwan Yunusa ya bayyana cewa bai taba ba da izinin amfani da sunansa a cikin takardar ƙara ba, kuma bai taɓa aiki da ofishin Potent Attorneys ba.

Source: Facebook
Ya ce:
“Na fitar da sunana daga wannan kara tun farko. Ina so in bayyana cewa ba ni da wata alaƙa da wannan kara, kuma ban ba da izinin amfani da sunana ba."
Shi ma Ahmed Musa ya tabbatar da cewa Ridwan ne ya sanar da shi da batun takardar, amma sam bai san an yi haka ba.
Ya ce:
“Ya ce zai fitar da bayani, na kuma ce ya turo min takardar domin in gani. Bayan na karanta, sai na ga an saka sunana a cikin masu sa hannu, duk da babu ni a cikin lamarin."
Sun ce wannan mataki na amfani da sunansu ba tare da izini ba yana nuna rashin kwarewa da ladabi a aikin lauya, kuma yana da nufin murkushe 'yancin 'yan jarida fadin gaskiya.
An soki gwamnatin Kano kan hadimin Abba
A baya, mun wallafa cewa Gwamnatin jihar Kano ta fuskanci suka kan yadda ta mayar da martani kan zarge-zargen da ake wa Daraktan Kula da Harkokin Fadar Gwamnati, Abdullahi Rogo.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta dauki harama, nan ba da jimawa ba za a daina dauke wuta a Najeriya
Rahotannin baya-bayan nan sun ce ana tuhumar Rogo da wawure makudan kudi daga asusun gwamnati, inda aka bayyana cewa hukumar EFCC da ICPC ne su ka yi aiki a kan batun.
Sai dai maimakon gwamnati ta bayyana matakin da take dauka don bincike ko hukunta wanda ake zargi, ta fito da sanarwa tana kare hadimin na Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
