'Yan Daba: Masu Shigar Mata Su Yi Kisan Gilla Sun Bulla a Kano, an Kama Wasu
- Rahoto ya nuna cewa an kama wasu da ake zargi da ‘yan daba ne a Kano, bayan sun yi shigar mata domin kai hari a wani yanki
- Rahotanni sun nuna cewa mutanen na cikin wata ƙungiyar masu kisan gilla da ke amfani da dabarar ɓoye fuska
- Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da samun matsalar 'yan daba da masu kwacen waya a Kano duk da kokarin da hukuma ke yi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kano - Rundunar tsaro a yankin Kurna da ke cikin birnin Kano ta yi nasarar cafke wasu mutane da ake zargi ‘yan daba ne da suka yi shigar mata domin kai hari a yankin.
Rahoton ya nuna cewa waɗannan mutane sun kutsa cikin yankin ne da nufin kai farmaki ga wasu mutane kafin jami’an tsaro na sa-kai su mamaye wurin.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An bayyana cewa yanzu haka an miƙa waɗanda aka kama hannun hukumomin tsaro domin gudanar da bincike tare da gurfanar da su a gaban kotu.
'Yan daba sun yi shigar mata a Kano
Bincike ya nuna cewa waɗanda aka kama na daga cikin wata ƙungiya da ke ɗaukar nauyin kai hare-hare a kan mutane musamman domin yin kisan gilla.
Wasu majiyoyi sun ce wannan dabara ta sanya tufafin mata na daga cikin hanyoyin da suke bi don shigar da kansu cikin jama’a ba tare da an gane su ba.
A wannan karon dai, shirin ya ci tura bayan jami’an tsaro na yankin Kurna suka samu bayanai a kansu, suka kuma ɗauki matakin gaggawa da ya kai ga cafke su.
Martanin al’ummar Kano kan lamarin
Mazauna yankin Kurna sun nuna jin daɗinsu kan yadda jami’an tsaro suka yi saurin daukar mataki domin kare rayukan jama’a.

Kara karanta wannan
'Duk da fara shirin sulhu, 'Yan bindiga sun yi kisa, an sace mutane masu yawa a Katsina
Sun yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara tsaurara matakai da saka idanu musamman a manyan hanyoyi da kuma unguwanni da ke fuskantar matsalar ‘yan daba.

Source: Facebook
Matsalar ‘yan daba a jihar Kano
Birnin Kano na fuskantar ƙalubale na ‘yan daba, musamman a wasu yankuna da ake yawan samun tarzoma da hare-hare da dare.
Hukumomin tsaro tare da gwamnatin jihar Kano sun dade suna gudanar da shirye-shirye domin magance wannan matsala, ciki har da ƙara sa ido da yawan sintiri a unguwanni.
Sai dai duk da wannan ƙoƙari, rahotanni suna nuna cewa 'yan daba na ci gaba da ƙirƙiro dabaru don cutar da jama’a.
An kashe Kachalla Babangida a Kogi
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun ragargaji wasu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar Kogi.
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sun yi nasarar kashe mataimakin shugaban 'yan ta'adda na yankin da ake kira Kachalla Babangida.
Sakamakon gumurzun da sojoji suka yi da 'yan ta'addan, da dama daga cikin 'yan bindigan sun samu munanan raunuka da za su iya mutuwa daga baya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
